‘Wannan Za Ta Zama Abin Tunawa A Gareku’
“Wannan rana fa za ta zama abin tunawa a gareku, za ku riƙe ta idi ga Ubangiji.”—FIT. 12:14.
1, 2. Wane bikin cika shekara ne ya kamata ka so sani sosai kuma me ya sa?
MENE NE kake tunawa sa’ad da ka ji furucin nan, bikin cika shekara? Idan kana da aure, za ka iya cewa, “ranar da na yi aure.” Ga wasu kuma, zai iya zama rana mai muhimmanci sosai, kamar ranar da ƙasarsu ta sami ’yanci. Amma shin ka san da wani bikin cika shekara da aka kwashe fiye da shekaru 3,500 ana yin sa?
2 Ana kiran wannan bikin, Idin Ƙetarewa ko Faska. A ranar ce aka ’yantar da Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar. Me ya sa ya kamata wannan ranar ta kasance da muhimmanci sosai a gare ka? Domin ta shafi rayuwarka a wasu muhimman hanyoyi. Amma za ka iya cewa: ‘Yahudawa ne suke Idin Ƙetarewa, amma ni Kirista ne. Yaya wannan Idin ya shafe ni?’ Za a sami amsar a wannan furuci na gaba: ‘An yanke faskarmu [idin ƙetarewarmu], watau Kristi.’ (1 Kor. 5:7) Mene ne hakan yake nufi? Domin mu san amsar, muna bukatar mu ƙara sanin yadda Yahudawa suke yin Idin Ƙetarewa da kuma yadda yake da alaƙa da dokar da aka ba dukan Kiristoci.
ME YA SA AKE IDIN ƘETAREWA?
3, 4. Mene ne ya faru kafin a soma Idin Ƙetarewa?
3 Miliyoyin mutane a faɗin duniya da ba Yahudawa ba sun san da abin da ya faru kafin a yi Idin Ƙetarewa na farko. Wataƙila sun taɓa karanta labarin a littafin Fitowa a cikin Littafi Mai Tsarki ko sun ji labarin daga bakin wani ko kuma sun kalla a fim. Amma kai kuma fa, ka tuna abin da ya faru?
4 Bayan Isra’ilawa sun kwashi shekaru da yawa suna bauta a ƙasar Masar, sai Jehobah ya aiki Musa da Haruna su gaya wa Fir’auna ya ’yantar da mutanensa. Amma da yake Fir’auna mai fahariya ne, ya ƙi ya ƙyale su su tafi. A sakamako, Jehobah ya gana wa Masarawa azaba da annoba goma. Dukan ’ya’yan fari na Masarawa sun mutu sa’ad da Allah ya aiko da annoba ta ƙarshe. Bayan hakan, sai Fir’auna ya ƙyale Isra’ilawa su tafi.—Fit. 1:11; 3:9, 10; 5:1, 2; 11:1, 5.
5. Mene ne aka ce Isra’ilawa su yi kafin a ’yantar da su? (Ka duba hoton da ke shafi na 17.)
5 Amma kafin Isra’ilawa su fita daga ƙasar Masar, sun bi wasu takamammun umurnin da aka ba su. Wannan ya faru aƙalla a ranar 21 ko 22 na Maris, shekara ta 1513 kafin zamaninmu, wato a watan da daga baya, Ibraniyawa suke kiran Abib ko Nisan. Allah ya gaya musu cewa su soma shiri a ranar 10 ga Nisan domin abin da zai faru da faɗuwar ranar 14 ga Nisan. Yahudawa suna ƙirga ranakunsu daga faɗuwar rana zuwa faɗuwar rana. Saboda haka, ranar ta soma daga faɗuwar rana. Sa’ad da ranar ta kai, an gaya wa kowace iyali cewa ta yanka rago (ko akuya) kuma ta yayyafa jininsa a dogaran ƙofar gidansu. (Fit. 12:3-7, 22, 23) Iyalan za su ci gasashen rago da gurasa marar yisti tare da wasu ganyaye. Mala’ikan Allah zai ƙetare ƙasar kuma zai kashe ’ya’yan fari na Masarawa, amma ba zai kashe ’ya’yan fari na Isra’ilawa masu biyayya ba. Bayan haka, za a ’yantar da bayin Allah.—Fit. 12:8-13, 29-32.
6. Me ya sa Isra’ilawa za su bukaci su riƙa kiyaye Idin Ƙetarewa kowace shekara?
6 Abin da ya faru ke nan kuma Isra’ilawa suna bukatar su riƙa tunawa da wannan ranar da aka ’yantar da su daga ƙasar Masar. Allah ya gaya musu: “Wannan rana fa za ta zama abin tunawa a gareku, za ku riƙe ta idi ga Ubangiji: har dukan tsararakinku za ku riƙe ta idi, bisa ga farilla har abada.” Bayan Isra’ilawa sun yi Idin Ƙetarewa a ranar 14, za su yi wani biki da ake kira Idin Gurasa Marar-yisti har kwana bakwai. Za a iya kiran wannan idodi na kwanaki takwas, Idin Ƙetarewa. (Fit. 12:14-17; Luk 22:1; Yoh. 18:28; 19:14) Idin Ƙetarewa yana cikin idodin da Allah ya umurci Isra’ilawa cewa su kiyaye kowace shekara.—2 Laba. 8:13.
7. Wane sabon Idi ne Yesu ya ce almajiransa su riƙa kiyayewa?
7 Yesu da almajiransa Yahudawa ne kuma suna kiyaye Dokar da aka ba da ta hannun Musa. Saboda haka, suna kiyaye Idin Ƙetarewa. (Mat. 26:17-19) A Idin Ƙetarewa na ƙarshe da Yesu da almajiransa suka yi tare, ya gaya musu cewa za su riƙa yin wani sabon idi kowace shekara. Ana kiran wannan idin, Jibin Maraice na Ubangiji. Amma, a wace rana ce ya kamata su kiyaye wannan Idin?
A WACE RANA CE AKE JIBIN MARAICE NA UBANGIJI?
8. Wace tambaya ce za mu yi game da Idin Ƙetarewa da kuma Jibin Maraice na Ubangiji?
8 Bayan Yesu ya idar da Idin Ƙetarewa tare da manzanninsa, sai ya ba da umurni cewa su riƙa kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji. Saboda haka, a ranar da aka kiyaye Idin Ƙetarewa ce aka yi Jibin Maraice na Ubangiji. Amma wataƙila ka lura cewa Yahudawa ba sa kiyaye Idin Ƙetarewa a ranar da muke Tunawa da Mutuwar Yesu. Me ya sa? Umurnin da Allah ya ba Isra’ilawa sa’ad da suke gab da yin idi na farko ya ba da amsar tambayar. Allah ya gaya musu sa’ar da za su yanka ragon a ranar 14 ga Nisan, kuma a wannan sa’ar ce za a soma Idin.—Karanta Fitowa 12:5, 6.
9. Kamar yadda littafin Fitowa 12:6 ya nuna, a wane lokaci ne za a yanka ragon Idin Ƙetarewa? (Ka kuma duba akwatin nan “A Wane Lokaci Ke Nan?”)
9 Wani littafin Yahudawa da ake kira, Pentateuch and Haftorahs ya ambata littafin Fitowa 12:6 cewa ya kamata a yanka ragon “tsakanin yammar biyu.” Furucin da ke wasu juyin Littafi Mai Tsarki ke nan. Amma wasu juyi, har da juyin Tanakh na Yahudawa sun ce “da maraice.” Akwai wasu juyin Littafi Mai Tsarki da suka ce “da almuru” ko “da yamma,” ko kuma “da faɗuwar rana.” Saboda haka, ya kamata a yanka ragon da faɗuwar rana, sa’ad da gari bai yi duhu ba tukun, wato sa’ad da aka shiga ranar 14 ga Nisan.
10. A wace sa’a ce wasu suke zato cewa ake yanka ragon Idin, shin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ke nan?
10 Daga baya, Yahudawa sun yi tunani cewa zai ɗauki lokaci da yawa kafin a gama yanyanka ragunan da aka kawo haikalin. Saboda haka, sun ɗauka cewa “tsakanin yamma biyu” da aka ambata a littafin Fitowa 12:6 yana nufin ƙarshen ranar 14 ga Nisan, wato tsakanin lokacin da rana ta soma faɗuwa har lokacin da ya gama faɗuwa da yamma. Amma idan hakan gaskiya ce, a wane lokaci ne suka ci abincin Idin Ƙetarewan? Wani shahararren shehun malami a Yahudanci na dā, mai suna Jonathan Klawans ya ce: “Ana shigan sabon rana sa’ad da rana ta faɗi, saboda haka, ana yin hadayar a ranar 14, amma ana soma Idin da kuma cin abincin a ranar 15, ko da yake ba a bayyana hakan a littafin Fitowa ba.” Ya kuma ce: “Littattafan Yahudawa . . . ba su bayyana yadda ake yin Idin Ƙetarewa kafin a halaka Haikalin a shekara ta 70 a zamaninmu ba.”
11. (a) Mene ne Yesu ya fuskanta a ranar Idin Ƙetarewa ta 33 a zamaninmu? (b) Me ya sa ake kiran 15 ga Nisan na shekara ta 33 “babbar” Assabbaci? (Ka duba hasiya.)
11 A wace rana ce aka yi Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 a zamaninmu? Kwana ɗaya kafin a yi Idin, wato a ranar 13 ga Nisan, Yesu ya gaya wa Bitrus da Yohanna cewa: “Ku tafi, ku shirya mana faska, domin mu ci.” (Luk 22:7, 8) Bayan haka, a ranar 14 ga Nisan, wato a ranar Alhamis da faɗuwar rana, Yesu ya ci abincin Idin Ƙetarewan tare da almajiransa. Bayan Idin, sai ya ba su umurni game da Jibin Maraice na Ubangiji. (Luk 22:14, 15) Sai aka kama shi daddare kuma aka hukunta shi. An kafa Yesu a gungumen azaba kusan da rana na 14 ga Nisan kuma ya mutu da rana. (Yoh. 19:14) Saboda haka, Yesu wanda shi ne ɗan ragon idin ƙetarewarmu, ya ba da ransa a ranar Idin. (1 Kor. 5:7; 11:23; Mat. 26:2) An binne Yesu kafin ranar 15 ga Nisan.a—Lev. 23:5-7; Luk 23:54.
ME ZA KA IYA KOYA DAGA ABIN TUNI?
12, 13. A wace hanya ce yaran Isra’ilawa suke saka hannu a Idin Ƙetarewa?
12 A lokacin da Isra’ilawa suka kiyaye Idin Ƙetarewa na farko a ƙasar Masar, Allah ya umurce su cewa su yi wannan Idin kowace shekara “har abada.” Yara suna tambayar iyayensu a ranar Idin a kowace shekara dalilin da ya sa suke kiyaye shi. (Karanta Fitowa 12:24-27; K. Sha 6:20-23) Saboda haka, Idin Ƙetarewan zai zama abin tuni, da har yara za su iya koyan darussa.—Fit. 12:14.
13 Isra’ilawa sun koya wa yaransu muhimman darussa game da Idin Ƙetarewan daga shekara zuwa shekara. Darasi na ɗaya shi ne cewa Jehobah zai iya kāre bayinsa. Yaran sun koyi cewa Jehobah Allah ne mai rai, yana kula da kuma kāre su. Ya yi hakan sa’ad da ya buga Masarawa da annoba ta goma, amma ya kāre ’ya’yan fari na Isra’ila.
14. Wane darasi ne iyaye Kiristoci za su iya koya wa yaransu?
14 Ba a umurci iyaye Kiristoci su riƙa gaya wa yaransu labarin Idin Ƙetarewa a kowace shekara ba. Amma shin kuna koya musu cewa Allah ya kāre bayinsa a ranar Idin Ƙetarewa? Shin kuna koya musu cewa a yau ma Jehobah yana kāre bayinsa? (Zab. 27:11; Isha. 12:2) Shin kuna sa su ji daɗin wannan tattaunawar ko dai kuna yi musu dogon jawabi ne kawai? Wannan darasin zai taimaka wa iyalinka ta daɗa dogara ga Jehobah.
15, 16. Mene ne Idin Ƙetarewa da ’yancin da Isra’ilawa suka samu daga Masar zai iya koya mana game da Jehobah?
15 Wani darasi kuma da muka koya daga Idin Ƙetarewan shi ne cewa Jehobah yana ’yantar da bayinsa. Ka yi tunanin yadda Isra’ilawa suka ji sa’ad da Jehobah ya ’yantar da su daga ƙasar Masar. Ya kāre su da umudin girgije da kuma na wuta har suka isa Jar Teku. Sai suka ga yadda Jehobah ya raba tekun biyu. Sai suka ƙetare tekun kuma bayan sun gama, Jehobah ya sa ruwan ya dawo ya halaka rundunar Masarawa. Isra’ilawa suka yabi Jehobah don ya ’yantar da su kuma suka rera waƙa. Sun ce: “Zan rera waƙa ga Ubangiji, . . . Da doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku. Ubangiji shi ne ƙarfina da waƙata, ya kuma zama cetona.”—Fit. 13:14, 21, 22; 15:1, 2; Zab. 136:11-15.
16 Idan kana da yara, shin kana taimaka musu su san cewa Jehobah, Allah ne mai ƙarfi da zai ceci bayinsa? Sa’ad da kake yanke shawara ko tattauna da yaranka, shin suna ganin yadda kake dogara cewa Jehobah zai cece ka da kuma iyalinka? Wataƙila sa’ad da kuke ibadarku ta iyali, za ku iya tattauna yadda littafin Fitowa surori 12-15 da Ayyukan Manzanni 7:30-36 ko Daniyel 3:16-18, 26-28 suka nuna yadda Jehobah ya ’yantar da bayinsa. Ya kamata dukanmu, manya da ƙanana mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ’yantar da bayinsa a nan gaba kamar yadda ya yi da su a dā.—Karanta 1 Tasalonikawa 1:9, 10.
DOMIN MU TUNA
17, 18. Me ya sa jinin Yesu ya fi na ragon Idin Ƙetarewa daraja?
17 Kiristoci na gaskiya ba sa yin Idin Ƙetarewa. Me ya sa? Domin Idin yana cikin Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa kuma Kiristoci ba sa bin Dokar. (Rom. 10:4; Kol. 2:13-16) Maimakon haka, muna kiyaye mutuwar Ɗan Allah. Amma, za mu iya koyon darussa masu yawa daga Idin Ƙetarewa da aka soma a ƙasar Masar.
18 Jinin ragon da Isra’ilawa suka yayyafa a dogaran ƙofar gidansu ya ceci ’ya’yansu na fari. A yau, ba ma yin hadaya da jinin dabbobi ga Allah a ranar Idin Ƙetarewa ko a wasu lokatai dabam. Amma, akwai wani jini da aka yi hadaya da shi da ya fi muhimmanci. Kuma mutanen da jinin ya ceci za su iya rayuwa har abada. Manzo Bulus ya ce “jinin yayyafawa” na Yesu ne ya ba Kiristoci shafaffu zarafin yin rayuwar har abada a sama. Su ’ya’yan fari ne “waɗanda an rubuta sunayensu a sama.” (Ibran. 12:23, 24) Jinin Yesu ya kuma sa ya yiwu waɗansu tumaki su samu begen yin rayuwa har abada a duniya. Ya kamata dukanmu mu riƙa tuna wa kanmu wannan alkawarin. “Muna da fansarmu a cikinsa ta wurin jininsa, gafarar laifofinmu, gwargwadon wadatar alherinsa.”—Afis. 1:7.
19. Ta yaya yadda Yesu ya mutu zai iya ƙarfafa imaninmu ga annabcin Littafi Mai Tsarki?
19 Allah ya umurci Isra’ilawa kada su karya ƙasusuwan ragon da suka yi Idin Ƙetarewan da shi. (Fit. 12:46; Lit. Lis. 9:11, 12) Kashin “Ɗan rago na Allah” kuma fa, wanda ya yi hadaya da ransa? (Yoh. 1:29) An kafa shi a gungumen azaba a tsakanin ɓarayi biyu. Yahudawa sun ce Bilatus ya sa a karya ƙasusuwan Yesu da kuma na ɓarayin domin su mutu da sauri. Da hakan, za a iya cire gawansu daga kan gungumen kafin ranar 15 ga Nisan wadda “babbar” Asabbat ce. Sojoji sun karya ƙafafun ɓarayin biyu, “amma sa’ad da suka zo wurin Yesu, suka gani kuma ya rigaya ya mutu, ba su karye ƙafafunsa ba.” (Yoh. 19:31-34) Ba a karya ƙasusuwan Yesu kamar yadda ba a karya na ragon Idin Ƙetarewan ba. Saboda haka, ragon Idin yana wakiltar hadayar da Yesu zai miƙa a ranar 14 ga Nisan, shekara ta 33 a zamaninmu. (Ibran. 10:1) Wannan ya cika kalaman da ke Zabura 34:20 kuma ya kamata hakan ya sa mu daɗa dogara ga annabcin Littafi Mai Tsarki.
20. Wane bambanci ne ke tsakanin Idin Ƙetarewa da kuma Jibin Maraice na Ubangiji?
20 Amma, akwai bambanci tsakanin Idin Ƙetarewa da Jibin Maraice na Ubangiji. Alal misali, Isra’ilawa suna cin naman ragon da aka yanka a Idin, amma ba sa shan jininsa. Amma abin da Yesu ya ce almajiransa su yi ya yi dabam da wannan. Ya ce waɗanda za su yi sarauta a “mulkin Allah,” su ci gurasa kuma su sha inabin da suke wakiltar jikinsa da jininsa. Za mu tattauna batun Tuna da Mutuwar Yesu dalla-dalla a talifi na gaba.—Mar. 14:22-25.
21. Me ya sa ya kamata mu koya game da Idin Ƙetarewa?
21 Idin Ƙetarewa yana da muhimmanci ga bayin Allah kuma kowanenmu zai iya koyon darussa masu yawa daga Idin. Ko da yake Yahudawa ne suke kiyaye Idin Ƙetarewa a dā, amma ya kamata Kiristoci su san wannan labarin da kuma darasi da ke ciki, domin “kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne.—2 Tim. 3:16.
a Washegarin ranar Idin, wato a ranar 15 ga Nisan ne farkon ranar Idin Gurasa Marar-yisti kuma Assabbaci ne. Ranar 15 ga Nisan na shekara ta 33 ce farkon Assabbaci na mako-mako, wato ranar Asabar. An kira ranar “babbar” Asabbat domin an yi Assabbacin biyu a rana ɗaya a shekarar.—Yoh. 19:31, 42.