Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 pp. 17-21
  • Shin Ka Yi Canje-Canje Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Ka Yi Canje-Canje Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME YA SA MUKE BUKATAR CANJE-CANJE?
  • MENE NE MUKE BUKATAR MU CANJA?
  • YADDA AKE YIN CANJE-CANJEN
  • Mu Kawar da Kowane Ra’ayin da Ya Saba wa Na Allah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Rika Amincewa da Gyarar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • “Ku Yarda Allah Ya Canja Ku Ya Sabunta Tunaninku da Hankalinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Wane ne Yake Sarrafa Tunaninka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 pp. 17-21

Shin Ka Yi Canje-canje Kuwa?

“Ku juyu bisa ga sabontar azancinku.”—ROM. 12:2.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa ya kamata dukan Kiristoci su yi canje-canje?

  • Waɗanne canje-canje ne ya wajaba dukan Kiristoci su yi?

  • Mene ne zai taimaka mana mu yi canje-canjen da muke bukata?

1, 2. Ta yaya yadda aka tarbiyyar da mu da kuma inda muka girma suke shafar mu?

YADDA aka tarbiyyar da mu yana shafar rayuwarmu sosai. Abokanmu da al’adarmu da kuma inda muka girma sukan shafi yadda muke yin ado da irin abincin da muke ci da kuma halayenmu.

2 Amma, akwai wasu abubuwa da suke fi yin ado da kuma irin abincin da muke ci muhimmanci. Alal misali, yayin da muke girma, an koya mana cewa wasu abubuwa suna da kyau, wasu kuma ba su da kyau. Amma, ra’ayoyin mutane game da mugunta da nagarta sun bambanta. Lamirinmu ma yana shafar irin zaɓin da muke yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a, kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a.” (Rom. 2:14) Da a ce babu takamaiman doka daga Allah, shin zai dace ne mu yi rayuwa kawai yadda aka tarbiyyar da mu da kuma yadda mutane a inda muka girma suke yi?

3. Waɗanne dalilai biyu ne suka sa Kiristoci ba sa bin mizanan wannan duniyar?

3 Akwai aƙalla dalilai biyu da suka sa Kiristoci ba sa yin hakan. Na farko, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Akwai wata hanya wadda ta ke da alamar kirki ga mutum, amma matuƙarta tafarkun mutuwa ce.” (Mis. 16:25) Saboda mu ajizai ne, ba za mu iya ja-gorar kanmu da kyau ba. (Mis. 28:26; Irm. 10:23) Na biyu kuma, Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan ne “allah na wannan zamani.” Shi ne yake sarrafa al’amuran da suke gudana a duniya, wato ra’ayoyin mutane game da mugunta da nagarta da kuma mizanan da suke bi. (2 Kor. 4:4; 1 Yoh. 5:19) Saboda haka, idan muna so Jehobah ya amince da mu kuma ya albarkace mu, wajibi ne mu bi shawarar da ke littafin Romawa 12:2.—Karanta.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 A wannan talifin za mu tattauna batutuwa uku masu muhimmanci da aka ambata a littafin Romawa 12:2. Na ɗaya, me ya sa muke bukata mu yi canje-canje? Na biyu, me muke bukatar mu canja? Na uku, ta yaya za mu iya yin canje-canje? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

ME YA SA MUKE BUKATAR CANJE-CANJE?

5. Bulus ya rubuta umurnin da ke littafin Romawa 12:2 ga su wane ne?

5 Manzo Bulus ya rubuta wannan wasiƙa ga ’yan’uwa da ke Roma a shekara ta 56 a zamaninmu don Kiristoci shafaffu da ke birnin, ba don dukan mazaunan Roma ba. (Rom. 1:7) Ya umurce su cewa su yi canji kuma ‘kada su kamantu bisa ga wannan zamani.’ Ga Kiristoci da ke Roma a lokacin, “wannan zamani” ya ƙunshi ƙa’idodi da al’adu da halaye da kuma irin adon mutanen Roma. Bulus ya ce ‘kada su kamantu,’ domin har ila akwai ’yan’uwa da suke bin halayen mutanen wannan zamanin. Ta yaya hakan ya shafe su?

6, 7. Wane ƙalubale ne Kiristoci da ke Roma suka fuskanta a zamanin Bulus?

6 A yau, sa’ad da masu yawon zagaya suka je birnin Roma, sukan ga kangayen haikali da kaburbura da kuma mutum-mutumi da aka gina tun shekaru da dama da suka shige. Waɗannan kangayen sun taimaka mana mu daɗa sanin irin rayuwar da mutanen birnin Roma ta dā suka yi da kuma ibadarsu. Ƙari ga haka, littattafan tarihi suna ɗauke da labaru game da irin mugun wasanni da sukuwa da kuma wasu wasannin kwaikwaiyo da kaɗe-kaɗe marasa ɗa’a da suke yi. Roma birnin kasuwanci ne mai ni’ima sosai inda akwai zarafin samun wadata.—Rom. 6:21; 1 Bit. 4:3, 4.

7 Duk da cewa Romawa suna da haikali da yawa cike da alloli iri-iri, yawancinsu ba su da dangantaka ta kud da kud da allolinsu. A ganinsu, addini ta ƙunshi yin bikin al’ada kamar su bikin haihuwa ko na aure ko kuma na jana’iza. Abin da rayuwarsu ta ƙunsa ke nan. Babu shakka, waɗannan abubuwan sun zama wa Kiristoci da ke Roma ƙalubale. Yawancinsu suna bauta wa allolin ƙarya sa’ad da suke girma, saboda haka, suna bukata su yi canje-canje don su zama Kiristoci na gaskiya. Bayan sun yi baftisma kuma, suna bukata su ci gaba da yin canje-canje.

8. Ta yaya wannan duniyar ta kasance wuri mai haɗari wa Kiristoci a yau?

8 Kamar birnin Roma ta dā, duniyar nan wuri ne mai haɗari wa Kiristoci a yau. Me ya sa muka ce hakan? Domin miyagun halaye sun zama ruwan dare a duniya. (Karanta Afisawa 2:2, 3; 1 Yohanna 2:16.) Sha’awoyi da tunani da ƙa’idodi da kuma ɗabi’un da ke tasiri a wannan duniyar suna iya shafar mu, kuma idan hakan ya faru, za mu soma bin ra’ayinta. Saboda haka, muna bukatar mu yi biyayya ga umurnin nan da ya ce, ‘kada mu kamantu bisa ga wannan zamanin,’ kuma mu yi canje-canje. Me muke bukatar mu canja?

MENE NE MUKE BUKATAR MU CANJA?

9. Waɗanne canje-canje ne mutane da yawa suka yi kafin su yi baftisma?

9 Yayin da mutum ya soma nazari da kuma bin koyarwar Littafi Mai Tsarki, zai fara kusantar Jehobah. Hakan zai sa ya daina bin addinin ƙarya kuma ya yi canje-canje a rayuwarsa. Zai ƙoƙarta ya sabonta halayensa kuma ya yi koyi da Yesu. (Afis. 4:22-24) Muna farin cikin ganin dubban mutane da suke samun irin wannan ci gaban kowace shekara. Waɗannan mutanen suna keɓe kansu ga Jehobah kuma suna yin baftisma. Babu shakka, hakan yana faranta wa Jehobah rai. (Mis. 27:11) Amma, shin waɗannan canje-canje ne kaɗai muke bukata mu yi?

10. Mene ne bambancin samun ci gaba da kuma yin canje-canje?

10 Yin canje-canje yana bukatar fiye da samun ci gaba. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce wannan furucin “ku juyu” da aka ambata a littafin Romawa 12:2, ya ƙunshi sabonta ko kuma canja yadda muke yin tunani ta wajen barin ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora. Saboda haka, canje-canjen da Kirista yake bukatar ya yi, ba daina halin banza ko ɗanyen magana ko kuma ɗabi’a marar kyau kaɗai ba. Wasu mutane da ba su san koyarwar Littafi Mai Tsarki ba suna ƙoƙarin guje wa waɗannan mugayen abubuwan. Mene ne muke bukata mu yi a matsayin Kiristoci don mu yi canje-canje?

11. Mene ne Bulus ya ce mutum yake bukata ya yi don ya yi canje-canje?

11 Bulus ya ce: “Ku juyu bisa ga sabontar azancinku.” ‘Azanci’ yana nufin yadda muke yin tunani. Amma a Littafi Mai Tsarki, hakan ya kunshi abubuwan da muke yin tunani a kai da halayenmu da kuma hankalinmu. A somawar wasiƙarsa ga ’yan’uwa da ke Roma, Bulus ya kwatanta mutanen da ke da “sangartacen hankali.” Irin waɗannan mutanen ne suke aika “rashin adalci, mugunta, ƙyashi, ƙeta; cike da kishi, kisankai, husuma, makirci,” da kuma wasu miyagun ayyuka. (Rom. 1:28-31) Babu shakka, hakan zai sa mu fahimci abin da ya sa Bulus ya umurci Kiristoci da ke zama a Roma ‘su juyu bisa ga sabontar azancinsu.’

‘Bari dukan hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gare ka.’—Afis. 4:31

12. Wane irin tunani ne mutane a yau suke yi, kuma me ya sa hakan yake da haɗari ga Kiristoci?

12 Abin baƙin ciki, muna zama ne a wannan duniyar da ke cike da mutane masu irin halayen da Bulus ya kwatanta. Waɗannan mutanen suna ganin cewa bin mizanai da kuma ƙa’idodi tsohon yayi ne kuma ba sa so wani ya tilasta musu su bi ƙa’idodi ko mizanai. Malamai da iyaye da yawa suna ƙyale yara su yi duk abin da suka ga dama. Sukan koya musu cewa kowa yana da ’yancin zaɓar abin da yake so ya yi. Irin waɗannan mutanen sun gaskata cewa babu yadda za a san abu mai kyau da marar kyau. Mutane da yawa da suke da’awa cewa sun yi imani da Allah suna ganin cewa ba sa bukata su bi umurnin Allah. (Zab. 14:1) Irin wannan halin haɗari ne ga Kiristoci na gaskiya. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya ƙin bin umurnan da muke samu daga ƙungiyar Allah, kuma mu soma yin gunaguni game da duk abin da ba ma so. Ko kuma wataƙila mu ƙi yarda sosai da gargaɗin Nassi game da nishaɗi da yin amfani da Intane da kuma zuwa makarantun gaba da sakandare.

13. Me ya sa muke bukata mu bincika kanmu da kyau?

13 Idan ba ma so mu bi halayen mutanen wannan zamanin, muna bukatar mu bincika kanmu da kyau. Muna bukatar mu bincika halayenmu yadda muke ji da maƙasudanmu da kuma mizananmu. Wasu za su iya cewa muna yin abu mai kyau, domin ba sa iya ganin abin da ke cikin zuciyarmu. Amma, mu kaɗai ne muka san ko mun bar abubuwan da muke koya daga Littafi Mai Tsarki su canja mu da kuma bari su ci gaba da yin hakan.—Karanta Yaƙub 1:23-25.

YADDA AKE YIN CANJE-CANJEN

14. Mene ne zai taimaka mana mu yi canje-canjen da muke bukata?

14 Idan muna son mu yi canje-canje, muna bukatar mu canja abin da ke cikin zuciyarmu, wato ainihin halinmu. Me zai taimaka mana mu yi irin waɗannan canje-canjen? Sa’ad da muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki, mun koya game da irin mutanen da Jehobah yake so mu zama. Yadda muke bin abin da muka karanta a Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu san irin abubuwan da ke cikin zuciyarmu. Hakan zai taimaka mana mu san canje-canjen da muke bukata mu yi don mu iya yin “nufin nan na Allah mai-kyau.”—Rom. 12:2; Ibran. 4:12.

15. Wane irin canje-canje ne muke yi sa’ad da Jehobah ya gina mu?

15 Karanta Ishaya 64:8. Kwatancin da annabi Ishaya ya yi ya koya mana wani darasi mai muhimmanci. Muna kama da yumɓu kuma Jehobah ne maginin tukwane. Sa’ad da yake gina mu, ba ya canja siffarmu, maimakon hakan, yana canja abin da ke ciki zuciyarmu. Idan muka ƙyale ya gina mu, wato ya taimaka mana mu canja yadda muke ji da kuma yin tunani, hakan zai sa mu guje wa tasirin wannan duniyar. Ta yaya Jehobah yake gina mu?

16, 17. (a) Ka kwatanta abin da maginin tukwane yake yi da yumɓu don ya gina tukunya mai kyau. (b) Ta yaya Kalmar Allah take taimaka mana mu zama da daraja a gaban Jehobah?

16 Idan mai yin tukwane yana so ya yi tukunya mai kyau, yana bukata ya yi amfani da yumɓu mai kyau sosai. Amma akwai abubuwa guda biyu da yake bukata ya yi tukuna. Na ɗaya, yana bukata ya cire duk wani gudaji-gudaji da ke cikin yumɓun. Na biyu kuma, yana bukata ya zuba masa ruwa daidai-wa-daida kuma ya kwaɓa shi yadda ko da an yi tukunya da shi ba zai fashe ba.

17 Maginin tukwane yana amfani da ruwa ta wajen cire gudaji-gudaji a cikin yumɓun da kuma sa shi ya yi laushi. Bayan hakan zai iya yin kowace irin tukunyar da yake so ya yi, har ma da tukwane masu wuya. Hakazalika, Kalmar Allah za ta iya canja mu. Za ta taimaka mana mu yi biris da irin tunanin da muke yi sa’ad da ba mu san Allah ba kuma mu zama masu daraja kamar tukunya mai kyau a gaban Allah. (Afis. 5:26) An tunatar da mu sau da sau cewa mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana da kuma halartar taro a kai a kai. Me ya sa aka ƙarfafa mu mu yi waɗannan abubuwan? Domin ta yin hakan, muna ƙyale Jehobah ya gina mu.—Zab. 1:2; A. M. 17:11; Ibran. 10:24, 25.

18. (a) Me ya sa muke bukatar yin bimbini idan muna so Kalmar Allah ta canja mu? (b) Waɗanne tambayoyi ne za su iya taimaka mana mu yi hakan?

18 Idan muna so Kalmar Allah ta canja mu, ba karanta Littafi Mai Tsarki da kuma sanin abin da ke ciki ne kaɗai ake bukata ba. Mutane da yawa suna karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuma sun san abubuwa da dama da ya ce. Wataƙila ka taɓa haɗuwa da irin waɗannan mutanen sa’ad da kake wa’azi. Wasu ma suna iya maimaita wasu ayoyi da ka. Amma, hakan ba ya canja tunaninsu da kuma halayensu. Me ya sa? Idan mutum yana son Kalmar Allah ta canja shi, wajibi ne ya bari ta ratsa zuciyarsa. Muna bukata mu yi bimbini a kan abin da muke koya daga Littafi Mai Tsarki. Zai dace mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Shin na tabbata cewa wannan ya fi koyarwar addini? Shin na ga tabbaci a rayuwata cewa wannan gaskiya ne? Shin ina amfani da abin da na koya maimakon zaton cewa ya kamata in koyawa wasu kawai? Shin na gaskata cewa abin da nake koya daga Jehobah ya shafe ni?’ Idan muka yi bimbini a kan irin waɗannan tambayoyin, za mu kusaci Jehobah. Sa’ad da koyarwarsa suka ratsa zuciyarmu, za su motsa mu mu yi canje-canjen da suka dace.—Mis. 4:23; Luk 6:45.

19, 20. Ta yaya za mu amfana idan muka bi shawarar da ke Littafi Mai Tsarki?

19 Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kansa a kai a kai, hakan zai taimaka mana mu ci gaba da yin abin da Bulus ya ce: ‘Ku tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa, ku yafa kuma sabon mutum, wanda ake sabunta shi zuwa ilimi.’ (Kol. 3:9, 10) Idan muka fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai kuma muka yi amfani da abin da muka koya, hakan zai motsa mu mu yafa sabon halaye na Kirista waɗanda za su iya kāre mu daga tarkunan Shaiɗan.

20 Manzo Bitrus ya ce: “Kamar ’ya’yan biyayya, ba za ku daidaita kanku bisa sha’awoyinku na dā,” amma “ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi.” (1 Bit. 1:14, 15) A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Jehobah zai albarkace mu idan muka ƙoƙarta don mu yi canje-canje a tunaninmu da kuma halayenmu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba