Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/1 p. 16
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Albishiri Daga Allah!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/1 p. 16

AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Allah yana jin kowane irin addu’a ne?

Allah yana jin addu’ar mutane daga dukan al’ummai. (Zabura 145:18, 19) A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ƙarfafa mu mu gaya masa duk abin da ke damun mu. (Filibiyawa 4:6, 7) Duk da haka, akwai wasu addu’o’in da ba sa faranta wa Allah rai, alal misali, addu’o’in da aka haddace kuma ake maimaitawa.—Karanta Matta 6:7.

Ƙari ga haka, Jehobah ba ya jin addu’o’in waɗanda suke yin watsi da dokokinsa. (Misalai 28:9) Alal misali, a zamanin dā, Allah ya ƙi jin addu’ar Isra’ilawa da suka yi kisan kai. A gaskiya, dole mu cika wasu farillai idan muna son Allah ya ji addu’armu.—Karanta Ishaya 1:15.

Mene ne ya wajaba mu yi don Allah ya saurare mu?

Idan ba mu da bangaskiya, ba zai yiwu mu yi wa Allah addu’a ba. (Yaƙub 1:5, 6) Wajibi ne mu gaskata cewa Allah ya wanzu kuma yana kula da mu. Bangaskiyarmu za ta ƙaru idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki domin ta wajen ganin tabbaci da ke cikin Kalmar Allah ne muke kasancewa da bangaskiya.—Karanta Ibraniyawa 11:1, 6.

Ya kamata mu yi addu’a daga zuciya kuma mu yi hakan cikin tawali’u. Yesu Ɗan Allah ma ya kasance da tawali’u sa’ad da yake addu’a. (Luka 22:41, 42) Saboda haka, maimakon mu riƙa gaya wa Allah abin da zai yi, zai dace mu yi ƙoƙarin fahimtar ƙa’idodinsa ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi hakan, za mu iya yin addu’a a hanyar da ta jitu da nufin Allah.—Karanta 1 Yohanna 5:14.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 17 na wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa

Za ka iya sauko da mujallar nan daga dandalin www.pr418.com/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba