AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Shin Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce da gaske?
Ya kamata a ce Kalmar Allah ta yi fice, ko ba haka ba? Haka Littafi Mai Tsarki yake. An buga biliyoyin Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa. Hikimar da ke cikinsa za ta iya gyara rayuwar mutane.—Karanta 1 Tasalonikawa 2:13; 2 Timotawus 3:16.
Mun san cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne domin dukan annabcin da ya yi game da gaba suna cika. Babu ɗan Adam da zai iya sa hakan ya faru. Alal misali, ka yi la’akari da littafin Ishaya. An samo wani kofinsa da aka kofa fiye da shekaru 100 kafin haihuwar Yesu, a cikin wani kogo da ke kusa da Tekun Gishiri. An ambata a cikin wannan kofin cewa a kwana a tashi, mutane ba za su zauna a Babila kuma ba. Wannan annabcin ya cika shekaru da yawa bayan hidimar Yesu a duniya.—Karanta Ishaya 13:19, 20; 2 Bitrus 1:20, 21.
Ta yaya aka rubuta Littafi Mai Tsarki?
Rubutun Littafi Mai Tsarki ya ɗauki shekaru fiye da 1,600. Mutane wajen 40 ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, sun yi bayyani a kan jigo guda kuma babu saɓani a abin da suka rubuta. Ta yaya hakan ya yiwu? Allah ne ya ja-gorance su.—Karanta 2 Sama’ila 23:2.
A wasu lokatai, Allah yakan yi wa marubutan Littafi Mai Tsarki magana ta bakin mala’iku ko ta wahayi ko kuma ta mafarki. Allah yakan gaya wa marubucin abin da yake so ya rubuta, sa’an nan ya ƙyale marubucin ya yi rubutun da nasa kalmomin.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 1:1; 21:3-5.