Jehobah Yana Mana Tanadi Kuma Yana Kāre Mu
“Tun da ya ƙallafa ƙaunarsa a gareni, domin wannan zan tsamar da shi, zan ɗaukaka shi, domin ya san sunana.”—ZAB. 91:14.
1, 2. Ta yaya yanayinmu ya bambanta a yadda muka girma da kuma yadda muka zama Shaidun Jehobah?
JEHOBAH ne ya kafa iyali. (Afis. 3:14, 15) Ko da mun fito daga iyali ɗaya ne, halayenmu da kuma yanayinmu sun bambanta. Wasunmu, iyayenmu ne suka yi rainon mu tun muna ƙanana. Wasu kuma sun yi rashin iyayensu sanadin cuta ko haɗari ko kuma wani bala’i. Har ila, wasu kuma ba su san ko wane ne iyayensu ba.
2 Dukanmu masu bauta wa Jehobah muna kamar waɗanda suke iyali ɗaya kuma yadda muka soma bauta wa Jehobah ya bambanta. Wataƙila iyayenka Shaidun Jehobah ne kuma sun yi rainon ka bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (K. Sha 6:6, 7) Ko kuma mai yiwuwa, kana ɗaya daga cikin dubban mutanen da Shaidun Jehobah suka yi musu wa’azi, kuma ta hakan ka zama Mashaidin Jehobah.—Rom. 10:13-15; 1 Tim. 2:3, 4.
3. Mene ne dukanmu muka gāda?
3 Ko da yake mun fito ne daga yanayi dabam-dabam, akwai abubuwa da dukanmu muka gāda. Dukanmu mun gāji zunubi, ajizanci da kuma mutuwa don Adamu ya yi wa Allah rashin biyayya. (Rom. 5:12) Duk da haka, a matsayin masu bauta ta gaskiya, za mu iya kiran Jehobah “Ubanmu.” A zamanin dā, mutanen Allah sun furta waɗannan kalaman da aka yi a Ishaya 64:8. Ayar ta ce: “Ya Ubangiji, kai ubanmu ne.” Ƙari ga haka, Yesu ya soma addu’ar misali da irin waɗannan kalaman, ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.”—Mat. 6:9.
4, 5. Waɗanne abubuwa ne za mu tattauna da za su sa mu daɗa ƙaunar Ubanmu, Jehobah?
4 Ubanmu na sama yana mana tanadi kuma yana kāre mu yayin da muke bauta masa da bangaskiya. Marubucin zabura ya ce Jehobah ya yi wannan kuɗirin: “Tun da [bawan Jehobah] ya ƙallafa ƙaunarsa a gareni, domin wannan zan tsamar da shi, zan ɗaukaka shi, domin ya san sunana.” (Zab. 91:14) Hakika, Jehobah Allahnmu mai ƙauna yana cetonmu kuma yana kāre mu don kada a halaka mu.
5 Bari mu tattauna yadda Ubanmu na sama, wato Jehobah yake (1) mana tanadi da (2) kāre mu da kuma yadda ya kasance (3) babban Amininmu don hakan zai sa mu daɗa ƙaunarsa. Yayin da muke tattauna waɗannan batutuwan, zai dace mu yi tunani sosai game da dangantakarmu da Allah da kuma yadda za mu girmama shi a matsayin Ubanmu. Zai kuma dace mu yi tunani a kan albarkar da Jehobah zai yi wa waɗanda suka kusace shi.—Yaƙ. 4:8.
JEHOBAH NE AINIHIN MAI MANA TANADI
6. A wace hanya ɗaya ce Jehobah ya zama mai ba da “kowace kyakkyawar baiwa”?
6 Almajiri Yaƙub ya ce: “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana saukowa daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙ. 1:17) Rai da muke mora ma baiwa ce daga Jehobah. (Zab. 36:9) Idan muka yi amfani da rayuwarmu don yin nufin Jehobah, za mu sami albarka sosai yanzu da kuma rai na har abada a sabuwar duniya. (Mis. 10:22; 2 Bit. 3:13) Amma ta yaya hakan zai yiwu, da yake rashin biyayya da Adamu ya yi ya jefa mu a cikin wani mugun hali?
7. Ta yaya Allah ya yi tanadi don mu kasance da dangantaka ta kud da kud da shi?
7 Hakika, Jehobah yana tanadar mana da abubuwa a hanyoyi da yawa. Alal misali, alherinsa ya sa shi ya ɗauki mataki don ya cece mu. Dukanmu muna zunubi kuma mun gāji ajizanci daga Adamu, wato ubanmu na duniya. (Rom. 3:23) Duk da haka, da yake Jehobah uba ne mai ƙauna, ya yi tanadi don mu kasance da dangantaka ta kud da kud da shi. Manzo Yohanna ya ce: “Inda aka bayyana ƙaunar Allah garemu ke nan, Allah ya aike Ɗansa haifaffensa kaɗai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai ƙauna, ba cewa mu ne muka yi ƙaunar Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma ya biya hakin zunubanmu.”—1 Yoh. 4:9, 10.
8, 9. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi ne Ainihin Mai Mana Tanadi a zamanin Ibrahim da Ishaƙu? (Ka duba hoton da ke shafi na 16.)
8 A kusan shekara ta 1893 kafin zamaninmu, akwai wani abin da ya faru da Ibrahim da ya nuna cewa Jehobah yana marmarin ba dukan masu biyayya rai na har abada. Littafin Ibraniyawa 11:17-19 ya bayyana cewa: “Ta wurin bangaskiya Ibrahim, da aka gwada shi, ya miƙa Ishaƙu; i, shi wanda ya karɓi alkawarai da farinciki yana cikin miƙa ɗansa haifaffensa kaɗai; wanda aka ce masa, Cikin Ishaƙu za a kira zuriyarka: ya aza Allah yana da iko ya tada mutum, ko daga matattu; inda ya sake karɓe shi kuma cikin misali.” Kamar yadda Ibrahim yake a shirye ya sadaukar da ɗansa da son ransa, haka ma Jehobah ya sadaukar da ɗansa, Yesu Kristi da son rai don ya ceci ’yan Adam.—Karanta Yohanna 3:16, 36.
9 Ka yi tunanin irin farin cikin da Ishaƙu ya yi sa’ad da ya fahimci cewa ba da shi za a yi hadaya ba. Babu shakka, ya yi godiya sosai cewa Jehobah ya yi tanadin rago a cikin kurmi da ke kusa don hadayar. (Far. 22:10-13) Shi ya sa Ibrahim ya kira sunan wajen “Jehovah-jireh,” wanda a Ibrananci yake nufin “Jehobah Zai Tanadar.”—Far. 22:14.
TANADI DON SULHU
10, 11. Su waye ne suke ja-gora a “hidima ta sulhu,” kuma ta yaya suka yi hakan?
10 Yayin da muke yin bimbini a kan dukan abubuwan da Jehobah ya tanadar mana, mun fahimci cewa da ba don tanadin hadayar Yesu ba, da ba za mu iya kasance da dangantaka da Jehobah ba. Bulus ya ce: “Gama haka mun gani, ɗaya ya mutu sabili da duka, duka fa suka mutu; kuma ya mutu sabili da duka, domin waɗanda ke rayuwa kada su ƙara rayuwa da kansu, amma ga wanda ya mutu ya kuwa tashi sabili da su.”—2 Kor. 5:14, 15.
11 Saboda ƙaunarsu ga Jehobah da kuma godiya don gatar bauta masa, Kiristoci na farko sun yi farin cikin karɓan “hidima ta sulhu.” Wannan hidimar ita ce wa’azi da kuma almajirtarwa da ke ba mutane damar yin sulhu da kuma ƙulla dangantaka mai kyau da Allah, daga baya kuma su sami zarafin zuwa sama a matsayin ’ya’yan Allah. Bayin Jehobah shafaffu suna yin wannan hidimar har ila. Su jakadu ne a madadin Allah da Kristi kuma hidimar da suke yi tana taimaka wa waɗanda suke da zuciyar kirki su kusaci Jehobah kuma su zama bayinsa.—Karanta 2 Korintiyawa 5:18-20; Yoh. 6:44; A. M. 13:48.
12, 13. Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga Jehobah saboda abubuwa da yawa da ya tanadar mana?
12 Waɗansu tumaki suna nuna godiyarsu ga Jehobah a matsayin Ainihin Mai Mana Tanadi ta wajen goyon bayan shafaffu don yin wa’azin Mulkin Allah. Muna amfani da Littafi Mai Tsarki a wannan aikin, kuma wannan wata kyauta ce mai tamani daga Allah. (2 Tim. 3:16, 17) Ta wajen yin amfani da hurarriyar Kalmar Allah sa’ad da muke wa’azi, muna ba wasu damar samun rai na har abada. Jehobah ya ƙara ba mu wata kyauta don mu yi nasara a wannan hidimar, wato ruhu mai tsarki. (Zak. 4:6; Luk 11:13) Sakamakon da ake samu a wannan aikin yana sa farin ciki kamar yadda rahotanni daga kowace fitowar Yearbook of Jehovah’s Witnesses take nunawa. Babu shakka, babban gata ne mu kasance cikin waɗanda suke yin wannan aikin da yake sa mutane su yabi Ubanmu mai yi mana tanadi!
13 Da yake Allah ya tanadar mana da abubuwa da yawa, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Shin ina iya ƙoƙarina a yin wa’azi don in nuna wa Jehobah cewa ina godiya don abubuwan da ya tanadar mini? Ta yaya zan kyautata yadda nake wa’azin bishara?’ Za mu iya nuna godiyarmu saboda abubuwan da Allah ya tanadar mana ta wajen saka al’amuran Mulki kan gaba a rayuwarmu. Idan muka yi hakan, babu shakka, Jehobah zai biya bukatunmu. (Mat. 6:25-33) Allah yana kula da mu sosai, saboda da haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi nufinsa kuma mu faranta masa rai.—Mis. 27:11.
14. Ta yaya Jehobah yake ceton mutanensa?
14 Dauda marubucin Zabura ya ce: “Ni matalauci ne, mai-talauci; Duk da haka Ubangiji yana tuna da ni: Kai ne taimakona, mai-cetona kuma.” (Zab. 40:17) Jehobah ya sha ceton al’ummarsa, musamman ma sa’ad da magabtansu suke tsananta musu. Muna farin ciki cewa Jehobah yana tanadar mana da abubuwan da suke taimaka mana mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar yanayi mai wuya.
JEHOBAH YANA KĀRE MU
15. Ka ba da misalin yadda uba mai ƙauna yake kāre ɗansa.
15 Uba mai ƙaunar yaransa yana biyan bukatunsu kuma yana kāre su. Yana hanzarin ceton su sa’ad da suka faɗa cikin haɗari. Wani ɗan’uwa ya tuna da yadda mahaifinsa ya taɓa cetonsa daga haɗari sa’ad da yake ƙarami. Shi da mahaifinsa suna dawowa daga wa’azi amma kafin su isa gida, sai sun haye wani rafi. An yi ruwa sosai da safiyar kuma hakan ya sa rafin ya cika har baki. Za a iya haye rafin ta wajen yin tsalle daga wani dutse zuwa wani. Yaron yana gaban babansa, da ya yi tsalle sai ya faɗa cikin rafin kuma ya nitse sau biyu. Baban ya kama kafaɗarsa nan da nan kuma ceto shi don kada ya sha ruwa, yaron ya gode sosai cewa babansa ya cece shi. Hakazalika, Ubanmu na sama yana kāre mu daga haɗarurrukan wannan mugun zamanin da kuma mai mulkin wannan zamanin, wato Shaiɗan. Hakika, Jehobah ne Ainihin Mai Kāre mu.—Mat. 6:13; 1 Yoh. 5:19.
16, 17. Ta yaya Jehobah ya taimaka da kuma kāre Isra’ilawa sa’ad da suka yaƙi Amalekawa?
16 Jehobah ya kāre mutanensa a shekara ta 1513 kafin zamaninmu. Kafin wannan lokacin, ya riga ya ceci Isra’ilawa daga bauta kuma ya kāre su sa’ad da suke haye Jar Teku. Bayan da suka yi tafiya a jeji ta Dutsen Sinai sai suka isa wani wuri da ake kira Rephidim.
17 Babu shakka, annabcin da ke Farawa 3:15 ya sa Shaiɗan ya so ya kai hari ga Isra’ilawa don a ganinsa ba su da kāriya. Ya yi hakan ta wajen yin amfani da magabtan bayin Allah, wato Amalekawa. (Lit. Lis. 24:20) Ta yaya Jehobah ya yi amfani da Joshua da Musa da Haruna da kuma Hur wajen kāre mutanensa daga waɗannan magabtan? Yayin da Joshua da mayaƙansa suke faɗa da mutanen Amalek, Musa da Haruna da kuma Hur suna kan wani dutse da ke kusa. Idan Musa ya ɗaga hannunsa, sai Isra’ilawan su riƙa yin nasara. Sa’ad da ya gaji, sai Haruna da Hur suka taimaka masa ta wajen riƙe hannayen. Saboda haka, “Joshua kuma ya kāda Amalek da mutanensa.” Ta hakan ne, Jehobah ya taimake su kuma ya kāre su. (Fit. 17:8-13) Bayan haka, sai Musa ya gina bagadi kuma ya kira sunan “Yahweh-nissi” ko kuma Jehobah nissi, wanda a Ibrananci yake nufin “Jehobah ne Mafakata.”—Karanta Fitowa 17:14, 15.
YANA KĀRE MU DAGA HANNUN SHAIƊAN
18, 19. Wace kāriya ce Jehobah yake tanadar wa bayinsa a zamaninmu?
18 Jehobah yana kāre waɗanda suke ƙaunarsa da kuma yi masa biyayya. Kamar yadda Isra’ilawa suka yi a Rephidim, mu ma muna dogara ga Allah don ya kāre mu daga magabtanmu. Jehobah yana kāre mu a matsayin al’ummarsa, kuma yana kuɓutar da mu daga tarkunan Shaiɗan. Alal misali, Jehobah ya kāre ’yan’uwanmu da suka kasance da aminci a batun tsakatsaki na Kirista. Wannan ya faru a ƙasar Jamus da wasu ƙasashe da ’yan Nazi suka mulka. Idan muka karanta labaran ’yan’uwanmu da ke cikin littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses da kuma wasu littattafanmu da suka yi magana game da yadda Allah ya kāre su kuma muka yi bimbini a kai, za mu sami ƙarfafa wajen dogara ga Jehobah a matsayin Mafakarmu.—Zab. 91:2.
19 Ƙungiyar Jehobah da kuma littattafanmu suna ba mu shawarwari da ke kāre mu. Ka yi tunanin yadda waɗannan shawarwari suka amfane mu a zamaninmu. Yayin da wannan duniyar take ƙara taɓarɓarewa a yin lalata da batsa da kuma shaye-shaye, Jehobah yana ba mu taimakon da muke bukata domin mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. Alal misali, muna samun shawara a kan yadda za mu guje wa mugun tarayya ta dandalin sadarwa na Intane.a—1 Kor. 15:33.
20. Ta yaya muke samun kāriya da ja-gora a ikilisiyar Kirista?
20 Ta yaya za mu nuna cewa Jehobah ne yake koyar da mu? Ta wurin kiyaye dokokinsa a kowane lokaci. (Isha. 54:13) Muna samun ja-gora da kāriya a ikilisiyoyinmu domin dattawa masu aminci suna ba mu shawara da taimako daga Littafi Mai Tsarki. (Gal. 6:1) Jehobah yana kula da mu sosai ta yin amfani da “kyautai ga mutane,” wato dattawa. (Afis. 4:7, 8) Mene ne ya kamata mu yi idan dattawa sun ba mu shawara? Mu yi marmarin bin wannan shawarar. Idan muka yi hakan, Jehobah zai albarkace mu.—Ibran. 13:17.
21. (a) Mene ne za mu ƙudura aniyar yi? (b) Mene ne za mu tattauna a talifin da ke gaba?
21 Bari mu ƙudura aniya cewa za mu bi ja-gorar ruhu mai tsarki da kuma na Ubanmu na sama. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi bimbini a kan irin rayuwar da Yesu ya yi kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu bi misali mai kyau da ya kafa. Saboda ya yi biyayya har bakin mutuwa, Jehobah ya albarkace shi sosai. (Filib. 2:5-11) Hakazalika, idan muka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu, zai albarkace mu. (Mis. 3:5, 6) Bari mu riƙa dogara ga Jehobah don shi ne mai tanadar mana da abubuwa da kuma kāre mu da kyau. Bauta wa Jehobah gata ne kuma abin ban farin ciki ne sosai! Amma, don me muka ce Jehobah ne babban amininmu? Talifin da ke gaba zai ba da amsar kuma hakan zai sa mu ƙara ƙaunarsa sosai.
a Za a sami waɗansu cikin shawarwarin a talifofin nan “Intane Yadda Za Mu Yi Amfani da Shi a Hanyar da Ta Dace” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2011, shafuffuka na 3-5 da kuma “Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2012, shafuffuka na 20-29.