Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/1 p. 8-p. 9 par. 5
  • Bitrus da Hananiya Sun Yi Ƙarya—Wane Darasi Ne Za Mu Iya Koya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitrus da Hananiya Sun Yi Ƙarya—Wane Darasi Ne Za Mu Iya Koya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Sa Bai Kamata Mu Yi Karya Ba
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Taimako Domin Mu Kawar da Tsoratarmu
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/1 p. 8-p. 9 par. 5

KU KOYAR DA YARANKU

Bitrus da Hananiya Sun Yi Ƙarya—Wane Darasi Ne Za Mu Iya Koya?

Kamar yadda ka sani, ƙarya tana nufin faɗin abin da ba gaskiya ba. Ka taɓa yin ƙarya?—a Manyan mutane da suke ƙaunar Allah ma sun taɓa yin ƙarya. Wataƙila ka san wani a cikin Littafi Mai Tsarki da ya taɓa yin hakan. Sunansa Bitrus ne, kuma yana ɗaya daga cikin almajirai 12 na Yesu. Bari mu ji labarin abin da ya sa ya yi ƙarya.

Bayan da aka kama Yesu, sai aka kai shi gidan babban firist, kuma a lokacin sha biyu na dare ya wuce. Ba wanda ya gane Bitrus sa’ad da ya shiga gidan babban firist ɗin. Sa’ad da Bitrus ya je wurin wuta, sai baiwar babban firist da ta buɗe masa ƙofa ta gane shi. Yarinyar ta ce: “Kai kuma dā kana tare da Yesu.” Bitrus ya ji tsoro kuma ya yi musun hakan.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa bayan hakan “wata kuyanga ta gan shi,” kuma ta ce: “Wannan mutum kuma dā yana tare da Yesu.” Sai Bitrus ya sake yin musu har ila. Da aka jima kaɗan, sai wasu suka je suka same Bitrus suka ce masa: “Hakika kai kuma na cikinsu ne.”

Bitrus ya tsorata ƙwarai. Saboda haka, a wannan karo na uku ya sake yin ƙarya, ya ce: “Ban san mutumin ba” sam! Sai zakara ya yi cara. Da Yesu ya kalli Bitrus, sai Bitrus ya tuna cewa bai daɗe ba da Yesu ya gaya masa cewa: ‘Kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.’ Bitrus ya fashe da kuka. Ya yi nadama sosai!

Shin irin wannan abin zai iya faruwa da kai?— Yana yiwuwa kana makaranta sai ka ji ’yan makarantarku suna magana game da Shaidun Jehobah. Wani ya ce: “Ba sa rera tāken ƙasa.” Wani kuma ya ce: “Shaidun Jehobah ba Kiristoci ba, su ’yan ƙungiyar asiri ne.” Wani kuma ya ƙara da cewa: “Ba sa bikin Kirsimati don ba su gaskata da Yesu ba.” Sai ɗayan su ya juya ya tambaye ka, “Kai ma Mashaidin Jehobah ne, ko ba haka ba?” Mene ne za ka ce?—

Kafin irin wannan abin ya faru, zai dace ka shirya abin da za ka faɗa tun da wuri don ka iya ba da amsa mai kyau. Bitrus bai shirya ba sam. Sa’ad da aka matsa masa, sai ya yi ƙarya! Duk da haka, ya tuba kuma Allah ya gafarce shi.

Hananiya, wani almajirin Yesu a ƙarni na farko ma ya yi ƙarya. Amma Allah bai gafarce shi da matarsa Safiratu ba. Sun haɗa baki don su yi ƙarya. Bari mu ga abin da ya sa Allah bai gafarce Hananiya da Safiratu ba.

Kwanaki goma bayan Yesu ya bar almajiransa kuma ya koma sama, mutane 3000 suka yi baftisma a Urushalima. Mutane da yawa sun zo daga wurare masu nisa don Idin Fentakos, kuma bayan sun zama almajiran Yesu, suka yi shawara cewa za su ɗan zauna a Urushalima don su ƙara fahimtar sabon addininsu. Saboda haka, wasu daga cikin almajiran Yesu sun yi amfani da kuɗaɗensu wajen kula da su.

Hananiya da matarsa suka sayar da filinsu don su sami kuɗin taimaka wa sababbin nan da suka yi baftisma. Sa’ad da Hananiya ya kawo wa manzanni kuɗin, sai ya ce dukan kuɗin filin da suka sayar ke nan. Amma ba gaskiya ba ne! Ya ɓoye sauran kuɗin! Allah ya bayyana wa Bitrus abin da suka yi, kuma saboda haka, Bitrus ya ce wa Hananiya: “Ba ka yi ƙarya ga mutane ba, amma ga Allah.” Sa’ad da Hananiya ya ji haka, sai ya faɗi ya mutu! Bayan awa uku, sai matarsa ta shigo. Ba ta san abin da ya faru da mijinta ba, sai ita ma ta tabka nata ƙaryar kuma ta faɗi ta mutu.

Wani babban darasi da za mu koya daga wurin su shi ne cewa faɗin gaskiya yana da muhimmanci! Hakika, dukanmu muna bukata mu koyi wannan darasi! Duk da haka, dukanmu mukan yi kuskure, musamman ma a lokacin da muke ƙanana. Sanin cewa Jehobah yana ƙaunarka kuma zai gafarce ka kamar yadda ya gafarci Bitrus abin farin ciki ne, ko ba haka ba?— Amma ka tuna cewa muna bukata mu riƙa faɗin gaskiya. A duk lokacin da muka yi ƙarya cikin kuskure, ya kamata mu roƙi Jehobah ya gafarce mu. Abin da Bitrus ya yi ke nan, kuma Allah ya gafarce shi. Idan muka yi ƙoƙari don kada mu ƙara yin ƙarya, mu ma Allah zai gafarce mu!

Ka Karanta A Naka Littafi Mai Tsarki

  • Matta 26:69-75

  • Ayyukan Manzanni 2:38-42; 4:32-37; 5:1-11

a Idan kana karatun da yaro ne, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ba yaron dama ya faɗi ra’ayinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba