Me Yesu Ya Cim ma a Sarautar da Ya Yi na Shekara 100?
“Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, . . . Sarkin zamanai.”—R. YOH. 15:3.
1, 2. Mene ne Mulkin Allah zai cim ma, kuma wane tabbaci muke da shi cewa Mulkin zai zo?
SA’AD DA Yesu da almajiransa suke kan dutsen Kafarnahum a shekara ta 31 a zamaninmu, ya ce su riƙa yin addu’a suna cewa: ‘Bari Mulkinka ya zo.’ (Mat. 6:10) A yau, mutane da yawa suna shakkar zuwan wannan Mulkin. Amma, muna da tabbaci cewa Allah zai amsa addu’ar da muke yi don Mulkinsa ya zo.
2 Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don haɗa kan mala’iku da kuma mutane. Nufin Jehobah zai tabbata. (Isha. 55:10, 11) Hakika, Jehobah ya riga ya zama Sarki a zamaninmu! Abubuwa masu ban al’ajabi da suka faru a cikin shekaru dari da suka shige sun tabbatar da hakan. Allah yana yin ayyuka masu girma da kuma ban al’ajabi ga miliyoyin bayinsa masu aminci. (Zak. 14:9; R. Yoh. 15:3) Amma akwai bambanci tsakanin furucin nan Jehobah ya zama sarki da kuma zuwan Mulkin Allah da Yesu ya ce mu riƙa addu’a ya zo. A waɗanne hanyoyi ne suka bambanta kuma ta yaya suka shafe mu?
SARKIN DA JEHOBAH YA NAƊA YA SOMA AIKI
3. (a) Yaushe ne aka naɗa Yesu Sarki, kuma a ina aka naɗa shi? (b) Ta yaya za ka bayyana cewa an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914? (Ka duba hasiya.)
3 Shekaru 20 kafin shekara ta 1900, bayin Allah sun soma fahimtar annabcin da Daniyel ya rubuta shekaru 2,500 da suka shige. Annabcin ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai.” (Dan. 2:44) Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun daɗe suna nuna cewa shekara ta 1914 za ta zama shekara mai muhimmanci. Mutane da yawa a lokacin sun yi ɗokin ganin abin da zai faru a nan gaba. Kamar yadda wani marubuci ya ce: “Mutane da yawa a shekara ta 1914 sun kasance da kyakkyawan zato da kuma bege.” Amma da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya ɓarke a wannan shekarar ne annabcin Littafi Mai Tsarki ya cika. Ƙarancin abinci da girgizar ƙasa da cututtuka da kuma wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika sun tabbatar mana cewa Yesu Kristi ya soma sarauta a sama a matsayin Sarkin Mulkin Allah a shekara ta 1914.a Sa’ad da Jehobah ya naɗa Ɗansa a matsayin Sarki, ya tabbatar mana cewa har ila yana sarauta a wata hanya dabam.
4. Wane abu ne Yesu ya fara yi sa’ad da aka naɗa shi Sarki, kuma me ya yi bayan hakan?
4 Abu na farko da sabon Sarkin da Allah ya naɗa ya yi shi ne, ya yaƙi babban magabcin Ubansa, Shaiɗan. Yesu da mala’ikunsa sun jefo Shaiɗan da aljanunsa daga sama. Hakan ya sa aka yi murna sosai a sama, amma wahala ta daɗa tsanani a duniya. (Karanta Ruya ta Yohanna 12:7-9, 12.) Bayan hakan, sai Sarkin ya mai da hankali ga mutanensa a duniya don yi musu gyara da koyo kuma don shirya su su yi nufin Allah. Bari mu tattauna abin da za mu iya koya daga biyayyar da suka yi ga umurnan Yesu.
YESU YANA YI WA TALAKAWANSA MASU ADALCI GYARA
5. Wane tsarkakewa ne aka yi daga shekara ta 1914 zuwa farkon shekara ta 1919?
5 Bayan da Yesu ya jefo Shaiɗan da Aljanunsa daga sama, Jehobah ya sa Yesu ya mai da hankali ga mabiyansa a duniya don ya bincika da kuma gyara su. Annabi Malakai ya kwatanta hakan da tsarkakewa. (Mal. 3:1-3) Tarihi ya nuna cewa hakan ya faru tsakanin shekara ta 1914 da farkon shekara ta 1919.b Idan muna so mu kasance cikin iyalin Jehobah, wajibi ne mu kasance da tsabta ko kuma tsarki. (1 Bit. 1:15, 16) Dole ne kuma mu guji gurɓata kanmu da siyasa ko kuma koyarwar addinan ƙarya.
6. Ta yaya ake yi mana tanadin koyarwar Allah, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
6 Yesu ya yi amfani da ikonsa a matsayin Sarki wajen naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Wannan bawan zai riƙa koyar da dukan waɗanda ke cikin “garke ɗaya” da ke ƙarƙashin ja-gorancin Yesu game da Jehobah. (Mat. 24:45-47; Yoh. 10:16) Tun daga shekara ta 1919, bawa mai aminci mai hikima yana yin wannan babban aiki na koyar da ‘iyalin gidan’ Yesu game da Allah kuma hakan yana sa mu kasance da bangaskiya sosai. Ƙari ga haka, wannan bawan yana taimaka mana mu kuɗiri aniyar kasancewa da tsabta a ibada da hali da tunani da jiki da kuma a wasu fannonin rayuwa don mu kasance da tsabta a gaban Allah. Wannan tanadin yana koyar da kuma shirya mu mu yi ƙwazo a aiki mai muhimmanci da aka danƙa mana, wato aikin wa’azi. Shin kana ba da kanka a kai a kai don ka riƙa more wannan tanadin kuwa?
SARKIN YANA KOYA WA TALAKAWANSA YIN WA’AZI A FAƊIN DUNIYA
7. Wane aiki mai muhimmanci ne Yesu ya soma sa’ad da yake duniya, kuma har yaushe za a ci gaba da yin shi?
7 A lokacin da Yesu ya soma hidimarsa a duniya, ya ce: “Dole in kai Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk 4:43) A shekaru uku da rabi da Yesu ya yi a duniya, aikin wa’azi ne ya saka a gaba. Ya umurci almajiransa cewa: “A cikin tafiyarku kuma ku yi wa’azi, ku ce, Mulkin sama ya kusa.” (Mat. 10:7) Bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya gaya wa mabiyansa su kai bishara har “iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Ya yi musu alkawari cewa zai tallafa musu a wannan aiki mai muhimmanci har zuwa zamaninmu.—Mat. 28:19, 20.
8. Ta yaya Sarkin ya motsa mabiyansa a duniya su yi wa’azi?
8 Daga shekara ta 1919, wa’azin ‘bishara ta mulki’ ya ƙara kasancewa da ma’ana. (Mat. 24:14) Sarkin yana sarauta a sama, kuma ya tattara wani ƙaramin rukunin bayi masu tsabta. Wannan rukunin ya bi umurnin Yesu cewa su yi wa’azi a dukan duniya suna cewa Mulkin Allah yana sarauta a sama! (A. M. 10:42) Alal misali, kusan mutane 20,000 da suke tallafa wa Mulkin ne suka halarci babban taro na ƙasashe da aka yi a Cedar Point, a jihar Ohio, a ƙasar Amirka, a watan Satumba na shekara ta 1922. Waɗanda suka halarta sun ji daɗi sosai sa’ad da Ɗan’uwa Rutherford ya yi jawabi mai jigo “Mulkin” kuma ya ce: “Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma mulkinsa.” Washegari, mutane dubu biyu suka fita wa’azi, kuma wasunsu sun yi tafiyar mil 45 daga wurin da aka yi taron don su yi wa’azi. Wani ɗan’uwa ya ce: “Ba zan taɓa manta da umurnin da aka ba da cewa mu yi shelar Mulkin da kuma ƙwazon da waɗanda suka halarci taron suka nuna ba!” Haka wasu ma suka shaida.
9, 10. (a) Waɗanne makarantu ne muke da su don koyar da masu wa’azi? (b) Ta yaya ka amfana daga wannan koyarwar?
9 Masu shela guda 17,000 ne suke wa’azi a ƙasashe 58 a faɗin duniya a shekara ta 1922. Amma, suna bukata a horar da su. A ƙarni na farko, Sarkin ya ba almajiransa umurni dalla-dalla game da abin da za su faɗa da wurin da za su je da kuma yadda za su yi wa’azin. (Mat. 10:5-7; Luk 9:1-6; 10:1-11) A yau ma, Yesu ya tabbata cewa mabiyansa sun sami umurni da kuma kayan aiki da ake bukata don su yi wa’azi da kyau. (2 Tim. 3:17) Yesu yana amfani da ikilisiyar Kirista don ya koya wa mabiyansa yin wa’azi. Hanya ɗaya da yake hakan ita ce, ta Makarantar Hidima ta Allah da ake yi a ikilisiyoyi fiye da 111,000 a faɗin duniya. Wannan makarantar ta taimaka wa masu shela fiye da miliyan bakwai su yi wa’azi a hanyar da za ta ratsa zukatan “dukan mutane.”—Karanta 1 Korintiyawa 9:20-23.
10 Ƙari ga haka, akwai wasu makarantun da ake koyar da Littafi Mai Tsarki ma da suke taimaka wa wajen koyar da dattawa da majagaba da ’yan’uwa maza marasa aure da Kiristoci ma’aurata da Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe da matansu da masu kula masu ziyara da matansu da kuma masu-wa’azi a ƙasashen waje.c Wasu ɗaliban da suka halarci wani aji na Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata sun ce: “Irin koyo mai kyau da muka samu ya ƙarfafa ƙaunarmu ga Jehobah kuma ya taimaka mana mu iya koyar da wasu.”
11. Ta yaya masu shelar Mulki suka ci gaba da jimrewa duk da hamayya?
11 Shaiɗan yana ganin irin ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ake yi don a yi wa’azi da kuma koyar da mutane. Yana so ya hana wannan aikin samun ci gaba kuma yana iya ƙoƙarinsa don ya hana saƙon yaɗuwa kuma ya sa waɗanda suke wa’azin Mulkin su yi sanyin gwiwa. Amma ba zai yi nasara ba ko kaɗan. Jehobah ya sanya Ɗansa “nesa da dukan sarauta, da hukunci, da iko, da mulki.” (Afis. 1:20-22) A matsayin Sarki, Yesu ya yi amfani da ikonsa wajen kāre da kuma ja-gorar almajiransa don ya tabbata cewa an yi nufin Allah.d Ana ci gaba da yin wa’azi kuma ana koya wa miliyoyin mutane yadda za su bauta wa Jehobah. Muna da gata sosai wajen saka hannu a yin wannan aiki mai muhimmanci.
SARKIN YA SHIRYA TALAKAWANSA DON AYYUKA MASU YAWA
12. Waɗanne gyare-gyare ne aka yi tun daga shekara ta 1914 zuwa yau?
12 Tun lokacin da aka kafa Mulkin a shekara ta 1914, Sarkin ya shirya bayin Allah don su yi nufin Allah. (Karanta Ishaya 60:17.) A shekara ta 1919 ne aka soma naɗa mai gudanar da hidima a kowace ikilisiya don ya ja-goranci aikin wa’azi. An soma aikin wa’azi gida-gida na ranar Lahadi a shekara ta 1927. A shekara ta 1931 ne kuma bayin Allah suka soma amfani da sunan nan Shaidun Jehobah kuma hakan ya sa suka yi wa’azin Mulkin da ƙwazo. (Isha. 43:10-12) A shekara ta 1938 ne aka daina yin siyasa don zaɓar masu hidima a ikilisiya kuma aka soma naɗa su. A shekara ta 1972 ne aka soma naɗa rukunin dattawa maimakon bawan ikilisiya guda don su riƙa kula da ikilisiya. An ƙarfafa dukan mazaje da suka ƙware su ba da kansu don su taimaka wajen yin “kiwon garken Allah.” (1 Bit. 5:2) A shekara ta 1976 ne aka tsara Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah zuwa kwamitoci shida don su riƙa kula da aikin Mulkin a faɗin duniya. Tun daga lokacin, Yesu ya ci gaba da shirya mabiyansa a duniya don su riƙa yin abubuwa yadda Jehobah yake so.
13. Ta yaya abubuwan da Mulkin ya cim ma ya shafi rayuwarka?
13 Ka yi tunanin irin aikin da Almasihu Sarki ya yi a farkon sarautarsa na shekara 100. Ya tsabtace wasu rukunin mutane da suke wakiltar Jehobah. Ya ja-goranci wa’azin bishara da ake yi a ƙasashe 239 kuma ya koya wa miliyoyin mutane yadda za su bauta wa Jehobah. Ya sa mutane fiye da miliyan bakwai masu biyayya waɗanda suke ba da kansu da yardar rai don su yi nufin Ubansa su kasance da haɗin kai. (Zab. 110:3) Hakika, Jehobah ya yi amfani da Mulkin Almasihu don ya yi ayyuka masu girma da ban al’ajabi. Har ila, akwai abubuwa masu ban al’ajabi da zai yi a nan gaba.
ALBARKAR DA MULKIN ALMASIHU ZAI KAWO A NAN GABA
14. (a) Mene ne muke roƙan Allah ya yi sa’ad da muka yi addu’ar nan: ‘Bari Mulkinka ya zo’? (b) Mene ne jigon shekara ta 2014, kuma me ya sa wannan ya dace?
14 Ko da yake Jehobah ya naɗa Ɗansa, Yesu Kristi a matsayin Sarki, hakan ba shi ne amsar wannan addu’ar ‘bari Mulkinka ya zo’ ba. (Mat. 6:10) An annabta a cikin Littafi Mai Tsarki cewa Yesu zai ‘ci sarauta a tsakiyar maƙiyansa.’ (Zab. 110:2) Gwamnatocin ’yan Adam da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan har ila suna gāba da Mulkin. Sa’ad da muka yi addu’a Mulkin Allah ya zo, muna roƙon Allah ya sa Sarki Almasihu da kuma waɗanda za su yi sarauta da shi su kawar da sarautar ’yan Adam da waɗanda suke gāba da Mulkin daga duniya. Wannan matakin da zai ɗauka zai cika kalmomin da ke Daniyel 2:44 cewa Mulkin Allah “za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki.” Za ya halaka gwamnatoci da suke gāba da Mulkin Allah. (R. Yoh. 6:1, 2; 13:1-18; 19:11-21) Lokacin da hakan zai faru ya yi kusa sosai. Shi ya sa jigon shekara ta 2014 da aka ɗauko daga littafin Matta 6:10 ya dace sosai. Jigon shi ne: ‘Bari Mulkinka ya zo’! Yanzu shekaru 100 ke nan da Yesu ya soma sarauta a sama.
Jigon shekara ta 2014: ‘Bari Mulkinka ya zo.’—Matta 6:10
15, 16. (a) Waɗanne abubuwa masu ban al’ajabi ne za su faru a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu? (b) Wane abu ne Yesu zai yi a ƙarshen sarautarsa, kuma ta yaya hakan zai shafi nufin Allah?
15 Bayan Sarki Yesu ya halaka magabtan Allah, zai jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar-matuƙa na tsawon shekaru dubu. (R. Yoh. 20:1-3) Bayan an fitar da mugun, nan da nan Mulkin zai taimaka wa mutane su amfana daga fansar Yesu kuma ya kawar da abubuwan da zunubin Adamu ya jawo. Sarkin kuma zai ta da miliyoyin matattu kuma zai shirya a koyar da su game da Allah. (R. Yoh. 20:12, 13) Duniya baƙi ɗaya za ta zama aljanna kamar gonar Adnin kuma dukan mutane masu aminci za su zama kamiltattu.
16 Sarautar Kristi zai cim ma nufin Allah ga duniya a shekaru dubun. Bayan haka, Yesu zai mayar wa Ubansa Mulkin. (Karanta 1 Korintiyawa 15:24-28.) Ba za mu bukaci wani da zai riƙa roƙon Jehobah a madadinmu ba. Dukan ’ya’yan Allah da ke sama da kuma ƙasa za su kasance da haɗin kai ga Ubansu na sama a matsayin iyalin Allah.
17. Mene ne ka ƙudura anniyar yi don Mulkin?
17 Abubuwa masu ban al’ajabi da Mulkin ya cim ma a wannan shekara 100 ya tabbatar mana cewa Jehobah ne ke ja-gora kuma tabbas, nufinsa ga wannan duniyar zai cika. Bari mu ci gaba da kasancewa da aminci a gare shi kuma mu riƙa sanar da mutane game da Sarkin da kuma Mulkinsa. Muna da tabbaci cewa ba da daɗewa ba, Jehobah zai amsa wannan addu’ar da muke yi cewa: ‘Bari Mulkinka ya zo’!
a Ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, shafuffuka na 88-92.
b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka 22-23, sakin layi na 12.
c Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2012, shafuffuka na 13-17 mai jigo: “Makarantu na Ƙungiyar Jehobah, Tabbaci Ne Cewa Jehobah Yana Ƙaunarmu.”
d Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2012, shafuffuka na 16-17, don ka ga misalan nasarar da muka yi a kotuna a ƙasashe dabam-dabam.