Ka Kiyaye Gādonka Ta Wajen Yin Zaɓi Mai Kyau
“Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku rungumi abin da ke nagari.”—ROM. 12:9.
1, 2. (a) Mene ne ya taimaka maka ka tsai da shawarar bauta wa Allah? (b) Waɗanne tambayoyi game da gādo ne wannan talifin zai ba da amsarsu?
MUN yi zaɓi mai kyau na bauta wa Jehobah Allah da kuma bin sawun Yesu Kristi sosai, kuma miliyoyin mutane sun yi hakan. (Mat. 16:24; 1 Bit. 2:21) Muna ɗaukan shawarar da muka tsai da na keɓe kanmu ga Allah da muhimmanci sosai. Ba mu tsai da wannan shawarar bayan mun koyi gaskiya sama sama daga Nassosi ba. Maimakon haka, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kuma mun ƙarfafa bangaskiyarmu ga gādon da Jehobah ya yi alkawarinsa ga waɗanda suka koya game da shi ‘Allah makaɗaici mai-gaskiya, da kuma wanda ya aiko, Yesu Kristi.’—Yoh. 17:3; Rom. 12:2.
2 Idan muna son dangantakarmu da Jehobah ta ci gaba, dole mu riƙa yin zaɓin da ke faranta masa rai. Wannan talifin zai amsa waɗannan tambayoyi masu muhimmanci: Mene ne gādonmu? Yaya ya kamata mu ɗauki gādon? Ta yaya za mu tabbata cewa mun samu gādonmu? Mene ne zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau?
MENE NE MUKA GĀDA?
3. Wane gādo ne (a) shafaffu za su samu da (b) “waɗansu tumaki”?
3 Kiristoci kalilan suna da begen yin rayuwa a sama har abada. Za su samu gata na musamman na yin sarauta tare da Kristi a Mulkinsa. (1 Bit. 1:3, 4) Don su samu wannan gādon, wajibi ne a sake ‘haifar mutum.’ (Yoh. 3:1-3) Wane gādo ne “waɗansu tumaki” na Yesu waɗanda suke tarayya da mabiyansa shafaffu a yin wa’azin bishara ta Mulkin Allah suke da shi? (Yoh. 10:16) Waɗansu tumaki za su samu abin da Adamu da Hawwa’u ba su samu ba, wato, rai madawwami a cikin aljanna a duniya inda ba za a riƙa wahala da mutuwa ko makoki ba. (R. Yoh. 21:1-4) Yesu ya yi wa mai laifi da ya mutu tare da shi alkawari cewa: “Gaskiya ina ce maka, yau kana tare da ni cikin Aljanna.”—Luk 23:43.
4. Wace albarka ce muke da ita?
4 A yanzu ma muna moran wasu fannoni na gādonmu. Muna da kwanciyar hankali da kuma dangantaka ta kud da kud da Allah, domin mun ba da gaskiya ga “fansa da ke cikin Yesu Kristi.” (Rom. 3:23-25) Mun fahimci alkawura da ke cikin Kalmar Allah sosai. Ƙaunar ’yan’uwarmu a faɗin duniya tana sa mu farin ciki sosai. Gata ne sosai mu zama masu yin wa’azi game da Jehobah. Muna da dalilai masu kyau na nuna godiya sosai don gādonmu!
5. Mene ne Shaiɗan yake ƙoƙarin yi wa mutanen Allah, kuma me zai taimaka mana mu yi tsayayya da dabarunsa?
5 Domin mu tabbata cewa ba mu yi hasarar gādonmu ba, dole ne mu guji tarkunan Shaiɗan. Yana neman sa mutanen Allah su yi zaɓi da bai dace ba, don su rasa gādonsu. (Lit. Lis. 25:1-3, 9) Da yake Shaiɗan ya san cewa ƙarshensa ya kusa, yana daɗa ƙoƙari sosai don ya yaudare mu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17.) Idan muna son mu “yi tsayayya da dabarun Shaiɗan,” dole ne mu ci gaba da ɗaukan gādonmu da tamani. (Afis. 6:11) Za mu iya koyon darussa masu muhimmanci daga yadda Isuwa ɗan Yakubu ya ɗauki gādonsa.
KADA KA YI KOYI DA ISUWA
6, 7. Wane ne Isuwa, kuma wane gādo ne ya kamata ya samu?
6 Kusan shekara 4,000 da ta shige, Rifkatu ta haifi Isuwa da Yakubu. Waɗannan tagwayen sun bambanta sosai. “Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji,” amma “Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida.” (Far. 25:27, Littafi Mai Tsarki) An kira Yakubu kintsattse domin shi mai aminci ne kuma yin zunubi bai zama halinsa ba.
7 Ibrahim, kakan Isuwa da Yakubu ya mutu sa’ad da suke ’yan shekara 15, amma Jehobah bai manta da alkawarin da ya yi wa Ibrahim. Daga baya, Jehobah ya maimaita wa Ishaƙu wannan alkawarin cewa dukan al’umman duniya za su samu albarka ta wurin zuriyar Ibrahim. (Karanta Farawa 26:3-5.) Ta wannan hanyar, Allah ya gaya wa Ibrahim cewa ɗaya cikin ’ya’yansa zai zama ‘zuriyar’ da aka ambata a Farawa 3:15, wato, Almasihu. Tun da yake Isuwa ne ɗan fari na Ishaƙu, yana da damar samun alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim. Saboda haka, ya kamata Almasihu ya fito daga ’ya’yan Isuwa. Hakika, Isuwa zai samu gādo mai ban al’ajabi! Shin ya nuna godiya ga wannan gādon?
8, 9. (a) Wane zaɓi ne Isuwa ya yi a batun gādonsa na haihuwa? (b) Bayan shekaru da yawa, mene ne Isuwa ya fahimta game da zaɓinsa, kuma mene ne ya yi?
8 Wata rana da Isuwa ya dawo daga jeji, sai ya ga Yakubu yana “dahuwa.” Isuwa ya gaya masa, “ka cishe ni da wannan jan dahuwa, ina roƙonka: gama duk na yi yaushi.” Sai Yakubu ya ce masa: “Ka sayar mini da gādonka na haihuwa yau.” Wane zaɓi ne Isuwa ya yi? Abin mamaki, sai ya ce: “Wane amfani kuwa gādona na haihuwa za ya yi mini?” Hakika, Isuwa ya zaɓi jan miya maimakon gādonsa na haihuwa! Da yake Yakubu yana son ya tabbata cewa Isuwa yana son ya sayar da gādonsa na haihuwa, sai ya gaya wa Isuwa: “Sai ka rantse mini yau.” Ba tare da ɓata lokaci ba, Isuwa ya sayar da gādonsa na haihuwa. Bayan hakan, “Yaƙub kuma ya ba Isuwa gurasa da wasawasa; ya ci, ya sha, ya tashi, ya yi tafiyarsa, hakanan Isuwa ya waƙala gādonsa na haihuwa.”—Far. 25:29-34.
9 Bayan shekaru da yawa, sa’ad da Ishaƙu ya ga cewa ya kusan mutuwa, Rifkatu ta tabbata cewa Yakubu ya samu gādon haihuwa da Isuwa ya sayar masa. Sa’ad da Isuwa ya ankara cewa ya yi zaɓi marar kyau, sai ya roƙi Ishaƙu: “Ka albarkace ni, ya ubana, i, har da ni kuma . . . Ba ka rage mini wata albarka ba?” Sa’ad da Ishaƙu ya ce ba zai iya canja albarka da ya riga ya ba Yakubu ba, sai “Isuwa fa ya tada muryatasa, ya yi ta kuka.”—Far. 27:30-38.
10. Yaya Jehobah yake ɗaukan Isuwa da Yakubu, kuma me ya sa?
10 Mene ne za mu koya game da halin Isuwa daga wannan labarin? Isuwa ya nuna cewa gamsar da sha’awoyinsa, ya fi samun albarka a nan gaba sanadiyyar gādonsa na haihuwa muhimmanci. Bai daraja gādonsa na haihuwa ba kuma ba ya ƙaunar Allah sosai. Kuma bai yi tunanin yadda zaɓinsa zai shafi zuriyarsa ba. Akasi, Yakubu ya daraja gādonsa sosai. Alal misali, ya kasance a shirye ya bi gargaɗin iyayensa sa’ad da yake zaɓan matar da zai aura. (Far. 27:46–28:3) Yakubu ya zama kakan Almasihu don zaɓin da ya yi, ko da yake hakan yana bukatar haƙuri da kuma sadaukarwa. Ta yaya Allah ya ɗauki Isuwa da Yakubu? Ta bakin annabi Malakai, Jehobah ya ce: ‘Na ƙaunaci Yakubu; amma Isuwa na ƙi.’—Mal. 1:2, 3.
11. (a) Me ya sa Kiristoci za su amfana daga labarin Isuwa? (b) Me ya sa Bulus ya ambata fasikanci sa’ad da yake magana game da abin da Isuwa ya yi?
11 Shin labarin Isuwa zai amfani Kiristoci a yau? Ƙwarai kuwa. Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci su mai da hankali “kada wani mai-fasikanci ya kasance, ko kuwa wani marar-ibada kamar Isuwa, wanda ya sayarda gādonsa na ɗan fari saboda akushin abinci.” (Ibran. 12:16) Mene ne muka koya daga wannan gargaɗin? Wajibi ne mu riƙa daraja abubuwa masu tsarki domin mu yi tsayayya da gwaji kuma mu kiyaye gādonmu. Me ya sa Bulus ya ambata fasikanci sa’ad da yake magana game da abin da Isuwa ya yi? Domin idan muka aikata kamar Isuwa kuma muka bar sha’awoyi na jiki su rinjaye mu, zai yi mana sauƙi mu yi zunubi kamar fasikanci, kuma a sakamako mu rasa gādonmu.
KA SHIRYA ZUCIYARKA TUN DA WURI
12. (a) Yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin gwada kowannenmu? (b) Waɗanne misalai da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana sa’ad da aka jarabce mu?
12 A matsayin bayin Jehobah, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guji yanayin da zai iya sa mu yi lalata. Kuma ya dace mu yi addu’a ga Jehobah Allah don ya taimaka mana mu tsayayya wa gwaji. (Mat. 6:13) Yayin da muke ƙoƙartawa mu kasance da aminci a cikin wannan muguwar duniya, Shaiɗan ma yana ƙoƙari ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. (Afis. 6:12) Tun da yake shi ne allahn wannan zamanin, Iblis yana cin zarafin kasawar mutane don ya sa su yi zunubi. (1 Kor. 10:8, 13) Kuma yana ƙoƙarin sa kowannenmu ya yi hakan. A ce mun tsinci kanmu a cikin yanayin da ya ba mu zarafin gamsar da sha’awoyinmu a hanyar da ba ta dace ba kuma fa? Wane zaɓi ne za ka yi? Za ka zama kamar Isuwa wanda ya faɗa wa gwaji nan da nan? Ko kuwa za ka yi tsayayya da gwajin kuma ka gudu kamar yadda Yusufu ɗan Yakubu ya yi sa’ad da matar Fotifar ta jarabce shi?—Karanta Farawa 39:10-12.
13. (a) Yaya mutane da yawa a yau suka bi misalin Yusufu, kuma yaya wasu suka yi kamar Isuwa? (b) Mene ne ya kamata mu yi don kada mu bi misalin Isuwa?
13 ’Yan’uwanmu da yawa sun fuskanci gwaje-gwaje da suka sa su zaɓa ko za su bi misalin Isuwa ko kuma Yusufu. Yawancin mutane sun yi zaɓi mai kyau kuma suka faranta wa Jehobah rai. (Mis. 27:11) Amma, wasu sun bi misalin Isuwa kuma ba su kiyaye gādonsu ba. Ana yi wa ’yan’uwa da yawa horo ko yankan zumunci a kowace shekara domin sun yi lalata. Saboda haka, yana da muhimmanci mu shirya zuciyarmu tun da wuri domin mu iya shawo kan kowane gwaji a nan gaba! (Zab. 78:8) Za mu tattauna abubuwa biyu da za mu iya yi, don mu yi shirin shawo kan gwaji kuma mu yi zaɓi mai kyau nan gaba.
KA YI TUNANI KUMA KA YI SHIRI
14. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu “yi ƙyamar abin da ke mugu” kuma mu “rungumi abin da ke nagari”?
14 Mataki na farko da za mu ɗauka shi ne yin tunani game da sakamakon ayyukanmu. Idan muna ƙaunar Jehobah sosai, za mu daɗa daraja gādonmu. Idan muna ƙaunar mutum sosai, ba za mu so mu ɓata masa rai ba. Maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu sa shi farin ciki. Saboda haka, ya kamata mu yi tunani sosai game da sakamakon zunubi, wato, yadda za mu ɓata wa kanmu da kuma wasu rai idan muka faɗa wa gwaji. Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Yaya halina zai shafi dangantakata da Jehobah? Yaya zunubin zai shafi iyalina? Yaya zai shafi ’yan’uwana a cikin ikilisiya? Shin halina zai ɓata wa wasu rai?’ (Filib. 1:10) Muna iya tambayar kanmu kuma: ‘Shin kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa idan na yi lalata na ’yan mintoci, kuma na fuskanci sakamakonsa? Ina son in zama kamar Isuwa, wanda ya yi kuka sosai sa’ad da ya fahimci sakamakon zunubinsa?’ (Ibran. 12:17) Yin tunani sosai game da waɗannan tambayoyi zai taimaka mana mu “yi ƙyamar abin da ke mugu” kuma mu “rungumi abin da ke nagari.” (Rom. 12:9) Ƙaunarmu ga Jehobah ce musamman za ta sa mu kiyaye gādonmu.—Zab. 73:28.
15. Mene ne zai taimaka mana mu kasance a shirye mu yi tsayayya da gwaji kuma mu kiyaye dangantakarmu da Allah?
15 Mataki na biyu da za mu ɗauka shi ne mu shirya kanmu don mu yi tsayayya da gwaji. Jehobah ya yi mana tanadi masu yawa da za su sa mu kasance a shirye don mu yi tsayayya da gwaji a wannan duniyar, kuma mu kiyaye dangantakarmu da shi. Wannan tanadin ya ƙunshi yin nazarin Littafi Mai Tsarki da taron Kirista da yin wa’azi da kuma addu’a. (1 Kor. 15:58) A duk lokacin da muka gaya wa Jehobah yadda muke ji a addu’armu, kuma a duk lokacin da muka saka hannu a aikin wa’azi, muna shirya kanmu don mu yi tsayayya da gwaji. (Karanta 1 Timotawus 6:12, 19.) Wajibi ne mu ci gaba da yin ƙoƙari mu yi waɗannan abubuwa idan muna son mu kasance a shirye mu yi tsayayya da gwaji. (Gal. 6:7) An tattauna wannan a sura ta biyu na littafin Misalai.
KA CI GABA DA ‘NEMANTA’
16, 17. Mene ne zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau?
16 Misalai sura ta 2 ta ƙarfafa mu mu nemi hikima da fahimi. Waɗannan halayen za su taimaka mana mu san abin da ya dace da abin da bai dace ba, kuma za su taimaka mana mu kame sha’awoyinmu maimakon mu gamsar da su a hanyar da ba ta dace ba. Amma, za mu iya yin hakan idan muna a shirye mu yi ƙoƙari sosai. Littafi Mai Tsarki ya bayyana: ‘Ɗana, idan ka karɓi zantattukana, ka ɓoye dokokina a wurinka: Har da za ka karkata kunnenka ga hikima, ka maida zuciyarka ga fahimi: I, idan ka nace bin ganewa, ka tada muryarka garin neman fahimi: Idan ka neme ta kamar azurfa, ka biɗe ta kamar da a ke biɗan ɓoyayyun dukiya: Sa’annan za ka gane tsoron Ubangiji, ka ruski sanin Allah. Gama Ubangiji yana bada hikima, daga cikin bakinsa ilimi da fahimi su ke fitowa.’—Mis. 2:1-6.
17 Idan muka yi abin da aka kwatanta a waɗannan ayoyi, za mu yi zaɓi mai kyau. Za mu yi tsayayya da gwaji idan muka bar maganar Jehobah ta canja halayenmu, idan muka ci gaba da yin addu’a don samun ja-gorar Allah, kuma idan muka ci gaba da neman sani kamar muna neman ɓoyayyun dukiya.
18. Mene ne ka ƙudurta ka ci gaba da yi, kuma me ya sa?
18 Jehobah yana ba da sani da fahimi da hikima ga waɗanda suke nemansu da anniya. Idan muka neme su kuma muka yi amfani da su, dangantakarmu da Jehobah Allah za ta daɗa yin kyau. Sa’an nan, dangantakarmu ta kud da kud da Jehobah za ta kāre mu sa’ad da muka fuskanci gwaji. Idan muka kusaci Jehobah kuma muka ji tsoronsa, za mu yi aiki tuƙuru don mu guji yin zunubi. (Zab. 25:14; Yaƙ. 4:8) Abokantakarmu da Jehobah da kuma hikima da yake bayarwa za su taimaka mana mu yi zaɓin da zai sa shi farin ciki kuma mu kiyaye gādonmu.