Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/1 p. 13
  • “Allah Yana Son Mai Bayarwa da Daɗin Rai”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Allah Yana Son Mai Bayarwa da Daɗin Rai”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Nuna Cewa Kana Ƙaunar Allah
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Allah Yana Son Mai Bayarwa da Dadin Rai
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Yadda Za Ka San Kyauta Mafi Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/1 p. 13

KA KUSACI ALLAH

“Allah Yana Son Mai Bayarwa da Daɗin Rai”

Wace irin kyauta ce idan aka yi maka za ka yi godiya sosai? Hakika yawancinmu za mu yi farin ciki sosai idan wani ya ba mu kyauta domin yana ƙaunarmu, ba don kawai ya rasa na yi ba. Irin muradin da mutum yake da shi sa’ad da yake bayarwa yana da muhimmanci sosai a gare mu. Daɗin daɗawa ma, Allah yana lura da hakan. Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya faɗa a littafin 2 Korintiyawa 9:7.

Me ya sa Bulus ya rubuta waɗannan kalmomi? Yana so ne ya ƙarfafa Kiristoci da ke Korinti su tallafa wa ’yan’uwansu mabukata da ke ƙasar Yahudiya. Shin ya yi ƙoƙarin tilasta musu su yi bayarwa ne? A’a. Akasin haka, ya ce: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” Bari mu bincika abin da Bulus ya faɗa da kyau.

“Yadda ya annita a zuciyarsa.” Manzo Bulus ya ce Kirista na gaske yana bayarwa domin ya ƙudura “a zuciyarsa” ya yi hakan. Ƙari ga hakan, Kirista yakan yi tunani sosai a kan bukatun ’yan’uwansa masu bi. Wani masani ya ce kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “annita” tana nufin mutum ya “shirya tun da wuri” kafin ya yi wani abu. Saboda haka, Kirista yakan yi tunani a kan bukatun ’yan’uwansa masu bi don ya ga yadda zai iya taimaka musu.—1 Yohanna 3:17.

‘Ba kamar ta dole ba.’ Manzo Bulus ya bayyana abubuwa biyu da za su dace Kiristoci su guji yi idan suna bayarwa. Wato kada su yi bayarwa da zuciya biyu ko kuma kamar ana tilasta musu. Mutumin da ke bayarwa da zuciya biyu ko kamar ana tilasta masa “yana baƙin ciki cewa za a raba shi da kuɗinsa,” in ji wata majiya. Irin wannan mutumin yana ji kamar ana matsa masa ne ya ba da kyauta. Shin za ka so irin mutumin nan ya yi maka kyauta?

“Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” Bulus ya ce idan Kirista yana so ya yi bayarwa, ya kamata ya yi hakan da daɗin rai ko kuma farin ciki. Hakika bayarwa da muradi mai kyau ne yake kawo farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Mai bayarwa da daɗin rai ba zai iya ɓoye murnarsa ba. Kalmar Helenanci da ke nufin “daɗin rai” tana kwatanta yadda mai bayarwar yake ji a cikin zuciyarsa kuma hakan zai bayyana a fuskarsa. Mutumin da ke bayarwa da daɗin rai yana sa mu da kuma Allah farin ciki. Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah yana ƙaunar mutanen da suke son bayarwa.”—Juyin Contemporary English Version.

“Allah yana ƙaunar mutanen da suke son bayarwa”

Wannan furucin da Allah ya hure Bulus ya rubuta shi ne ƙa’idar da ya kamata Kirista ya riƙa la’akari da ita sa’ad da yake bayarwa. Ko da muna yin amfani da lokacinmu ko ƙarfinmu ko dukiyarmu wajen taimaka wa mutane musamman ma mabukata, ya kamata mu yi hakan ne da son rai kuma don muna so mu taimake su. Irin wannan bayarwar za ta sa mu farin ciki kuma za ta sa Allah ya ƙaunace mu domin “yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”

Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Nuwamba

Titus 1-3; Filimon 1-25; Ibraniyawa 1-13–Yaƙub 1-5

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba