Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Afirka ta Yamma
A LOKACIN da Pascal yake girma a wani gari a ƙasar Kwaddebuwa da ake talauci, ya yi ɗokin yin rayuwa mai ma’ana. Da yake bai ƙware a yin dambe ba, ya yi tunani, ‘Me zan yi don in zama zakaran wasanni har in kasance da arziki?’ Sa’ad da ya kai shekara ashirin da biyar, sai ya tsai da shawara cewa ƙasar Turai ne inda zai ji daɗin rayuwa. Zai zama baƙon haure a Turai da yake bai da takardun shigan ƙasar.
Sa’ad da Pascal yake ɗan shekara 27 a shekara ta 1998, sai ya soma tafiyarsa. Ya ƙetare zuwa ƙasar Ghana, sai ya shiga Togo, daga Togo ya shiga ƙasar Benin, daga Benin sai ya iso wani garin da ake ƙira Birni Nkonni a ƙasar Niger. To, yanzu ne za a soma ainihin tafiya mai haɗari. Don ya isa arewacin ƙasar, yana bukatar ya hau babban mota don ya ƙetare Hamadar Sahara. Kuma bayan ya iso Bahar Rum, sai ya shiga kwalekwalen da zai kai shi Turai. Ko da yake burinsa ke nan, amma wasu abubuwa biyu sun faru a ƙasar Niger da suka hana shi shigan ƙasar Turai.
Na farko, kuɗinsa ya ƙare. Na biyu kuma, ya haɗu da wani majagaba mai suna Noé da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Abin da ya koya ya ratsa zuciyarsa sosai har ya sake shawara. Ya daina yin tunani game da yin arziki kuma ya soma tunanin bauta wa Allah. Pascal ya yi baftisma a watan Disamba na shekara ta 1999. Don ya nuna godiyarsa ga Jehobah, ya soma hidimar majagaba a shekara ta 2001 a ƙasar Niger, wato a inda ya koyi gaskiya. Yaya yake ji game da hidimar da yake yi? Ya ce, “Ina jin daɗin rayuwa yanzu kuma ina yin amfani da lokacina da kyau!”
YIN RAYUWA MAI MA’ANA A AFIRKA
Mutane da yawa sun gano cewa, yin rayuwa mai ma’ana ya dangana ga kafa maƙasudai na bauta wa Allah, kamar yadda Pascal ya yi. Don su cim ma irin waɗannan maƙasudan, wasu sun bar ƙasar Turai kuma sun zo Afirka don su yi hidima a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Hakika, aƙalla Shaidu 65 masu shekaru tsakanin 17 da 70 sun bar ƙasar Turai kuma sun zo ƙasashen da ke Afirka ta Yamma kamar su Benin da Burkina Faso da Niger da kuma Togo don su yi hidima a inda ake bukatar masu shela.a Mene ne ya taimaka musu su yi irin wannan tafiyar kuma da wane sakamako?
Wata ’yar ƙasar Denmark mai suna Anne-Rakel ta ce, “Iyayena sun yi hidima a matsayin masu-wa’azi a ƙasashen waje a ƙasar Sinigal. A koyaushe suna hirar yadda hidimar take da daɗin gaske kuma na yi ɗokin yin irin wannan rayuwar.” A shekaru sha biyar da suka shige, sa’ad da Anne-Rakel take ’yar shekara ashirin da wani abu, sai ta tafi don ta yi hidima a inda ake bukatar masu shela a wata ikilisiya da ake yaren kurame na ƙasar Togo. Ta yaya matakin da ta ɗauka ya ƙarfafa wasu? Ta ce: “Daga baya, ƙanwata da kuma ƙanina sun bi ni zuwa ƙasar Togo.”
Wani ɗan’uwa ɗan shekara 70 ma’auraci mai suna Aurele da ke ƙasar Faransa ya ce: “Sa’ad da na yi murabus da aiki shekaru biyar da suka shige, na kasance da zaɓi biyu. Na farko, in ji daɗin rayuwata kuma in jira Aljanna ta zo ko kuma in faɗaɗa hidimata.” Wane zaɓi ne ya yi? Aurele ya faɗaɗa hidimarsa. Kusan shekaru uku da suka shige, shi da matarsa, Albert-Fayette, sun ƙaura zuwa ƙasar Benin. Aurele ya ce: “Ba da kai da muka yi don mu bauta wa Jehobah a nan shawara ce mafi kyau da muka yi.” Ya kuma daɗa yana murmushi, “A ƙarshe, mun ji daɗin hidimarmu domin gabar tekun tana da kyau kamar Aljanna.”
Wani ɗan’uwa mai suna Clodomir da matarsa Lysiane, sun ƙaura zuwa ƙasar Benin shekaru sha shida da suka shige. Da farko, ma’auratan sun yi kewar iyalinsu da abokansu da suka bari a ƙasar Faransa kuma sun ji tsoro cewa ba za su iya saba da wurin ba. Amma bai kamata su ji tsoro ba. Sun yi farin ciki sosai. Clodomir ya ce: “A cikin shekaru sha shida da muka yi muna hidima, mun sami gatan taimaka wa mutane aƙalla ɗaya kowace shekara su soma bauta wa Jehobah.”
Wasu ma’aurata ’yan ƙasar Faransa masu suna Sébastien da Johanna sun ƙaura zuwa ƙasar Benin a shekara ta 2010. Sébastien ya ce, “Akwai ayyuka da yawa a ikilisiyar. Yin hidima a nan ya sa muna saurin koyo!” Wane sakamako ne suka samu a hidimarsu? Johanna ta ce: “Mutane suna marmarin koyo game da Jehobah. Ko ba ma wa’azi, sai mutane su tsai da mu suna mana tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki ko kuma su ce mu ba su wasu littattafanmu.” Ta yaya ƙaurar da suka yi ta shafi aurensu? Sébastien ya ce: “Hidimar ta ƙarfafa aurenmu. Ina jin daɗin yin wa’azi tare da matata a koyaushe.”
Eric da matarsa Katy, sun yi hidimar majagaba a arewacin ƙasar Benin da babu mutane sosai. Sa’ad da suke ƙasar Faransa, shekaru goma da suka shige, sun soma karanta talifofin da suka yi magana a kan yin ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela da kuma ji ta baƙin masu hidima ta cikakken lokaci. Hakan ya sa sun ƙaura zuwa wata ƙasa a shekara ta 2005. Sun samu ƙaruwa sosai a wurin. Eric ya ce: “Shekaru biyu da suka shige, akwai masu shela 9 a rukuninmu da ke birnin Tanguiéta, amma yanzu mu 30 ne. A kowace ranar Lahadi, mutane tsakanin 50 da 80 ne suke halartan taro. Mun yi farin cikin shaida irin wannan gagarumar ƙaruwa!”
SANI DA KUMA SHAWO KAN ƘALUBALE
Waɗanne ƙalubale ne waɗannan suke hidima a inda ake da bukata suka fuskanta? Benjamin, ɗan shekara 33 ɗan’uwan Anne-Rakel ne. Sa’ad da yake ƙasar Denmark a shekara ta 2000, ya haɗu da wani mai wa’azi a ƙasar waje da ya taɓa hidima a ƙasar Togo. Benjamin ya ce: “Sa’ad da na gaya masa cewa ina so in yi hidimar majagaba, sai ya ce: ‘Ka san cewa za ka iya yin hidima a ƙasar Togo.’” Benjamin ya yi la’akari sosai a kan wannan batun. Ya ce: “A lokacin ban kai shekara 20 ba tukun, amma ’yan’uwana mata biyu sun riga sun soma hidima a ƙasar Togo. Hakan ya sa ya kasance mini da sauƙi in ƙaura zuwa wurin.” Bayan ya ƙaura zuwa ƙasar, ya fuskanci wani ƙalubale. Ya ce: “Ban san ko sannu da Faransanci ba. Watanni shida na farko da na yi a wurin bai kasance mini da sauƙi ba domin ba na iya tattaunawa da mutane.” Amma da sannu-sannu, sai ya soma jin yaren. Yanzu Benjamin yana hidima a Bethel da ke ƙasar Benin kuma yana saka hannu wajen rarraba littattafai da kuma taimakawa a sashen kwamfuta.
Eric da Katy da aka ambata ɗazun, sun taɓa hidima a wata ikilisiya da ke wani yare a ƙasar Faransa kafin su ƙaura zuwa Benin. Ta yaya Afirka ta Yamma ta yi dabam? Katy ta ce: “Bai kasance mana da sauƙi mu sami wurin kwana mai kyau ba. Mun yi wasu watanni muna zama a wani gida da babu wutar lantarki da ruwan famfo.” Eric ya ƙara da cewa: “Maƙwabtanmu suna yawan saka waƙa mai ƙara sosai har tsakar dare. Dole mu yi haƙuri da wasu irin wannan yanayin kuma mu yi ƙoƙari mu saba da hakan.” Dukansu sun amince cewa: “Farin cikin da muka yi a yin hidima a yankunan da ba a taɓa yin wa’azi ba ya shawo kan kowane ƙalubale da muka fuskanta.”
Michel da Marie-Agnès, ma’urata ne daga ƙasar Faransa da suka kusan shekaru sittin, sun ƙaura zuwa ƙasar Benin wajen shekara biyar da suka shige. Sun damu ƙwarai a lokacin. Michel ya ce wasu sun ɗauka cewa ƙaurar da suka yi yana da haɗari. Ya ƙara da cewa: “Za ka iya jin tsoro idan ba ka tabbata cewa Jehobah zai taimake ka ba. Saboda haka, sai muka ƙaura don mu bauta wa Jehobah kuma ya taimaka mana.”
YADDA ZA KA YI SHIRI
Waɗanda suka ƙware a yin hidima a inda ake bukata sun nanata muhimmancin yin shiri sosai ta wajen ɗaukan waɗannan matakan: Ka yi shiri tun da wuri. Ka yi ƙoƙari ka saba da sabon yanayin. Kada ka kashe kuɗi fiye da abin da ka shirya kashewa. Ka dogara ga Jehobah.—Luk 14:28-30.
Sébastien da aka ambata ɗazun ya ce: “Kafin mu ƙaura, ni da matata Johanna mun tara kuɗi cikin shekara biyu ta wurin rage kuɗaɗen da muke kashewa a nishaɗi kuma mun daina sayan wasu kayayyaki da ba su da muhimmanci.” Suna zuwa yin aiki a ƙasar Turai na wasu watanni a kowace shekara, sa’an nan su yi amfani da sauran watannin wajen yin hidimar majagaba a ƙasar Benin. Hakan ya taimaka musu su ci gaba da hidima a ƙasar waje.
Marie-Thérèse tana cikin wasu ’yan mata 20 da ba su yi aure ba da suka ƙaura don su yi hidima a inda ake bukatar masu shela a Afirka ta Yamma. Ita direbar bas ce a ƙasar Faransa, amma a shekara ta 2006 ta ɗauki hutun shekara guda don ta yi hidimar majagaba a ƙasar Niger. Ba da daɗewa ba, sai ta ankara cewa irin wannan rayuwar ce take so ta biɗa. Marie- Thérèse ta ce: “Sa’ad da na koma ƙasar Faransa, sai na gaya wa shugabana cewa ina so in ɗan yi gyara a tsarin aikina kuma ya amince da hakan. Yanzu, daga watan Mayu zuwa Agusta, ina yin aikin tuƙa bas a ƙasar Faransa, sai daga watan Satumba zuwa Afrilu, ina komawa ƙasar Niger don in yi hidimar majagaba.”
Waɗanda suka ‘fara biɗan mulkin’ suna da tabbaci cewa Jehobah zai ƙara musu “waɗannan abubuwa duka.” (Mat. 6:33) Ga wani misali: Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa marar aure ’yar Faransa da ta kusan shekara 30 mai suna Saphira, da take hidimar majagaba a ƙasar Benin. A shekara ta 2011, ta koma ƙasar Faransa don ta nemi kuɗin da za ta yi hidima ta shekara guda a Afirka kuma wannan shekara ta shida ke nan. Saphira ta ce: “Jumma’a ce rana ta ƙarshe da zan yi a wurin aiki, amma har ila ina bukatar kuɗin aikin kwana goma don in samu isashen kuɗin da zan kashe a shekara mai zuwa kuma sati biyu ne kawai ya rage mini a ƙasar Faransa. Na yi addu’a ga Jehobah kuma na bayyana masa yanayin da nake ciki. Jim kaɗan bayan hakan, sai aka ƙira ni aka ce ko zan iya sauya wata a aiki na sati biyu.” A ranar Litinin, sai Saphira ta je baƙin aiki don wadda za ta sauya ta koya mata aikin. Ta ce: “Na yi mamaki sosai sa’ad da na san cewa wadda zan sauya ’yar’uwa ce da ta nemi hutun sati biyu don ta halarci Makarantar Hidima ta Majagaba! Shugabanta ya ƙi ya ba ta hutun wai sai an sami wadda za ta sauya ta. Ta yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ta kamar yadda ni ma na yi.”
ABIN DA KE KAWO WADAR ZUCI SOSAI
Wasu ’yan’uwa sun yi hidima a Afirka ta Yamma na shekaru da yawa kuma har ila suna wurin. Wasu kuma sun yi hidima na wasu shekaru kaɗan kuma suka koma ƙasashensu. Amma har ila, waɗanda suka taɓa yin hidima a wuraren da ake bukatar masu shela suna amfana sosai. Sun koya cewa bauta wa Jehobah ce ke kawo wadar zuci sosai.
a Ofishin reshen Benin ne ke kula da ayyukan ƙasashe huɗun nan da ake yin Faransanci.