Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
“In darajanta sunanka kuma har abada.”—ZAB. 86:12.
1, 2. Yaya Shaidun Jehobah suke ɗaukan sunan Allah?
COCIN Kiristendam ba sa amfani da sunan Allah. Alal misali, fassarar Revised Standard Version ta ce “bai dace ba ko kaɗan” mutane suna kiran sunan Allah.
2 Amma, Shaidun Jehobah suna alfahari a kira su da sunan Allah kuma suna daraja sunan. (Karanta Zab. 86:12; Ish. 43:10.) Ƙari ga haka, muna ɗaukan cewa gata ne mu fahimci ma’anar sunan Allah kuma mun san cewa yana da muhimmanci a tsarkake sunansa. (Mat. 6:9) Don kada mu manta cewa daraja ce a gare mu mu san sunan nan Jehobah, za mu tattauna tambayoyi uku masu muhimmanci: Mene ne yake nufi a san sunan Allah? Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya cancanci samun sunan nan mai girma. Kuma ta yaya za mu yi biyayya da sunan nan Jehobah?
MA’ANAR SANIN SUNAN ALLAH
3. Mene ne sanin sunan Allah yake nufi?
3 Sanin sunan Allah ba ya nufin sanin kalmar nan “Jehobah” kawai ba. Yana nufin sanin wane irin Allah ne shi. Hakan ya ƙunshi sanin ra’ayinsa da halinsa da nufinsa da yadda yake ayyuka, musamman yadda yake bi da mutanensa. Hakika, Jehobah yana bayyana mana waɗannan abubuwan da sannu-sannu, cikin jituwa da nufinsa. Jehobah yake cika nufinsa, a hankali ya bayyana ko shi wane irin Allah ne. (Mis. 4:18) Mun san cewa Allah ya gaya wa Adamu da Hawwa’u sunansa, domin Hawwa’u ta yi amfani da sunan bayan ta haifi Kayinu. (Far. 4:1) Bayin Jehobah masu aminci kamar su Nuhu da Ibrahim da Ishaƙu da Yaƙubu sun san sunan Allah. Sun ƙara sanin ko shi wane irin Allah ne sa’ad da ya albarkace su da kula da su da kuma bayyana musu nufinsa. Daga baya, Allah ya bayyana wa Musa wani abu mai muhimmanci game da ma’anar sunansa.
4. Me ya sa Musa ya tambayi Allah sunansa, kuma me ya sa yake son ya tabbatar wa Isra’ilawa cewa Allah zai cece su?
4 Karanta Fitowa 3:10-15. Allah ya ba Musa umurni sa’ad da yake ɗan shekara 80, cewa: “Ka fito da mutanena ’ya’yan Isra’ila daga cikin Masar.” Sai Musa ya yi wa Jehobah tambaya mai muhimmanci cewa: ‘Idan Isra’ilawa suka tambaye ni mene ne sunanka, me zan ce musu?’ Me ya sa Musa ya yi wannan tambayar, da yake mutanen Allah sun san sunansa da daɗewa? Yana son ya san ko wane irin Allah ne Jehobah don ya tabbatar wa Isra’ilawa cewa Allah zai cece su da gaske. Tambayar da ya yi ta dace, domin Isra’ilawa bayi ne da daɗewa, kuma wataƙila sun yi shakka cewa Jehobah zai iya ceton su. Wasu Isra’ilawa ma sun soma bauta wa allolin ƙasar Masar!—Ezek. 20:7, 8.
5. Mene ne Jehobah ya bayyana wa Musa game da sunansa?
5 Wace amsa ce Jehobah ya ba Musa? Ya ce: “Haka za ka ce wa ’ya’yan Isra’ila, NI NE ya aike ni a gare ku.”a Sai ya daɗa cewa: “Yahweh, Allah na ubanninku . . . ya aike ni gare ku.” Ta wajen faɗan hakan, Allah ya bayyana cewa zai zama duk abin da yake bukata ya zama ko kuma zai yi kome da yake bukata ya yi don ya cika alkawuransa. Shi Allah ne da ke cika alkawuransa a koyaushe. Shi ya sa Jehobah ya daɗa a aya ta 15 cewa: “Wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.” Babu shakka, wannan kalamin ya burge Musa kuma ya ƙarfafa bangaskiyarsa.
JEHOBAH YA CIKA MA’ANAR SUNANSA
6, 7. Ta yaya Jehobah ya cika alkawarinsa?
6 Ba da daɗewa ba da ya gama magana da Musa, Jehobah ya cika alkawarinsa kuma ya ’yantar da Isra’ilawa. Ya bugi Masarawa da annoba goma kuma ya nuna cewa Fir’auna da allolin ƙasar ba su da ƙarfi. (Fit. 12:12) Sai Jehobah ya buɗe wa Isra’ilawa hanya a cikin Jar Teku suka wuce, kuma ya sa ruwa ya ci Fir’auna da rundunarsa. (Zab. 136:13-15) A cikin “babban jeji mai-ban tsoro,” Jehobah ya ceci miliyoyin Isra’ilawa ta wajen ba su abinci da ruwa. Ya sa tufafinsu da takalmansu ba su lalace ba. (K. Sha 1:19; 29:5) Dukan waɗannan sun nuna cewa ba abin da zai iya hana Jehobah cika alkawuransa ba. Daga baya ya ce: “Ni dai, ni ne [Jehobah] banda ni kuma babu wani mai-ceto.”—Isha. 43:11.
7 Joshua wanda ya ɗauki matsayin Musa, ya ga ayyuka masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi a ƙasar Masar da kuma cikin jeji. Saboda haka, sa’ad da Joshua ya kusan mutuwa, ya gaya wa Isra’ilawa: “Kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” (Josh. 23:14) Jehobah ya cika alkawarin da ya yi.
8. Ta yaya Jehobah yake cika alkawarinsa a yau?
8 Jehobah yana cika alkawarinsa a yau. Ta hanyar Ɗansa, ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, za a yi wa’azin Mulkin “cikin iyakar duniya.” (Mat. 24:14) Jehobah ne kaɗai zai iya annabta cewa za a yi wannan aikin kuma shi ne yake da ikon ya tabbata an yi shi. Kuma yana amfani da mutane da yawa ‘marasa-karatu da talakawa’ don ya yi aikin nan. (A. M. 4:13) Saboda haka, muna cika annabcin Littafi Mai Tsarki sa’ad da muka yi wa’azin bishara. Muna daraja Ubanmu kuma muna nuna cewa mun amince da abin da muka faɗa sa’ad da muke addu’a: “A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Mat. 6:9, 10.
SUNANSA MAI GIRMA NE
9, 10. Mene ne muka ƙara koya game da Jehobah daga yadda ya yi sha’ani da Isra’ilawa?
9 Ba da daɗewa ba, Jehobah ya ƙara bayyana wa Isra’ilawa wasu abubuwa game da sunansa bayan da suka bar ƙasar Masar. Ta hanyar Dokar alkawari, Jehobah ya ce zai kula da su yadda miji yake kula da matarsa. (Irm. 3:14) Isra’ilawa kuma suka zama kamar mata ga Jehobah, don su mutane ne masu ɗauke da sunansa. (Isha. 54:5, 6) Idan sun yi biyayya ga dokokinsa, zai albarkace su, ya kāre su kuma ya sa su kasance da salama. (Lit. Lis. 6:22-27) Dukan al’ummai za su sani cewa babu wani Allah kamar Jehobah. (Karanta Kubawar Shari’a 4:5-8; Zabura 86:7-10.) Yayin da Isra’ilawa suke bauta wa Allah, baƙi da yawa daga wasu al’ummai sun soma bauta ta gaskiya. Sun faɗi abin da Ruth ’yar ƙasar Mowab ta gaya wa Naomi: “Danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.”—Ruth 1:16.
10 A cikin shekaru 1,500 da Jehobah ya yi sha’ani da Isra’ilawa, ya bayyana abubuwa da yawa game da halinsa. Ko da yake sun sha yi masa rashin biyayya, Jehobah ya ci gaba da nuna musu cewa shi “Allah ne cike da juyayi” da kuma “mai-jinkirin fushi.” Shi Allah ne mai yawan haƙuri da kuma tsawon jimrewa. (Fit. 34:5-7) Amma, haƙurin Jehobah yana da iyaka, domin al’ummar Isra’ila ba ta ƙara zama mutane masu ɗauke da sunansa ba, sa’ad da ta ƙi ta gaskata da Yesu kuma ta kashe shi. (Mat. 23:37, 38) Sun zama kamar busashen itace a gaban Jehobah. (Luk 23:31) Ta yaya hakan ya shafi halinsu game da sunan Allah?
11. Me ya sa Isra’ilawa suka daina amfani da sunan Allah?
11 Da shigewar lokaci, Isra’ilawa suka soma kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da sunan Allah. Suna ganin bai kamata kowa ya kira sunan Allah ba, da yake sunan yana da tsarki sosai. (Fit. 20:7) Saboda haka, a hankali aka daina amfani da sunan nan Jehobah. Babu shakka, Jehobah ya yi fushi sosai game da yadda suka ƙi daraja sunansa. (Zab. 78:40, 41) Sunansa yana da muhimmanci a gare shi, domin Littafi Mai Tsarki ya ce yana kishi don sunansa. Isra’ilawa ba su cancanci zama masu ɗauke da sunan Allah ba da yake sun ƙi daraja sunansa. (Fit. 34:14) Wannan ya koya mana cewa yana da muhimmanci sosai mu daraja sunan Mahaliccinmu.
WASU MUTANE MASU ƊAUKE DA SUNAN ALLAH
12. Su waye ne suka zama mutane da aka kira sunan Allah a bisansu?
12 Ta bakin Irmiya, Jehobah ya ce zai yi “sabon alkawari” da sabuwar al’umma. Dukan waɗanda suke cikin wannan sabuwar al’umma daga “ƙaraminsu har zuwa babba,” za su “san Ubangiji.” (Irm. 31:31, 33, 34) Wannan annabcin ya cika a Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu, a lokacin da Allah ya kafa wannan sabon alkawarin. Sabuwar al’umma, wato, “Isra’ila na Allah” wadda ta ƙunshi Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, sun zama mutane “domin sunansa [Allah],” ko kuma mutane da aka “kira sunana a bisansu” in ji Jehobah.—Gal. 6:16; karanta Ayyukan Manzanni 15:14-17; Matt. 21:43.
13. (a) Shin Kiristoci na farko sun yi amfani da sunan Allah? Ka bayyana. (b) Yaya kake ɗaukan gatar yin amfani da sunan Allah a hidimarka?
13 A matsayin mutane da aka “kira sunan [Allah] a bisansu,” waɗanda suke cikin sabuwar al’umma sun yi amfani da sunan Allah. Alal misali sun yi amfani da sunansa sa’ad da suke ƙaulin Nassosin Ibrananci.b Sa’ad da manzo Bitrus yake magana da Isra’ilawa da waɗanda suka zama Kiristoci a ranar Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu, ya yi amfani da sunan Allah sau da yawa. (A. M. 2:14, 20, 21, 25, 34, NW) Domin Kiristoci na farko sun daraja sunan Allah, ya albarkaci aikinsu na wa’azi. A yau ma, Jehobah zai albarkaci hidimarmu sa’ad da muka gaya wa mutane sunansa, kuma muka nuna musu a nasu Littafi Mai Tsarki idan akwai sunan a ciki. Gata ne a gare mu mu gaya wa mutane game da Jehobah a wannan hanyar. Ga waɗanda suka san Allah, hakan yana iya zama somawar dangantaka na kud da kud da Jehobah har abada.
14, 15. Ta yaya muka san cewa Jehobah ya kāre sunansa?
14 Bayan mutuwar manzanni, wasu suka soma gurɓata ikilisiyar Kirista da koyarwar ƙarya. (2 Tas. 2:3-7) Waɗannan malaman ƙarya sun bi al’adar Yahudawa na ƙin yin amfani da sunan Allah. Shin Jehobah ya ƙyale a kawar da sunansa ne? A’a. Ta yaya muka sani? Ba mu san yadda ake furta sunan Allah a dā ba, amma har ila sunansa bai bi iska ba. Shekaru da dama, sunan Allah yana cikin fassarorin Littafi Mai Tsarki masu yawa, da kuma cikin rubuce-rubucen masanan Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a shekara ta 1757, wani mai suna Charles Peters ya rubuta cewa, ma’anar sunan Allah ta nuna ko wane irin Allah ne Jehobah fiye da kowane irin laƙabi. A wani littafi da aka rubuta a shekara ta 1797 game da bautar Allah, Hopton Haynes ya ce, Jehobah ne sunan da Yahudawa suke kiran Allah, “wanda shi kaɗai ne suka bauta wa, kamar yadda Kristi da manzanni suka yi.” Henry Grew (1781-1862) ya yi amfani da sunan Allah kuma ya fahimci cewa mutane sun kawar da wannan sunan kuma wajibi ne a tsarkake shi. George Storrs (1796-1879) da Charles T. Russell, waɗanda suka yi aiki tare, sun yi amfani da sunan Allah.
15 Shekara ta 1931 tana da muhimmanci ga mutanen Allah. Kafin wannan shekarar, ana kiran su ɗaliban Littafi Mai Tsarki, amma a wannan shekarar ne suka fara amfani da sunan nan Shaidun Jehobah. (Isha. 43:10-12) Sai suka sanar wa duniya cewa suna alfaharin zama mutane masu ɗauke da “sunansa.” (A. M. 15:14) Sa’ad da muka yi tunani a kan yadda Jehobah ya kāre sunansa, muna tuna kalamin littafin Malakai 1:11 da ya ce: “Daga fitowar rana har faɗuwanta sunana ya ɗaukaka a wurin al’ummai.”
KA YI BIYAYYA DA SUNAN NAN JEHOBAH
16. Yaya ya kamata mu ji sa’ad da ake kiran mu da sunan nan Shaidun Jehobah?
16 Annabi Mikah ya ce: “Dukan kabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” (Mi. 4:5) A wajen mutanen Allah, kiransu da sunan Allah abin ɗaukaka ne mai girma. Hakan ya sa suka kasance da tabbaci cewa suna da tagomashin Allah. (Karanta Malakai 3:16-18.) Shin kana jin haka ne? Kana yin iya ƙoƙarinka don ka yi biyayya ga sunan Jehobah? Ka fahimci abin da yin hakan ya ƙunsa?
17. Mene ne yake nufi a yi biyayya ga sunan Jehobah?
17 Yin biyayya ga sunan Allah ya ƙunshi abubuwa uku. Na ɗaya, wajibi ne mu sanar da sunan nan, domin sai wanda ya “kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” (Rom. 10:13) Na biyu, wajibi ne mu kasance da irin halayen Jehobah, musamman ƙauna. Na uku, wajibi ne mu bi dokokin Allah kuma ta hakan mu daraja sunan Ubanmu. (1 Yoh. 4:8; 5:3) Za ka ci gaba da yin biyayya ga sunan Jehobah har abada?
18. Me ya sa duka waɗanda suke daraja sunan Jehobah suke da tabbaci game da nan gaba?
18 Nan ba da daɗewa ba, dukan waɗanda suka yi tawaye da Jehobah za su san kowaye ne shi. (Ezek. 38:23) Wannan ya ƙunshi mutane kamar Fir’auna da ya ce: “Wanene Ubangiji, har da zan ji muryatasa?” Amma daga baya, ya fahimci cewa Jehobah Allah ne mai girma. (Fit. 5:1, 2; 9:16; 12:29) Mun san Jehobah kuma mun zaɓi mu zama abokansa. Muna alfaharin zama mutanensa masu biyayya da ke ɗauke da sunansa. Muna ɗokin ganin abin da zai faru a nan gaba kuma mun tabbata da alkawarin da ke Zabura 9:10 da ta ce: ‘Waɗanda sun san sunanka za su dogara gareka; gama ba ka yarfar da masu-nemanka ba, ya Ubangiji.’
a An samo sunan Allah daga fi’ili na Ibrananci da yake nufi “na kasance.” Saboda haka, “Jehobah” yana nufin “Yana sa Ya Kasance.”
b Sunan nan Jehobah yana cikin nassosin Ibrananci da Kiristoci na farko suka yi amfani da shi. Mai yiwuwa sunan nan Jehobah yana cikin nassosi na farko na Septuagint, wato, Nassosin Ibrananci da aka fassara zuwa Helenanci.