KU KOYAR DA YARANKU
Yesu Kristi Jariri Ne ko Kuma Sarki Mai Iko?
A watan Disamba, mutane da yawa a dukan duniya suna ganin hotuna ko kuma siffofin Yesu a matsayin jariri. Ana nuna shi a cikin komin dabbobi, wato babban akwati da ake saka ciyawa a ciki don dabbobi su ci. Amma ya kamata mu riƙa yi wa Yesu kallon jariri ne har yanzu?—a Bari mu tattauna yadda ya kamata mu riƙa ɗaukansa. Za mu iya koyan hakan daga wani abin da ya faru da wasu makiyaya sa’ad da suke kiwo a wani fili kusa da Bai’talami da dare.
Makiyayan suna nan, sai kawai wani mala’ika ya fito. Ya gaya musu cewa: “Yau . . . an haifa maku Mai-ceto, shi ne Kristi Ubangiji.” Mala’ikan ya ce za su sami Yesu “a nannaɗe cikin tsummoki, yana kwance a cikin [komi].” Nan da nan, mala’iku da yawa suka fito suka soma “yabon Allah.”
Me za ka yi idan ka ji mala’iku suna yabon Allah?— Makiyayan sun yi farin ciki! Sai suka ce: “Bari mu tafi yanzu har Bai’talami, mu ga wannan al’amarin da ya faru.” A wajen suka ga “Maryamu da Yusufu, da jariri kuma yana kwance a cikin [komi].”
Ba da daɗewa ba, sauran mutane suka je Bai’talami inda Maryamu da Yusufu suke. Dukansu sun yi mamaki sa’ad da makiyayan suka gaya musu abin da ya faru. Kana farin cikin sanin waɗannan abubuwa masu ban mamaki?— Dukanmu masu ƙaunar Allah muna farin ciki. Yanzu, bari mu ga dalilin da ya sa mutanen suka yi farin ciki sosai sa’ad da aka haifi Yesu. Kafin mu san dalilin, muna bukatar sanin abin da ya faru kafin Maryamu ta yi aure.
Wata rana, wani mala’ika mai suna Jibra’ilu ya ziyarci Maryamu. Ya ce za ta haifi jariri wanda “za ya zama mai girma, za a ce da shi Ɗan Maɗaukaki.” Ya kuma daɗa da cewa: “Za shi yi mulki kuma . . . mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”
Maryamu ta so ta san yadda hakan zai faru, tun da yake ba ta taɓa kwana da namiji ba. Sai Jibra’ilu ya ce mata: “Ruhu mai tsarki za ya auko miki, ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantadda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai tsarki, Ɗan Allah.” Allah ya ɗauki Ɗansa kuma ya saka shi a cikin Maryamu don ya yi girma har ya zama jariri. Wannan abin mamaki ne sosai!
Ka taɓa ganin hotunan “shehunnai uku” tare da makiyaya sa’ad da suka ziyarci Yesu a lokacin da yake jariri?— Ana yawan ganin waɗannan hotuna a lokacin Kirsimati. Amma, hotunan ba daidai ba ne. Waɗannan “shehuna” masanan taurari ne da suke yin abin da Allah ba ya so. Bari mu ga abin da suka tarar sa’ad da suka iso wurin. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Suka shiga gidan, suka ga ɗan yaron tare da Maryamu uwatasa.’ Saboda haka, a lokacin Yesu ba jariri da ke kwance cikin komi ba ne, amma ɗan yaro ne da ke zama da Yusufu da Maryamu a cikin gida!
Ta yaya shehunan suka sami Yesu?— Wani “tauraro” ne ya bi da su wurin Sarki Hirudus a Urushalima kafin ya kai su Bai’talami. Littafi Mai Tsarki ya ce Hirudus ya so ya san inda Yesu yake don ya kashe shi. Ka yi tunani a kan wannan. Kana ganin wane ne ya sa wannan abin da ya yi kamar tauraro ya bi da waɗannan masanan taurari wurin Hiridus?— Ba Jehobah ba ne, amma maƙiyinsa Shaiɗan Iblis ne!
A yau, Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mutane su riƙa yi wa Yesu kallon jaririn da bai san kome ba. Amma mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu cewa: “Za shi yi mulki kuma . . . ; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” A yanzu, Yesu babban Sarki ne a sama, kuma ba da daɗewa ba zai halaka dukan maƙiyan Allah. Yadda ya kamata mu riƙa ɗaukan Yesu ke nan, kuma mu riƙa gaya ma wasu game da hakan.
Ka karanta a naka Littafi Mai Tsarki
Matta 2:7-12; 1 Bitrus 5:8
Ru’ya ta Yohanna 19:19-21; 1 Yohanna 2:17
a Idan kana karatun da yaro ne, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata don ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.