ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZAI DACE KA YI ADDU’A KUWA?
Me Ya Sa Mutane Suke Yin Addu’a?
Kana yin addu’a kowace rana kuwa? Mutane da yawa suna yin hakan, har da waɗanda ba su yarda da wanzuwar Allah ba. Amma me ya sa mutane suke yin addu’a? Wani bincike da aka yi a Faransa ya nuna cewa kashi hamsin bisa ɗari na ’yan ƙasar suna yin addu’a ko kuma bimbini “domin hankalinsu ya kwanta.” Ba sa ɗaukan yin addu’a a matsayin ibada, kamar yadda Turawa da yawa ba sa yi. Maimakon haka, suna yin addu’a ne kawai domin suna so su sami kwanciyar hankali da suke ganin ana samu daga yin addu’a. A wani ɓangare kuma, wasu masu bi ma suna yin addu’a a lokacin da suke da bukata ne kawai, kuma suna so Allah ya amsa addu’ar nan da nan.—Ishaya 26:16.
Kai kuma fa? Kana ɗaukan addu’a a matsayin abin da za ka yi ne kawai don ka wartsake? Idan kai mai bin Allah ne, kana ganin yadda addu’a take taimaka maka kuwa? Ko kuma kana ganin ba a amsa addu’o’inka ne? Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka ɗauki addu’a a matsayin hanya mai tamani na kusantar Allah, a maimakon maganin kwanciyar hankali kawai.