Ka Bauta Wa Jehobah
“Cikin ƙwazo kada ku yi ragonci; . . . kuna bauta wa [Jehobah].”—ROM. 12:11.
1. Mene ne ra’ayin yawancin mutane game da bayi kuma yaya wannan ra’ayin ya yi dabam da abin da ke Romawa 12:11?
YAWANCIN mutane suna zato cewa bawa mutumi ne da ubangijinsa yake gaya masa duk abin da zai yi kuma yana shan wahala sosai har ma a wulaƙanta shi. Amma hurarriyar Kalmar Allah ta ce bawa zai iya zaɓa ya yi wa ƙaunataccen Ubangijinsa bauta. Hakika, sa’ad da manzo Bulus ya aririci Kiristoci su riƙa “bauta wa Ubangiji,” yana ƙarfafa su ne su bauta wa Allah don suna ƙaunarsa. (Rom. 12:11) Mene ne irin wannan bautar ya ƙunsa? Ta yaya za mu iya tsare kanmu daga zama bayin Shaiɗan? Kuma, wace lada ce za mu samu idan mun zama bayin Jehobah kuma mun bauta masa da aminci?
“INA ƘAUNAR UBANGIJINA”
2. (a) Mene ne zai iya sa bawa Ba’isra’ile ya ci gaba da bauta wa ubangijinsa? (b) Mene ne huda kunnen bawa yake nunawa?
2 A cikin Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, mun koyi irin bautar da Jehobah yake so mu yi. Bawa Ba’ibrane yana samun ’yanci sa’ad da ya bauta wa ubangijinsa shekara bakwai. (Fit. 21:2) Amma, idan bawan yana ƙaunar ubangijinsa sosai kuma yana so ya ci gaba da bauta masa, Jehobah ya yi musu wani babban tanadi. Ubangijinsa zai kawo shi bakin ƙofa ko kuma madogaran ƙofa kuma ya huda kunnensa da basilla. (Fit. 21:5, 6) Me ya sa ake yin hakan? Hakan ya nuna cewa bawan yana so ya ci gaba da yi wa ubangijinsa bauta da kuma biyayya. Hakazalika, sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun nuna cewa muna so mu yi masa biyayya domin muna ƙaunarsa.
3. Me ya sa muke keɓe kanmu ga Allah?
3 Kafin a yi mana baftisma, mun riga mun yanke shawarar bauta wa Jehobah ko kuma zama bayinsa. Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun yi alkawari cewa za mu yi masa biyayya kuma mu yi nufinsa. Babu wanda ya tilasta mana mu yi hakan. Matasa ma da suke yin baftisma, suna yin hakan da son ransu ba don su faranta ran iyayensu ba. Ƙaunar da Kirista yake wa Ubangijinmu na sama, Jehobah ne zai sa ya keɓe kansa gare shi. Manzo Yohanna ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yoh. 5:3.
KO DA MUN SAMI ’YANCI, MU BAYI NE
4. Mene ne muke bukata mu yi idan muna so mu zama “bayin adalci”?
4 Muna godiya sosai ga Jehobah domin ya yi mana tanadin abubuwan da muke bukata don mu zama bayinsa! Imaninmu ga hadayar fansa na Kristi ya taimaka mana mu sami ’yanci daga zunubi. Ko da yake mu ajizai ne, mun zaɓa mu yi wa Jehobah da kuma Yesu biyayya. Bulus ya bayyana hakan dalla-dalla a wasiƙarsa cewa: “Ku maida kanku matattu ne ga zunubi, amma rayayyu ga Allah cikin Kristi Yesu.” Sai ya ba da gargaɗi cewa: “Ba ku sani ba, shi wanda ku ke miƙa kanku bayi gareshi garin biyayya, nasa bayi ku ke wanda ku ke biyayya da shi; ko na zunubi zuwa mutuwa, ko kuwa na biyayya zuwa adalci? Amma godiya ga Allah, ko da shi ke ku bayi ne na zunubi a dā, da zuciya ɗaya kuka zama masu-biyayya ga wannan irin koyarwa inda aka kai ku; da aka ’yantar da ku daga zunubi kuma, kuka zama bayin adalci.” (Rom. 6:11, 16-18) Ka lura cewa manzon ya ce mu zama masu-biyayya “da zuciya ɗaya.” Babu shakka, keɓe kanmu ga Jehobah ya sa mun zama “bayin adalci.”
5. Wace kokawa ce dukanmu muke yi, kuma me ya sa?
5 A matsayin bayin Allah, muna da wasu abubuwa biyu da ya wajaba mu shawo kansu. Na ɗaya, shi ne ajizancinmu. Manzo Bulus ya fuskanci wannan matsalar. Ya ce: “Gama ina murna da shari’ar Allah bisa ga mutum na ciki: amma ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwana.” (Rom. 7:22, 23) Saboda haka, a kullum muna yin kokawa da sha’awoyi jikinmu, wato sha’awoyin da ke sa mu yi abin da Allah ya haramta. Manzo Bitrus ya ce: “Kamar ’yantattu, ba kuwa za ku mori ’yancinku misalin mayafin ƙeta ba, amma kamar bayin Allah ne.”—1 Bit. 2:16.
6, 7. Ta yaya Shaiɗan yake sa mu ga kamar duniyarsa tana da kyau?
6 Abu na biyu da ya wajaba mu shawo kansa, shi ne kokawa da wannan duniyar da aljanu suke tasiri a kansa. Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar, kuma yana amfani da kowane makami don ya sa mu daina kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma Yesu. Yana so ya yi tasiri a kanmu don mu zama bayinsa. (Karanta Afisawa 6:11, 12.) Hanya ɗaya da Shaiɗan yake yin hakan, ita ce ta wajen sa mu ga kamar akwai abubuwan jin daɗi da kuma shaƙatawa a duniyarsa. Manzo Yohanna ya gargaɗe mu: “Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.”—1 Yoh. 2:15, 16.
7 A duniya baki ɗaya, mutane suna so su sami kayan duniya sosai. Shaiɗan yana sa su gaskata cewa samun kuɗi ruwa a jallo ne zai sa su kasance da farin ciki. A yau akwai manyan shaguna a ko’ina. Tallace-tallace da yawa suna ƙarfafa salon rayuwar da ke nuna cewa wadata da kuma nishaɗi ne suka fi muhimmanci. Kamfanoni da ke tsara tafiye-tafiye suna ƙarfafa mutane su yi tafiya zuwa wasu wurare masu ban sha’awa tare da mutanen duniya. Hakika, mutane da ke kewaye da mu suna matsa mana mu canja salon rayuwarmu daidai da na wannan duniyar.
8, 9. Wane haɗari ne muke fuskanta, kuma me ya sa?
8 A ƙarni na farko, Bitrus ya gargaɗi wasu Kiristoci da suka soma kasancewa da ra’ayin duniya. Ya ce: “Suna aza abin nishatsi ne a yi zari da rana, aibobi ne su, tabbai, suna nishatsi cikin bukukuwansu na ƙauna sa’anda suna biki tare da ku; Gama, lokacin da suke furtar da manyan rubobi, bisa ga lalata, cikin sha’awoyin jiki suna jarabci mutane waɗanda suna kan tsira daga hannun mazauna ciki saɓo; suna alkawarta musu ’yanci, su da kansu fa a cikin bautar ruɓa su ke; gama shi wanda ya ci nasara bisa mutum, shi ke saka shi cikin bauta kuma.”—2 Bit. 2:13, 18, 19.
9 Gamsar da “sha’awoyin jiki” ba ya ’yantar da mutum, maimakon haka, yakan sa ya zama bawan ubangijin wannan duniyar, wato Shaiɗan Iblis. (1 Yoh. 5:19) Zama bawan abubuwan duniya babban haɗari ne. Kuma idan muka ƙyale hakan ya faru, bari zai yi wuya sosai.
AIKI MAI ƘAYATARWA
10, 11. Su waye ne Shaiɗan ya fi kai wa hari, kuma ta yaya makarantun gaba da sakandare suke shafan matasa Kirista?
10 Shaiɗan yana kai wa marasa wayo hari, kamar yadda ya yi a gonar Adnin. Kuma ya fi mai da hankalinsa ga matasa. Shaiɗan yana bakin ciki sa’ad da matashi ko kuma wani ya yanke shawarar bauta wa Jehobah. Kuma yana so dukan waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah su kasa cika alkawarin da suka yi na bauta wa Allah da aminci.
11 Bari mu sake yin la’akari da misalin bawan da ya yarda a huda kunnensa. Babu shakka, wannan bawan ya ji zafi na ɗan lokaci yayin da ake huda kunnensa, amma hakan ya bar tabo da ya nuna cewa zai yi bauta na dindindin. Zai kasance da wuya matasa su yi zaɓin da ya bambanta da na tsararsu. Alal misali, Shaiɗan yana ƙarfafa wannan ra’ayin cewa idan kana so ka yi rayuwa mai ma’ana, kana bukatar ka samu aiki mai kyau. Amma, za mu yi rayuwa mai ma’ana, idan muka sa Jehobah farko a rayuwarmu. Yesu ya ce: “Masu-albarka ne waɗanda suke yunwata suna ƙishirta zuwa adalci.” (Mat. 5:6) Kiristoci sun keɓe rayuwarsu don yin nufin Allah, ba na Shaiɗan ba. Suna karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yi bimbini a kan sa dare da rana. (Karanta Zabura 1:1-3.) Amma, makarantun gaba da sakandare ba sa ba bayin Allah damar yin bimbini a kan Kalmarsa da kuma bauta masa.
12. Wane zaɓi ne matasa suke da shi a yau?
12 Idan Kirista yana wa wani aiki, zai iya shan wuya sosai. A wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta ga Korintiyawa, ya ce: “Kana bawa aka yi kiranka? kada wannan ya dame ka: amma idan kana da zarafi ka sami kanka, gwamma ka more shi.” (1 Kor. 7:21) Hakika, ’yanci daga bauta aka fi so. A ƙasashe da yawa a yau, doka ta ƙayyade tsawon shekarun da ya wajaba matasa su je makaranta. Bayan haka, ɗaliban za su iya zaɓa ko za su ci gaba da zuwa makaranta ko a’a. Zai yi wuya Kirista ya sami ’yancin bauta wa Jehobah na cikakken lokaci, idan ya zaɓi zuwa makarantar gaba da sakandare don ya iya samun aiki mai kyau.—Karanta 1 Korintiyawa 7:23.
ILIMIN GABA DA SAKANDARE KO ILIMI MAFI GIRMA?
13. Wane irin ilimi ne zai amfane bayin Jehobah?
13 Bulus ya gargaɗi Kiristocin da ke Kolosi, ya ce: “Ku yi hankali kada kowa ya cuce ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga ta’adar mutane, bisa ga rukunai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.” (Kol. 2:8) Malamai da yawa suna koyarwar da “ta’adar mutane, bisa ga rukunai na duniya.” Makarantun gaba da sakandare ma suna koyar da irin waɗannan abubuwan, kuma ba sa koya wa ɗalibai aikin hannu da zai taimake su a rayuwa, don haka ba sa iya yin rayuwa mai ma’ana. Akasin haka, mutanen Jehobah sun zaɓi ilimin da zai iya taimaka musu su zama da aikin hannun da zai sa su yi rayuwa mai sauƙi don su iya bauta wa Allah. Sun ɗauki shawarar da Bulus ya ba Timotawus da muhimmanci. Ya ce: “Amma ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma: amma da ya ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (1 Tim. 6:6, 8) Maimakon biɗan digiri don su yi suna, Kiristoci na gaskiya suna aiki tuƙuru don su samu “wasiƙun yabo” ta wajen fita wa’azi a kai a kai.—Karanta 2 Korintiyawa 3:1-3, Littafi Mai Tsarki.
14. Kamar yadda littafin Filibiyawa 3:8 ya nuna, ta yaya Bulus ya ɗauki gatan bauta wa Allah da kuma Yesu?
14 Bari mu yi la’akari da misalin manzo Bulus. Wani malami mai suna Gamaliel da ke koyar da Dokar Yahudawa ne ya koyar da shi. Za a iya kwatanta koyarwar da aka yi wa Bulus da wanda ake yi a makarantar gaba da sakandare a yau. Yaya Bulus ya ɗauki koyarwar sa’ad da ya gwada ta da gatan zama bawan Allah da kuma Kristi? Ya ce: “Ina lissafta dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu Ubangijina.” Ya kuma daɗa cewa: “Na sha hasarar dukan abu sabili da shi, kamar kayan banza kuwa na ke maishe su, domin in ribato Kristi.” (Filib. 3:8) Irin wannan ra’ayin zai iya taimaka wa Kiristoci matasa da kuma iyayensu su yanke shawara mai kyau a batun makaranta. (Ka duba hotunan.)
KA AMFANA DAGA ILIMI MAFI GIRMA
15, 16. Waɗanne koyarwa ne ƙungiyar Jehobah take tanadarwa, kuma mene ne maƙasudansu?
15 Yaya yanayin makarantun gaba da sakandare suke? Lalata da shaye-shaye da ƙungiyoyin asiri da siyasa da tawaye da kuma koyarwar bayyanau gama gari ne a waɗannan makarantun. (Afis. 2:2) Akasin haka, ƙungiyar Jehobah tana tanadar da koyarwa mafi girma kuma a yanayi mai salama, wato cikin ikilisiya. Kowannenmu yana da damar amfana daga Makarantar Hidima ta Allah da ake yi kowane mako. Akwai wasu makarantu kuma don ’yan’uwa maza majagaba marasa aure da ake kira, Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure da kuma na ma’aurata majagaba da ake kira Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata. Waɗannan makarantun suna taimaka mana mu yi biyayya ga Jehobah, wato Ubangijinmu da ke sama.
16 Za mu iya samun gaskiya masu tamani a cikin Watch Tower Publications Index ko kuma the Watchtower Library da ke CD-ROM. Asalin maƙasudan waɗannan makarantun su ne don a bauta wa Jehobah. Ana kuma koya mana yadda za mu taimaka wa mutane su zama abokan Allah. (2 Kor. 5:20) Bayan haka, waɗanda muka koyar za su iya koyar da wasu ma.—2 Tim. 2:2.
ALBARKAR DA BAWAN ZAI SAMU
17. Wace albarka ce ake samu don zaɓan ilimi mafi girma?
17 A almarar Yesu game da talinti, an yaba wa bayi biyun masu aminci don aikinsu, kuma hakan ya faranta wa ubangijinsu rai, har ma ya ba su ƙarin ayyuka. (Karanta Matta 25:21, 23.) Zaɓan ilimi mafi girma yana kawo albarka da kuma farin ciki. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Micheal ya yi ƙoƙari sosai a makaranta. Sai malamansa suka shawarce shi cewa ya je makarantar gaba da sakandare. Amma sun sha mamaki sa’ad da ya gaya musu cewa bai zai je ba. Maimakon haka, ya koyi aikin hannu na ɗan lokaci don ya iya yin hidima a matsayin majagaba na kullum. Shin ya yi hasara ne? Ya ce: “Makarantar hidima da na je a matsayin majagaba da kuma gatan da nake da shi yanzu a matsayin dattijo a ikilisiya sun amfane ni sosai. Albarka da kuma gatan da na samu sun ninka kuɗin da wataƙila zan samu. Na yi farin ciki da ban zaɓi zuwa makarantar gaba da sakandare ba.”
18. Me ya sa muka zaɓi ilimi mafi girma?
18 Ilimi mafi girma yana koya mana yin nufin Allah kuma yana taimaka mana mu bauta masa. Yana sa mu kasance da begen “tsira daga bautar ɓacewa,” kuma daga baya mu samu “’yancin darajar ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:21) Mafi muhimmanci ma, ta hakan ne za mu nuna cewa muna ƙaunar Ubangijinmu, Jehobah.—Fit. 21:5.