Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/1 pp. 10-13
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SALIHI A CIKIN DUNIYA DA AKE MUGUNTA
  • “SAI KA YI JIRGI”
  • ‘KA SHIGA . . . CIKIN JIRGI’
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Nuhu Ya Gina Jirgi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Babbar Rigyawa—Su Wane Ne Suka Yi Biyayya? Su Wane Ne Ba Su Yi Ba?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Jirgin Nuhu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/1 pp. 10-13

KA YI KOYI DA IMANINSU

Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”

NUHU ya tashi tsaye don ya miƙe jikinsa. A ce kana ganin sa yana kallon babban jirgin sa’ad da yake zaune a kan babban katako don ya ɗan huta. Ƙaurin kwalta ya cika ko’ina kuma ana jin ƙarar kayayyakin aiki. Daga inda Nuhu yake zaune, yana ganin yadda yaransa suke aiki tuƙuru don su harhaɗa manyan katako. Shi da matarsa da kuma ’ya’yansa da matansu duk sun yi shekaru da yawa suna fama da wannan aikin. Sun riga sun gama gina wani gefen jirgin, amma akwai aiki birjik da ya rage!

Mutanen da suke ganin su sun ɗauka cewa su wawaye ne. Yayin da Nuhu da iyalinsa suka ci gaba da gina jirgin, mutane suka ci gaba da musu dariya domin suna ganin cewa rigyawa ba za ta taɓa mamaye duniya ba. Suna ganin abin da Nuhu yake musu gargaɗi a kai ba zai taɓa faruwa ba! Sun kasa sanin dalilin da ya sa wannan mutum da iyalinsa suke ɓata lokacinsu suna irin wannan aikin wofin. Amma Jehobah, Allahn Nuhu bai ɗauka haka ba.

Kalmar Allah ta ce: Nuhu ya yi “tafiya tare da Allah.” (Farawa 6:9) Mene ne hakan yake nufi? Ba wai Allah ya sauko duniya ko kuma Nuhu ya je sama domin su yi tafiya tare ba. Amma, Nuhu ya yi wa Allah biyayya da zuciya ɗaya kuma ya ƙaunaci Jehobah sosai har ya zama kamar shi da Jehobah suna takawa tare a matsayin aminai. Dubban shekaru bayan haka, Littafi Mai Tsarki ya ambata game da Nuhu cewa: “Ta bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta.” (Ibraniyawa 11:7, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya ya yi hakan? Mene ne za mu koya daga bangaskiyarsa?

SALIHI A CIKIN DUNIYA DA AKE MUGUNTA

Nuhu ya yi girma a lokacin da mutane a duniya suke daɗa mugunta. Haka ma ya faru a zamanin mahaifin kakansa Anuhu, wani mai adalci da ya yi tafiya tare da Allah. Anuhu ya yi annabci cewa za a hukunta mutane masu mugunta a duniya. Amma a zamanin Nuhu, mugunta ta daɗa ƙaruwa. Hakika a gaban Jehobah, duniya ta ɓace gaba ɗaya domin ta cika da mugunta. (Farawa 5:22; 6:11; Yahuda 14, 15) Me ya sa yanayin ya yi muni haka?

Wani mummunan bala’i ya auku tsakanin mala’ikun Allah. Wani daga cikin su ya yi tawaye da Jehobah, kuma ta wajen tsegunta Allah da kuma ruɗin Adamu da Hawwa’u su yi zunubi, ya mai da kansa Shaiɗan Iblis. A zamanin Nuhu wasu mala’iku sun bi irin wannan tafarkin kuma sun yi wa Jehobah tawaye. Sa’ad da mala’ikun sun ƙi da aikin da Jehobah ya ba su a sama, sun sauko duniya a matsayin ’yan Adam kuma suka auri kyawawan mata. Waɗannan mala’iku masu fahariya da suka yi tawaye sun yi mugun tasiri a kan mutane.—Farawa 3:1-5; 6:1, 2; Yahuda 6, 7.

Bugu da ƙari, saduwar da mala’ikun suka yi da mata ’yan adam ta haifar da yara ƙatta masu mugun ƙarfi. Littafi Mai Tsarki ya kira su Nephilim, wato, masu cin zalin mutane. Da yake Nephilim ɗin masu cin zali ne, sun sa zalunci ya daɗa yaɗuwa a duniya. Saboda haka, a gaban Mahaliccinmu, ‘muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.’ Jehobah ya ƙudura cewa zai halaka waɗannan mutane masu mugunta bayan shekaru 120.—Farawa 6:3-5.

Ka yi tunanin yadda yake da wuya mutum ya yi renon yara a irin wannan yanayin! Duk da haka, Nuhu ya yi renon yaransa da kyau. Ya auri mata mai hankali. Bayan Nuhu ya cika shekara 500, sai matarsa ta haifa masa ’ya’ya maza uku, wato, Shem, Ham da Japheth.a Nuhu da matarsa suka yi ƙoƙarin kāre ’ya’yansu daga miyagun mutane da ke kewaye da su. Ƙananan yara maza sukan yi sha’awar kallon “ƙarfafan mutane” da “mutane masu suna”; saboda haka, yana yiwuwa cewa yara a lokacin sun yi sha’awar waɗannan Nephilim sosai. Nuhu da matarsa ba za su iya kāre ’ya’yansu daga jin dukan labaran mugunta da ƙattan suke yi ba, amma za su iya koya musu gaskiya game da Jehobah, Allah wanda ya tsani mugunta. Sun bukaci su taimaki yaransu su gane cewa mugunta da tawaye da mutane suke yi suna ɓata wa Jehobah rai.—Farawa 6:6.

Iyaye a yau ma za su iya fahimtar irin yanayin da Nuhu da matarsa suka fuskanta. Duniya da muke ciki ma tana cike da mugunta da tawaye. Wasanni da aka tsara don yara ma sun ƙunshi hakan. Iyaye masu ƙaunar Jehobah za su yi ƙoƙari sosai su koya wa yaransu tafarkin Jehobah, Allah na salama, wanda zai kawar da dukan mugunta a nan gaba. (Zabura 11:5; 37:10, 11) Zai yiwu a koya wa yara abin da Jehobah yake bukata, ko a wannan duniya mai mugunta ma! Nuhu da matarsa sun yi nasara. Yaransu sun yi girma har sun zama mazajen kirki, kuma suka auri matan da suka so yin nufin Jehobah, Allah na gaskiya.

“SAI KA YI JIRGI”

Wata rana, rayuwar Nuhu ta canja gaba ɗaya. Jehobah ya bayyana wa wannan bawan da yake ƙauna cewa Yana son ya halaka miyagun mutane na zamanin. Allah ya umurci Nuhu: “Sai ka yi jirgi” da katako.—Farawa 6:14.

Wannan jirgin ba irin jirgi na zamani kamar yadda wasu suke tsammani ba. Tsarinsa yana nan kamar akwati mai girma ne kawai. Jehobah ya gaya wa Nuhu yadda ainihin girman jirgin zai kasance, yadda zai tsara jirgin gaba ɗaya da kuma yadda zai shafe jirgin da kwalta, ciki da waje. Kuma Allah ya gaya wa Nuhu dalilin cewa: “Ina kawo ruwan tufana a bisa duniya, . . . Dukan abin da ke cikin duniya za shi mutu.” Amma Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa: “Za ka shiga cikin jirgi kuma, da kai, da ’ya’yanka, da matarka, da matayen ’ya’yanka tare da kai.” An kuma gaya wa Nuhu ya shigar da dukan ire-iren dabbobi, bibiyu ko kuma bakwai-bakwai. Abubuwan da ke cikin jirgin ne kaɗai za su tsira wa Tufanar!—Farawa 6:17-20.

Nuhu ya sami babban aiki. Wannan jirgin zai zama babba sosai domin tsawonsa kafa 437 ne, faɗinsa kafa 73 kuma tsayinsa kafa 44 ne. Ya fi kowane jirgin ruwa na zamaninmu da aka yi da katako girma. Shin, Nuhu ya yi ƙoƙarin kauce wa wannan aikin ne, ya soma gunaguni game da ƙalubale da zai fuskanta ko kuma ya canja tsarin da aka ba shi domin ya sauƙaƙa wa kansa aikin ne? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa cewa: “Hakanan kuwa Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.”—Farawa 6:22.

Sun yi shekaru da yawa suna wannan aikin, mai yiwuwa shekaru 40 ko 50. Ya kamata su yanke itatuwa, su kai su zuwa inda za su yi amfani da su, su mai da su katako, sa’an nan su gyara da kuma harhaɗa su. Jirgin zai zama mai hawa uku da ɗakuna a ciki da kuma kofa a gefe. Hakika za a saka tagogi ta saman jirgin da kuma rufin da za a ɗan karkata domin kada ruwan sama ya taru a kan jirgin.—Farawa 6:14-16.

Yayin da shekaru suke shigewa kuma ana gama aikin a hankali, Nuhu ya yi farin ciki domin iyalinsa sun tallafa masa. Amma akwai wani sashen aikin da aka ba shi da ya fi gina jirgin wuya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (2 Bitrus 2:5) Da gaba gaɗi Nuhu ya ja-goranci iyalinsa wajen yi wa miyagun mutanen nan gargaɗi game da halaka da ke tafe. Mene ne mutanen suka yi? Shekaru bayan wannan lokacin, Yesu ya ce mutanen zamanin Nuhu “ba su” mai da hankali ba. Ya ce sun damu da harkokinsu na yau da kullum sosai, kamar ci da sha da kuma yin aure, kuma hakan ya sa ba su saurari Nuhu ba. (Matta 24:37-39) Hakika, mutane da yawa sun yi wa Nuhu da iyalinsa ba’a; mai yiwuwa wasu sun yi musu hamayya har ma da barazana.

Duk da haka, Nuhu da iyalinsa ba su ja da baya ba. Sun ci gaba da gina jirgin ko da yake mutanen da suke kewaye da su suna gani kamar yin hakan aikin wofi ne. Iyalan Kiristoci a yau za su iya koyan darussa sosai daga bangaskiyar Nuhu da iyalinsa, domin muna rayuwa ne a lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timotawus 3:1) Yesu ya annabta cewa zamaninmu zai kasance ɗaya da zamanin Nuhu, wato, lokacin da ya gina jirgi. Saboda haka, idan mutane sun yi mana hamayya ko ba’a ko kuma sun tsananta mana domin wa’azin da muke yi game da Mulkin Allah, ya kamata mu tuna da Nuhu. Ba mu ne muka fara fuskantar irin wannan yanayin ba.

‘KA SHIGA . . . CIKIN JIRGI’

Shekaru da dama sun shige kuma a hankali, aka gama gina jirgin. An yi wa Nuhu rashi sa’ad da ya kusa shekara 600. Mahaifinsa, Lamech, ya rasu.b Shekaru biyar bayan hakan, mahaifin Lamech, Methuselah, wato, kakan Nuhu ya rasu yana da shekaru 969. Shi ne ɗan Adam da ya fi kowa a duniya shekaru. (Farawa 5:27) An haifi Methuselah da Lamech a lokacin da Adamu yana raye.

A wannan shekarar ne Jehobah ya ba Uban iyalin nan Nuhu, wata saƙo cewa: ‘Ka shiga kai da dukan gidanka cikin jirgi.’ Allah ya sake gaya wa Nuhu ya saka dabbobi dabam-dabam cikin jirgin, wato, masu tsabta da za a iya yin hadaya da su bakwai-bakwai, sauran kuma bibiyu.—Farawa 7:1-3.

Shigar da su cikin jirgin abu ne da ba za a taɓa mantawa ba. Ɗarurruwan dabbobi suka yi ta shiga jirgin, wasu suna tafiya, wasu suka tashi fir suka shiga, wasu suna jan jiki, wasu suna tafiya da kyar, wasu kuma da sauri. Dabbobi kala-kala, manya da ƙanana kuma duka halayensu dabam-dabam. Nuhu bai lallaɓi dabbobin jejin kafin su shiga inda za a rufe su cikin jirgin ba. Labarin ya ce ‘suka shiga cikin jirgi wurin Nuhu.’—Farawa 7:9.

Wasu masu shakka za su iya yin tambayar nan: ‘Ta yaya hakan zai yiwu? Yaya za a ce waɗannan dabbobi da ke da halaye dabam-dabam sun zauna tare cikin lumana a wuri ɗaya?’ Ka yi la’akari da wannan: Horar da dabbobin da Mahaliccin sararin sama da kansa ya halitta za ta gagare shi ne? Ka tuna cewa Jehobah ne Allahn da ya raba Jan Teku kuma ya sa rana ta tsaya cak. Ashe ba zai iya yin dukan abubuwan da aka ambata cewa sun faru a cikin labarin Nuhu ba? Hakika, zai iya, kuma ya yi hakan!

A gaskiya, da a ce Allah ya so da ya cetar da dabbobin a wata hanya dabam. Amma, ya zaɓi hanya da za ta tuna mana cewa tun farko, Allah ya naɗa ’yan Adam su kula da dukan abubuwa masu rai a wannan duniya. (Farawa 1:28) Da haka, iyaye da yawa suna amfani da labarin Nuhu don su koya wa yaransu cewa Jehobah ya damu da mutane da kuma dabbobin da ya halitta.

Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa Rigyawar za ta auku bayan sati ɗaya. Babu shakka, iyalin Nuhu sun shaƙu sosai da hidimomi a wannan lokacin. Ka yi tunanin irin aikin da ke gaban su, za su shigar da kayansu da dabbobin da abincinsu kuma su shirya waɗannan abubuwan da kyau. Wataƙila matar Nuhu da matan Shem, Ham, da Japheth sun damu da yadda za su mai da jirgin wurin zama mai kyau.

Mene ne mutane da ke kewaye da su suka yi? “Ba su” mai da hankali ba duk da tabbacin da suka gani cewa Jehobah yana wa Nuhu da ayyukansa albarka. Sun lura cewa dabbobin suna shiga cikin jirgin. Amma bai kamata mu yi mamaki cewa sun nuna halin ko-in-kula ba. Mutane a yau ma ba sa mai da hankali ga tabbacin da suke gani cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Kuma kamar yadda manzo Bitrus ya annabta, masu ba’a za su yi wa waɗanda suke bin wannan gargaɗin dariya. (2 Bitrus 3:3-6) Hakazalika, mutane sun yi wa Nuhu da iyalinsa ba’a.

Yaushe suka daina ba’ar? Labarin ya nuna mana cewa muddin Nuhu da iyalinsa da kuma dabbobin suka shiga jirgin, sai “Ubangiji kuma ya rufe shi a ciki.” Idan da masu ba’a kusa da jirgin, da yadda Jehobah ya kulle ƙofar zai sa su su yi tunani. Amma idan abin da Jehobah ya yi bai jijjiga su, tabbas ne cewa ruwan saman ya yi, domin ya sauko kamar da bakin ƙwarya. Ruwan saman ya sauko kuma ya mamaye duniya kamar yadda Jehobah ya annabta cewa zai faru.—Farawa 7:16-21.

Jehobah ya yi farin ciki ne sa’ad da miyagun nan suka mutu? A’a! (Ezekiyel 33:11) Akasin haka, ya ba su dama su canja halinsu kuma su yi abin da ya kamata. Da za su iya canjawa kuwa? Rayuwar Nuhu ta ba da amsar wannan tambayar. Ta wajen yin tafiya da Jehobah da kuma yi masa biyayya a kome, Nuhu ya nuna cewa hakan zai iya yiwuwa. Saboda haka, bangaskiyarsa ta bayyana laifin mutanen zamaninsa; Nuhu ya nuna cewa zai yiwu mutum ya faranta wa Allah rai. Bangaskiyarsa ta cece shi da iyalinsa. Idan ka yi koyi da bangaskiyar Nuhu, za ka iya cetar da kanka da waɗanda kake ƙauna. Kamar Nuhu, za ka iya tafiya tare da Jehobah a matsayin amininka. Kuma wannan dangantakar za ta iya kasancewa har abada!

a Mutane a wancan zamanin suna shekaru da yawa fiye da mu kafin su mutu. Hakan ya yiwu ne wataƙila don bai daɗe ba da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi.

b Lamech ya ba ɗansa suna Nuhu, kuma mai yiwuwa ma’anar sunan shi ne “Hutu” ko kuma “Ta’aziya.” Lamech ya annabta cewa Nuhu zai aikata abin da sunansa yake nufi ta wajen kawo wa mutane hutu daga wahala da suke sha don an la’anta ƙasa. (Farawa 5:28, 29) Lamech ya mutu kafin annabcin nan ya cika.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba