TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE
Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala?
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wata Mashaidiya mai suna Michelle ta ziyarci wata mata mai suna Sophia.
ALLAH YA DAMU DA WAHALAR DA MUKE SHA KUWA?
Michelle: Sannu Sophia. Na yi murnar sake haɗuwa da ke.
Sophia: Yawwa sannu.
Michelle: Wancan karon da na zo, mun tattauna game da yadda Allah yake ji a duk lokacin da ya ga muna shan wahala.a Kin ambata cewa kin daɗe kina yin tunani a kan wannan batun, musamman ma bayan mahaifiyarki ta ji rauni a hatsarin mota da ta yi. To yaya jikin mahaifiyarki yanzu?
Sophia: Jikin yakan tashi a wasu lokatai, amma, yau ta ɗan sami sauƙi.
Michelle: Na yi mata murna. Na san ba shi da sauƙi ki kasance da farin ciki a irin wannan yanayin.
Sophia: Gaskiyarki. Na ƙosa in ga ta warke.
Michelle: Ni ma haka. Ki tuna cewa a wancan karon, na tambaye ki ko kin san abin da ya sa Allah ya ƙyale mutane su ci gaba da shan wahala ko da yake yana da iko ya kawo ƙarshen hakan.
Sophia: E fa, na tuna.
Michelle: Kafin mu amsa wannan tambayar daga Littafi Mai Tsarki, bari mu ɗan yi bitar wasu abubuwa da muka koya a wancan karon.
Sophia: To.
Michelle: Mun koyi cewa wani amintaccen bawan Allah ma ya nemi ya san dalilin da ya sa Allah yake ƙyale mutane su sha wahala. Allah bai tsauta masa don wannan tambayar ba, kuma bai gaya masa cewa bangaskiyarsa ta kasa ba.
Sophia: Ai ranar ne lokaci na farko da na ji wannan bayanin.
Michelle: Mun kuma koyi cewa Jehobah Allah ya tsani ya ga muna shan wahala. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a lokacin da mutanensa suke cikin ƙunci, shi ma “ya ƙuntata.”b Sanin cewa Allah yana tausaya mana a duk lokacin da muke shan wahala yana ƙarfafa mu, ko ba haka ba?
Sophia: Haka ne.
Michelle: A ƙarshe, mun yarda cewa tun da yake Mahaliccinmu yana da iko sosai, lallai zai iya kawo ƙarshen wahala a duk lokacin da ya so.
Sophia: Inda na ɗan rikice ke nan. Me ya sa Allah yake barin waɗannan munanan abubuwa su faru tun da yake yana da iko ya hana su faruwa?
WANE NE YA FAƊI GASKIYA TSAKANINSU?
Michelle: Don mu sami amsar tambayarki, bari mu tattauna wani labari da ke littafin Farawa. Kin san labarin Adamu da Hawwa’u da kuma ’ya’yan itacen da aka hana su ci?
Sophia: E, an koya mana a coci sa’ad da nake ƙarama. Allah ya hana su cin ’ya’yan wani itace, amma sun yi taurin kai.
Michelle: Hakan gaskiya ne. Yanzu bari mu tattauna abubuwan da suka faru kafin Adamu da Hawwa’u su yi zunubi. Waɗannan abubuwan za su taimaka mana mu san dalilin da ya sa muke shan wahala. Don Allah ki karanta littafin Farawa sura 3, ayoyi na 1 zuwa 5.
Sophia: To. Wurin ya ce: “Amma maciji ya fi kowane dabban da Ubangiji Allah ya yi hila. Ya fa ce wa macen, Ashe, ko Allah ya ce, Ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce wa macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taɓa ba, domin kada ku mutu. Sai macijin ya ce ma macen, ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.”
Michelle: Na gode da karatun. Bari mu bayyana waɗannan ayoyin bi da bi. Na farko, ki lura cewa wani maciji ya yi magana da macen, wato Hawwa’u. Wani nassi kuma ya nuna cewa Shaiɗan Iblis ne ainihi ya yi magana da ita ta bakin macijin.c Shaiɗan ya yi mata tambaya game da dokar da Allah ya ba su a kan wani itace. Kin lura da abin da Allah ya ce zai sami Adamu da Hawwa’u idan suka ci ’ya’yan itacen?
Sophia: Ya ce za su mutu.
Michelle: Gaskiyarki. Bayan hakan Shaiɗan ya yi wa Allah wani zargi. Ya ce: “Ba lallai za ku mutu ba.” Shaiɗan ya kira Allah maƙaryaci!
Sophia: Ban taɓa sanin hakan ba.
Michelle: Zargin da Shaiɗan ya yi cewa Allah maƙaryaci ne, zargi ne da zai bukaci lokaci don a warware shi. Yanzu kin ga abin da ya sa Allah yake bukatar lokaci sosai don ya warware wannan batun?
Sophia: Hmm. Ban fahimce ki sosai ba.
Michelle: To barin in ba ki wani misali. A ce na zo wurinki wata rana kuma na gaya miki cewa na fi ki ƙarfi. Ta yaya za ki ƙaryata ni?
Sophia: Ai za mu yi gwaji.
Michelle: Ƙwarai kuwa. Mai yiwuwa mu nemi wani kaya mai nauyi kuma mu ga wadda za ta iya ɗagawa a cikinmu. Sanin wadda ta fi ƙarfi a tsakaninmu ba abu mai wuya ba ne.
Sophia: Gaskiyarki ne.
Michelle: Amma idan na yi da’awar cewa na fi ki gaskiya kuma fa? Sanin gaskiyar hakan zai ɗan yi wuya, ko ba haka ba?
Sophia: Haka ne.
Michelle: Sanin mai gaskiya ba batun da za a iya warwarewa nan da nan ba ne.
Sophia: Hakika.
Michelle: Yadda za a iya sanin ko wa ya fi gaskiya cikinmu shi ne ta wajen yin la’akari da ayyukanmu, kuma hakan zai ɗauki lokaci.
Sophia: Gaskiya ne kam.
Michelle: Ki sake yin la’akari da labarin da ke littafin Farawa. Shin Shaiɗan yana da’awa cewa ya fi Allah ƙarfi ne?
Sophia: A’a.
Michelle: Ai da ƙaryata shi ba zai zama wani abu a wurin Allah ba. Amma, Shaiɗan ya yi da’awa cewa ya fi Allah gaskiya. Wato yana gaya wa Hawwa’u cewa, ‘Ƙarya Allah yake miki, amma ni, gaskiya nake gaya miki.’
Sophia: Lallai kuwa.
Michelle: Da yake Allah mai hikima ne, ya san cewa warware wannan batun zai bukaci lokaci. A kwana a tashi, za a san wanda yake faɗin gaskiya da kuma wanda yake ƙarya.
BATU MAI MUHIMMANCI
Sophia: Amma bayan Hawwa’u ta rasu, ai hakan ya nuna cewa Allah ne yake da gaskiya, ko ba haka ba?
Michelle: E, to, haka ne. Amma akwai wani abu kuma da Shaiɗan ya ƙalubalanci Allah a kai. Ki sake duba aya ta 5. Kin lura da wani abu kuma da Shaiɗan ya gaya wa Hawwa’u?
Sophia: Ya ce idan ta ci ’ya’yan itacen, idanunta za su buɗe.
Michelle: Ya kuma ce za ta zama ‘kamar Allah, tana sane da nagarta da mugunta.’ Saboda haka, Shaiɗan yana da’awa cewa Allah yana hana ’yan Adam wani abu mai kyau.
Sophia: Oho!
Michelle: Wannan ba ƙaramin zargi ba ne.
Sophia: Me kike nufi?
Michelle: Ta wajen abin da ya faɗa, Shaiɗan ya yi da’awa cewa Hawwa’u da kuma dukan ’yan Adam za su fi jin daɗin rayuwa idan ba sa ƙarƙashin ja-gorancin Allah. Saboda haka, Jehobah ya san cewa hanya mafi kyau na warware wannan zargin ita ce ta wajen ba Shaiɗan dama ya nuna ko zargin da yake yi gaskiya ne. Saboda haka, Allah ya ba Shaiɗan lokaci ya yi mulkin wannan duniya. Abin da ya sa muke ganin wahala a ko’ina ke nan. Shaiɗan ne ainihi yake mulkin duniya, ba Allah ba.d Amma, akwai wani albishiri.
Sophia: Me ke nan?
Michelle: Littafi Mai Tsarki ya bayyana abubuwa biyu game da Allah. Na farko, Jehobah yana damuwa da mu a duk lokacin da ya ga muna shan wahala. Alal misali, ki yi la’akari da kalamin Sarki Dauda a littafin Zabura 31:7. Dauda ya sha wahala sosai, amma ki ji abin da ya faɗa sa’ad da yake addu’a. Don Allah ki karanta wannan ayar.
Sophia: Ayar ta ce: “Zan yi murna in yi farin ciki cikin jinƙanka: Gama ka ga ƙuncina; Ka san masifun raina.”
Michelle: Duk da cewa Dauda ya sha wahala, ya san cewa Allah yana ganin dukan abubuwan da ke faruwa da shi kuma hakan ya ƙarfafa shi. Shin sanin cewa Jehobah yana ganin kome, har da abubuwan da ke ci mana tuwo a ƙwarya da mutane ba za su iya sani ba yana ƙarfafa ki kuwa?
Sophia: E.
Michelle: Na biyu shi ne cewa Allah ba zai ƙyale mu mu ci gaba da shan wahala har abada ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Allah zai kawo ƙarshen muguwar sarautar Shaiɗan. Ƙari ga haka, zai kawar da dukan munanan abubuwa da suka faru, har da waɗanda suka faru da ke da kuma mahaifiyarki. Zan so in sake dawowa mako mai zuwa don in nuna miki abin da ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Allah zai kawar da dukan wahala ba da daɗewa ba.e
Sophia: Hakan zai yi kyau.
Ka taɓa tunanin wani abu da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai daga cikin Littafi Mai Tsarki? Za ka so ka ƙara sanin wasu daga cikin koyarwar Shaidun Jehobah ko kuma dalilin da ya sa suka yi imani da wasu abubuwa? Idan haka ne, ka nemi ƙarin bayani daga Shaidun Jehobah. Za su yi farin cikin tattauna waɗannan batutuwan da kai.
a Ka duba talifin nan “Tattaunawa Tsakanin Shaidun Jehobah da Mutane—Allah Ya Damu da Wahalar da Muke Sha Kuwa?” da ke fitowar Satumba–Oktoba 2013 na mujallar Hasumiyar Tsaro. Za ka iya samunta a dandalin www.pr418.com/ha.
b Ka karanta Ishaya 63:9.
c Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9.
d Ka karanta Yohanna 12:31; 1 Yohanna 5:19.
e Don ƙarin bayani, ka duba babi na 9 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.