Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 6/15 pp. 24-28
  • Ka Bar Horon Jehobah Ya Mulmula Ka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bar Horon Jehobah Ya Mulmula Ka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA MAGININ TUKWANE YAKE YIN AMFANI DA IKONSA
  • ALLAH BA YA SON KAI
  • JEHOBAH YA SAN SA’AD DA ZAI CANJA SHAWARARSA
  • KADA MU ƘI HORON DA JEHOBAH YAKE MANA
  • Ka Rika Amincewa da Gyarar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Bar Jehobah Ya Gyara Tunaninka da Halayenka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Kana Barin Jehobah Ya Mulmula Ka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Ji Shawara, Ka Karɓi Horo
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 6/15 pp. 24-28

Ka Bar Horon Jehobah Ya Mulmula ka

“Za ka bishe ni da shawararka, bayan wannan kuma za ka karɓe ni zuwa daraja.”—ZAB. 73:24.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya nuna cewa Jehobah ba ya tilasta wa mutane don ya mulmula su kuma ba ya son kai?

  • Me ya sa za mu yi farin ciki cewa Jehobah zai iya “tuba”?

  • Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da Jehobah ya yi mana gargaɗi ko kuma horo?

1, 2. (a) Mene ne muke bukatar mu yi don mu kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah? (b) Ta yaya binciken yadda wasu suka ɗauki horon Allah zai amfane mu?

MARUBUCIN wani zabura ya furta gaba gaɗin da yake da shi ga Jehobah, ya ce: “Amma ya yi mini kyau in kusanci Allah, na maida Ubangiji Yahweh mafakata.” (Zab. 73:28) Me ya sa ya furta hakan? Domin kafin wannan lokacin, ya fara yin baƙin ciki sa’ad da ya lura da yadda masu mugunta suke zama cikin lumana. Ya ce: “Banza na tsarkake zuciyata, na wanke hannuwana da rashin laifi.” (Zab. 73:2, 3, 13, 21) Amma, sa’ad da ya shiga “wuri mai-tsarki na Allah,” sai ya canja ra’ayinsa game da miyagu kuma ya ci gaba da kusantar Allah. (Zab. 73:16-18) Wannan marubucin zabura ya koyi darasi mai muhimmanci, wato idan mutum yana so ya ci gaba da moran abuta da Jehobah, wajibi ne ya kasance tare da bayinsa kuma ya riƙa ji da kuma bin shawararsa.—Zab. 73:24.

2 Muna so mu more dangantaka ta kud da kud da Allah mai rai da kuma gaskiya. Saboda haka, ya kamata mu riƙa bin shawara da kuma horonsa. Hakan zai taimaka mana mu zama mutanen da Jehobah ya amince da su. Allah ya nuna wa mutane da kuma al’ummai baki ɗaya jin ƙai a dā, ta wajen ba su damar karɓan horonsa. An rubuta labaransu a cikin Littafi Mai Tsarki “domin koyarwarmu” kuma “domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.” (Rom. 15:4; 1 Kor. 10:11) Za mu bincika wasu misalai a wannan talifin don mu fahimci yadda Jehobah yake tunani da kuma yadda za mu amfana idan ya mulmula mu.

YADDA MAGININ TUKWANE YAKE YIN AMFANI DA IKONSA

3. Ta yaya aka kwatanta yadda Jehobah yake nuna iko a kan mutane a littafin Ishaya 64:8 da kuma Irmiya 18:1-6? (Ka duba hoto na farko.)

3 Littafin Ishaya 64:8 ya kwatanta yadda Jehobah yake nuna ikonsa a kan mutane da kuma al’ummai, ya ce: “Ya Ubangiji, kai ubanmu ne, mu yimɓu ne, kai ne mai-yin tukwane da mu: mu dukanmu kuma aikin hannunka ne.” Mai tukwane yana da ikon yin duk irin tukunyar da yake so da yumɓu. Yumɓun ba zai iya zaɓan abin da za a yi da shi ba. Hakan ma yake tsakanin ’yan Adam da Allah. Kamar yadda yumɓu ba zai iya gaya wa mai tukunya abin da za a yi da shi ba, haka ma ɗan Adam ba zai iya gaya wa Allah yadda zai mulmula shi ba.—Karanta Irmiya 18:1-6.

4. Shin Jehobah yana mulmula mutane ko kuma al’ummai ƙarfi da yaji? Ka bayyana.

4 Jehobah ya mulmula Isra’ilawa kamar yadda magini yake yin tukunya. Amma, Jehobah ya bambanta da maginin tukwane ɗan Adam. Ta yaya? Maginin tukwane zai iya yin duk abin da ya so da yumɓu, amma Jehobah ba ya yin hakan. Ba ya mulmula wasu mutane ko kuma al’ummai su zama nagargaru wasu kuma miyagu. Jehobah ya ba mutane ’yancin yin zaɓi. Ba ya tilasta musu su yi masa biyayya, maimakon haka, ya ƙyale su su zaɓa ko suna so ya mulmula su.—Karanta Irmiya 18:7-10.

5. Ta yaya Jehobah yake nuna ikonsa idan mutane ba su ƙyale shi ya mulmula su ba?

5 Idan mutum ya ƙi ya ƙyale Jehobah, Babban Magini ya mulmula shi kuma fa? Ta yaya Jehobah zai nuna ikonsa a matsayin magini? Ka yi la’akari da abin da magini yakan yi da yumɓun da bai iya fitar da ainihin abin da ya so ba. Maginin zai iya gina wani abu da yumɓun ko kuma ya zubar da shi. Kasawar maginin ne ba yumɓun ba. Amma ba hakan yake da Jehobah ba. (K. Sha 32:4) Idan mutum bai ƙyale Jehobah ya mulmula shi ba, mutumin ne yake da laifi. Yadda Jehobah yake mulmula mutane ya dangana ga yadda suka aikata. Waɗanda suka ƙyale Jehobah ya mulmula su, sukan zama da amfani a gare shi. Alal misali, Kiristoci shafaffu “tukwane na jinƙai” ne waɗanda aka mulmula sun zama ‘tukwane zuwa daraja.’ Akasin haka, waɗanda suka ƙi yin biyayya ga Jehobah sun zama “tukwane na fushi shiryayyu ga halaka.”—Rom. 9:19-23.

6, 7. Mene ne Sarki Dauda da kuma Saul suka yi sa’ad da Jehobah ya gargaɗe su?

6 Hanya ɗaya da Jehobah yake mulmula mutane ita ce ta wajen ba su shawara ko kuma yi musu horo. Alal misali, ka yi la’akari da yadda Jehobah ya mulmula Saul da Dauda, sarakunan Isra’ila. Sa’ad da Sarki Dauda ya yi zina da Bath-sheba, munanan sakamakon sun shafe shi da kuma wasu. Jehobah ya yi wa Dauda horo duk da cewa shi sarki ne. Ya aiki annabi Nathan ya gargaɗi Dauda. (2 Sam. 12:1-12) Mene ne Dauda ya yi? Ya yi baƙin ciki sosai kuma ya tuba. Hakan ya sa Jehobah ya yi masa jin ƙai.—Karanta 2 Sama’ila 12:13.

7 Amma, Sarki Saul wanda ya yi sarauta kafin Dauda ya ƙi bin gargaɗi. Jehobah ya aiki Sama’ila ya gaya wa Sarki Saul cewa ya halaka dukan Amalekawa da dabbobinsu. Amma, Saul ya yi kunne uwar shegu ga dokar Jehobah. Bai kashe Sarki Agag da kuma dabbobinsa masu koshin lafiya ba. Me ya sa? Wataƙila domin yana son mutane su girmama shi. (1 Sam. 15:1-3, 7-9, 12) Mene ne Saul ya yi sa’ad da Jehobah ya gargaɗe shi? Ya ƙi ya ƙyale Babban Magini ya mulmula shi. Ya ba da hujja don yin rashin biyayya ga umurnin Jehobah. Ya ce abin da ya yi ba laifi ba ne domin zai yi hadaya da dabbobin, kuma bai saurari gargadin da Sama’ila ya yi masa ba. Jehobah ya ƙi da Saul a matsayin sarki, kuma ya daina dangantaka da shi.—Karanta 1 Sama’ila 15:13-15, 20-23.

ALLAH BA YA SON KAI

8. Mene ne za mu iya koya daga abin da Isra’ilawa suka yi sa’ad da Jehobah ya so ya mulmula su?

8 Jehobah ya ƙyale al’ummai su zaɓa ko suna so ya mulmula su. Bayan Jehobah ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, sai suka zama al’ummarsa ta musamman a shekara ta 1513 kafin zamaninmu. Jehobah ya yi alkawarin zai riƙa mulmula su. Amma, mutanen sun ƙi kuma suka ci gaba da yin mugunta. Har ma sun bauta wa allolin ƙarya. Jehobah ya aika annabawa sau da sau don su ja kunnuwansu, amma sun ƙi jin kira. (Irm. 35:12-15) Saboda haka, Jehobah ya yi musu horo mai tsanani. Sai Assuriyawa suka halaka ƙabilu goma da ke arewancin Isra’ila, kuma Babiloniyawa suka halaka ƙabilu biyu da ke kudancin Yahuda. Ya kamata mu koya darassi sosai daga wannan labarin. Idan muna so mu amfana daga yadda Jehobah yake mulmula mu, wajibi ne mu saurare shi.

9, 10. Mene ne mutanen Nineba suka yi sa’ad da Jehobah ya gargaɗe su?

9 Jehobah ya kuma ƙyale mutanen da ke babban birnin Assuriya, wato Nineba su zaɓa ko za su bi umurninsa ko a’a. Jehobah ya ce wa Yunana: “Tashi, ka tafi Nineveh, babban birnin nan, ka tada murya, ka faɗace ta; gama muguntassu ta hau gaba gareni.”—Yun. 1:1, 2; 3:1-4.

10 Sa’ad da mutanen Nineba suka ji umurnin Jehobah, sai ‘suka gaskata Allah.’ Sun yi azumi kuma sun yafa tufafin makoki don su nuna cewa sun tuba da gaske. Sarkin ƙasar ma “ya sauka daga kursiyinsa, ya tuɓe rigarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.” Mutanen Nineba sun ƙyale Jehobah ya mulmula su kuma sun tuba. Shi ya sa Jehobah bai halaka birnin ba.—Yun. 3:5-10.

11. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya bi da al’ummar Isra’ila da kuma Nineba?

11 Jehobah ya yi wa Isra’ilawa horo, duk da cewa su al’umma ce ta musamman a gare shi. Mutanen Nineba ba al’umma ta musamman ba ce, amma sun ƙyale Jehobah ya mulmula su. Saboda haka, Jehobah ya yi musu jin ƙai kuma bai halaka su ba. Waɗannan misalai biyu sun nuna cewa Allahnmu Jehobah “ba ya tara.”—K. Sha 10:17.

JEHOBAH YA SAN SA’AD DA ZAI CANJA SHAWARARSA

12, 13. (a) Me ya sa Jehobah yake canja ra’ayinsa sa’ad da mutane suka ƙyale shi ya mulmula su? (b) Ta yaya Jehobah ya canja shawararsa game da Saul da kuma Nineba?

12 Jehobah zai iya canja ra’ayinsa game da mutane idan suka canja ayyukansu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya “tuba” da naɗa Saul a matsayin sarkin Isra’ila. (1 Sam. 15:11) Kuma sa’ad da mutanen Nineba suka tuba kuma suka daina aikata mugunta, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah kuwa ya tuba ga barin masifar da ya ce za ya yi masu; ba ya kuwa aikata ba.”—Yun. 3:10.

13 Mene ne furucin nan Jehobah ya “tuba” yake nufi? Hakan yana nufin cewa ya canja ra’ayinsa ko kuma shawarar da ya tsai da game da mutum. Jehobah ne ya naɗa Saul sarki, kuma shi ne ya cire shi. Shin hakan ya nuna cewa Jehobah ya yi kuskure ne da ya naɗa Saul sarki? A’a, Saul ya yi rashin biyayya, shi ya sa Jehobah ya ƙi da shi. Allah ya kuma canja shawararsa game da mutanen Nineba. Jehobah mai alheri ne da jin ƙai, kuma yana a shirye ya canja ra’ayinsa game da mai zunubin da ya tuba. Sanin hakan yana ƙarfafa mu sosai.

KADA MU ƘI HORON DA JEHOBAH YAKE MANA

14. (a) Ta yaya Jehobah yake mulmula mu a yau? (b) Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da Jehobah yake mulmula mu?

14 A yau, Jehobah yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma ƙungiyarsa wajen mulmula mu. (2 Tim. 3:16, 17) Ya kamata mu amince da duk gargaɗi ko kuma horon da aka mana ta waɗannan hanyoyin. Ko da mun yi shekaru muna bauta wa Jehobah, kuma komen gatan da muke da shi a cikin ikilisiya, zai dace mu ci gaba da jin gargaɗinsa. Idan muka ƙyale Jehobah ya mulmula mu, za mu zama mutanen da yake so.

15, 16. (a) Yaya mutum zai iya ji idan ya rasa gatansa a cikin ikilisiya? Ka ba da misali. (b) Mene ne zai taimaka mana mu shawo kan kunya sa’ad da aka yi mana horo?

15 Jehobah yana yi mana horo a hanyoyi da yawa. Yana koyar da mu kuma yana taimaka mana mu daidaita tunaninmu. A wani lokaci kuma, yana iya yi mana horo don mun taka dokarsa. Hakan yana iya sa mu rasa gatanmu a cikin ikilisiya. Ga misalin wani dattijo mai suna Dennis.a An yi masa horo don ya yi kuskure a sha’anin kasuwanci. Yaya Dennis ya ji sa’ad da aka sanar wa ikilisiya cewa shi ba dattijo ba ne kuma? Dennis ya ce: “Na ji kamar na gama yawo. A cikin shekaru 30 da suka shige, na more gata dabam-dabam. Na yi hidimar majagaba na kullum da hidima a Bethel. Na zama bawa mai hidima da dattijo, kuma ban daɗe da ba da jawabina na farko a taron gunduma ba. Amma yanzu, dukan waɗannan gatan sun bi ruwa. Na ji kunya sosai, kuma na ji kamar ba ni da wani amfani a cikin ƙungiyar Jehobah.”

16 Dennis yana bukatar ya canja halinsa. Amma, mene ne ya taimaka masa ya shawo kan kunyar da yake ji? Ya ce ya ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah kullum da zuwa wa’azi a kai a kai da kuma halartar dukan taro. Ya amfana sosai daga yadda ’yan’uwa suka ƙarfafa shi da kuma abin da ya karanta a cikin littattafanmu. Dennis ya ce: “Na ɗauki talifin nan ‘Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma? da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2009 a matsayin wasiƙar da ke ɗauke da amsar addu’ata. Wannan talifin ya koya mini cewa ya kamata in yi amfani da zarafin da nake da shi yanzu, wajen ƙarfafa dangantakata da Jehobah.’” Ta yaya Dennis ya amfana daga horon? Bayan ’yan shekaru, Dennis ya ce: “Jehobah ya sake albarkace ni da gatan zama bawa mai hidima a cikin ikilisiya.”

17. Ta yaya yankan zumunci zai iya taimaka wa mai zunubi? Ka ba da misali.

17 Yankan zumunci ma horo ne daga Jehobah. Yana kāre ikilisiya daga mummunar tasiri, kuma yana taimaka wa mutum mai zunubin ya tuba. (1 Kor. 5:6, 7, 11) An yi wa wani mai suna Robert yankan zumunci har kusan tsawon shekara 16. A duk tsawon shekarun nan, iyayensa da kuma ’yan’uwansa sun ƙi su yi cuɗanya da shi, har ma da gaisuwa da shi kamar yadda aka faɗa cikin Littafi Mai Tsarki. Yanzu an yi shekaru da yawa tun da aka dawo da Robert kuma yana samun ci gaba a cikin ikilisiya. Sa’ad da aka tambaye shi abin da ya taimake shi ya komo ga Jehobah da kuma mutanensa bayan waɗannan shekarun, sai ya ce matakin da iyayensa da ’yan’uwansa suka ɗauka ne ya taimake shi. Ya ce: “Da a ce iyayena da ’yan’uwana sun yi cuɗanya da ni, ko da na ɗan lokaci ne kawai ko kuma sun kira ni su ji ko ya nake, da ban yi kewarsu ba, balle ma in so komowa ga Jehobah.”

18. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da Allah yake mulmula mu?

18 Wataƙila ba za a yi mana irin horon da aka yi wa wannan ɗan’uwan ba. Amma sa’ad da Allah yake mulmula mu da kuma yi mana horo, ya kamata mu tambayi kanmu, Shin zan amince da horo kamar Dauda? Ko kuma zan ƙi saurarawa kamar Saul? Jehobah Babban Magini, shi ne Ubanmu. Kada ka manta cewa wanda “ya ke ƙauna shi ya ke tsauta ma, kamar yadda uba ya kan yi ma ɗan da ya ke jin daɗinsa.” Saboda haka, “kada ka rena koyarwar Ubangiji: kada ka yi kasala kuma da tsautawarsa.”—Mis. 3:11, 12.

a An canja sunayen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba