Begen Waɗanda Suka Mutu Shi ne Tashin Matattu
Shin ka gaskata da alkawarin Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu?a Muna farin ciki sosai sa’ad da muka yi tunanin sake saduwa da ’yan’uwanmu ko kuma abokanmu da suka rasu. Amma, zai yiwu mu sake saduwa da su kuwa? Don mu samu amsar wannan tambayar, ya kamata mu yi la’akari da misalin manzannin Yesu Kristi.
Manzannin sun yi imani sosai da tashin matattu. Me ya sa? Aƙalla domin dalilai biyu. Na farko, sun kasance da wannan begen domin an ta da Yesu daga mutuwa. Waɗannan manzannin da kuma “’yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda” sun ga Yesu bayan tashiwarsa. (1 Korintiyawa 15:6; Littafi Mai Tsarki) Ƙari ga haka ma, mutane da yawa sun shaida kuma sun yarda cewa Yesu ya tashi daga mutuwa, kamar yadda marubutan Linjila huɗu suka nuna.—Matta 27:62–28:20; Markus 16:1-8; Luka 24:1-53; Yohanna 20:1–21:25.
Na biyu kuma, manzannin sun ga lokacin da Yesu ya ta da aƙalla mutane uku da suka rasu a garin Nayin da Kafarnahum da kuma Bait’anya. (Luka 7:11-17; 8:49-56; Yohanna 11:1-44) A ɗaya daga cikin talifofin da suka gabaci wannan, mun tattauna yadda Yesu ya ta da wani daga mutuwa a Bait’anya, kuma iyalin mutumin abokan Yesu ne. Bari mu ƙara bincika abin da ya faru.
“NI NE TASHIN MATATTU”
“Ɗan’uwanki zai tashi.” Abin da Yesu ya gaya wa Martha ke nan, wadda ɗan’uwanta Li’azaru ya rasu kwanaki huɗu kafin wannan lokacin. Da farko, Martha ba ta fahimci abin da Yesu yake nufi ba. Sai ta ce masa: ‘Na san zai tashi,’ amma a ganinta hakan zai faru a gaba ne. Ka yi tunanin irin mamakin da ta yi sa’ad da ta ji Yesu ya ce, “Ni ne tashin matattu, ni ne rai,” kuma ta ga ya ta da ɗan’uwanta!—Yohanna 11:23-25.
Ina Li’azaru yake har tsawon kwana huɗu bayan mutuwarsa? Li’azaru bai faɗi wani abu da ya nuna cewa yana rayuwa a wani wuri cikin waɗannan kwanaki huɗu ba. Li’azaru ba shi da kurwa da ta je sama. Sa’ad da Yesu ya ta da Li’azaru, bai dawo da shi duniya don ya hana shi jin daɗin zama tare da Allah a sama ba. To, ina ne Li’azaru ya je a waɗannan kwanaki huɗun? Gaskiyar ita ce, yana barci a kabari.—Mai-Wa’azi 9:5, 10.
Ka tuna cewa Yesu ya kamanta mutuwa da irin barcin da idan mutum ya yi ba zai iya tashiwa ba, sai a tashin matattu. A cikin labarin, Yesu ya ce: “Abokinmu Li’azaru yana barci; amma zan tafi, domin in tashe shi daga barci.” Sai almajiran suka ce masa: “Ubangiji, idan barci ya ɗauke shi, zai farka.” Amma, Yesu yana gaya musu ne cewa Li’azaru ya mutu, su kuma suka ɗauka cewa yana nufin Li’azaru yana barci ne don ya huta. Sai Yesu ya gaya musu dalla-dalla cewa: “Li’azaru ya mutu.” (Yohanna 11:11-14) Ta wajen ta da Li’azaru daga mutuwa, Yesu ya ba shi damar rayuwa da kuma sake saduwa da iyalinsa. Hakika, hakan babban alheri ne ga wannan iyalin!
Yadda Yesu ya ta da waɗanda suka mutu a lokacin da yake duniya, ya nuna abin da zai yi a nan gaba a matsayin Sarkin Mulkin Allah.b A lokacin da Yesu zai soma sarauta bisa duniya, zai ta da ’yan Adam da suke barci a cikin kabari. Abin da yake nufi ke nan sa’ad da ya ce, “Ni ne tashin matattu.” Yaya za ka ji idan ka sake ganin mutanenka da suka mutu? Yaya kuma kake ganin waɗanda aka tashe su daga mutuwa za su ji? Lallai za su yi farin ciki sosai!—Luka 8:56.
Yaya za ka ji idan ka sake ganin mutanenka da suka mutu?
KA KASANCE DA BANGASKIYA DON KA RAYU HAR ABADA
Yesu ya gaya wa Martha cewa: “Wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu: kuma dukan wanda yana da rai, yana kuwa ba da gaskiya gare ni, ba shi mutuwa ba har abada.” (Yohanna 11:25, 26) Dukan waɗanda Yesu zai tayar a lokacin sarautarsa ta shekara dubu za su rayu har abada idan suka kasance da bangaskiya a gare shi.
“Wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu.”—Yohanna 11:25
Bayan da Yesu ya yi wannan furucin game da tashin matattu, sai ya yi wa Martha wata tambaya da za ta sa ta yi tunani sosai. Ya ce mata: “Kin gaskata wannan?” Sai ta amsa cewa: “I, Ubangiji; na rigaya na ba da gaskiya kai ne Kristi, Ɗan Allah.” (Yohanna 11:26, 27) Kai kuma fa? Za ka so ka kasance da irin bangaskiyar da Martha take da shi game da tashin matattu? Mataki na farko da za ka ɗauka shi ne, ka yi ƙoƙari ka san nufin Allah ga ’yan Adam. (Yohanna 17:3; 1 Timotawus 2:4) Hakan zai taimaka maka ka kasance da bangaskiya. Me zai hana ka samun Shaidun Jehobah don su bayyana maka koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan wannan batun? Za su yi farin cikin tattauna begen tashin matattu da kai.
a Ka duba talifin nan “Mutuwa Ba Ƙarshe Ba Ce!” a shafi na 6 a wannan mujallar.
b Don ƙarin bayani a kan alkawarin Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu, ka karanta babi na 7 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.