Kana Ɗaukan Kasawar Wasu Yadda Jehobah Yake Ɗaukansu Kuwa?
“Gaɓaɓuwa da ake ganinsu kamar raunana bukatattu ne.”—1 KOR. 12:22.
1, 2. Mene ne ya taimaka wa Bulus ya fahimci yanayin waɗanda suka raunana?
DUKANMU mukan raunata a wasu lokatai. Mura ko zazzaɓi zai iya sa mu kasala kuma mu kasa yin wasu ayyukan da ya kamata mu yi. Amma yanzu ka ɗauka cewa wata illa ta sa ka raunana kuma ka daɗe kana cikin wannan yanayin. Yaya za ka so wasu su bi da kai? Babu shakka, za ka so su fahimci yanayinka kuma su tausaya maka, ko ba haka ba?
2 A wasu lokatai, manzo Bulus ya sami kansa a irin wannan yanayin saboda matsalolin da ya fuskanta daga mutane a waje da kuma ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya. Har ma a wasu lokuta ya ɗauka cewa abin ya fi ƙarfinsa. (2 Kor. 1:8; 7:5) Sa’ad da yake magana game rayuwarsa da kuma wahalolin da ya fuskanta, Bulus ya ce: “Wanene rarrauna, ni ban zama rarrauna kuwa?” (2 Kor. 11:29) Bulus ya kwatanta ikilisiyar Kirista da gaɓoɓin jikin mutum kuma ya ce, “gaɓaɓuwa da ake ganinsu kamar raunana bukatattu ne.” (1 Kor. 12:22) Mene ne hakan yake nufi? Me ya sa ya kamata mu ɗauki waɗanda ake gani raunana ne kamar yadda Jehobah yake ɗaukan su? Kuma ta yaya hakan zai amfane mu?
YADDA JEHOBAH YAKE ƊAUKAN KASAWARMU
3. Mene ne zai iya shafan yadda muke ɗaukan ’yan’uwa da suke bukatar taimako a cikin ikilisiya?
3 Mutane da yawa a duniya yanzu suna wulaƙanta marasa ƙarfi don su sami abin da suke so. Suna gani cewa idan kana da ƙwarjini shi ne za ka iya samun ci gaba. Irin wannan halin zai iya shafanmu kuma mu soma raina ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya da suke bukatar taimako. Amma za mu iya kasancewa da ra’ayi irin na Jehobah. Ta yaya za mu iya yin hakan?
4, 5. (a) Ta yaya kwatancin da ke 1 Korintiyawa 12:21-23 ya sa mun fahimci yadda Jehobah yake ɗaukan kasawa? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka taimaka wa waɗanda suka kasa?
4 Za mu iya gane yadda Jehobah yake ɗaukan kasawarmu idan muka yi la’akari da wani kwatanci da Bulus ya yi a wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korintiyawa. A sura ta 12, Bulus ya ce gaɓar jikin da ta fi muni ma tana da amfani. (Karanta 1 Korintiyawa 12:12, 18, 21-23.) Wasu da suka gaskata da ra’ayin bayyanau sun ce akwai wasu abubuwa a jikinmu da ba su da amfani. Amma wasu bincike da masu ilimin halittar jiki suka yi ya nuna cewa wasu abubuwa a cikin jikinmu da aka ɗauka cewa ba su da amfani suna da muhimmanci.a Alal misali, a dā wasu sun musunta amfanin ƙaramar yatsar; amma, yanzu an gano cewa tana taimaka mana kada mu faɗi idan muna tsaye.
5 Kwatancin Bulus ya nuna cewa dukan ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya suna da muhimmanci. Shaiɗan yana so mu ɗauka cewa ba mu da amfani. Amma Jehobah ya ɗauki dukan bayinsa da mutunci har da waɗanda ake gani sun raunana. (Ayu. 4:18, 19) Ya kamata hakan ya taimaka mana mu daraja matsayinmu a cikin ikilisiyarmu kuma a ƙungiyar Jehobah. Ka tuna lokacin da ka taimaka wa wani da ya tsufa da ke bukatar taimako. Wataƙila ka daidaita yanayinka da nasa. Babu shakka, ya amfana. Amma ba ka ji daɗi cewa ka taimaka masa ba? Hakika, duk lokacin da muka taimaka wa mutane muna farin ciki kuma muna koyan halaye masu kyau kamar haƙuri da ƙauna kuma za mu nuna cewa mun manyanta. (Afis. 4:15, 16) Ubanmu mai ƙauna yana son mu san cewa dukan waɗanda ke cikin ikilisiya suna da amfani kuma hakan ya haɗa da waɗanda ake gani sun kasa. Idan muka kasance da irin ra’ayinsa, ƙauna za ta bunƙasa a cikin ikilisiya.
6. Mene ne kalmomin nan “raunana” da “ƙarfafa” suke nufi kamar yadda Bulus ya yi amfani da su?
6 Gaskiya ne cewa manzo Bulus ya yi amfani da kalmomin nan “raunana” da kuma “rashin ƙarfi” sa’ad da ya yi magana game da wasu a cikin ikilisiya. Ya yi hakan ne don yadda marasa bi suke ɗaukan Kiristoci. Amma Bulus ba ya nufin cewa wasu Kiristoci sun fi wasu daraja ba. Ƙari ga haka, ya ce shi da kansa ma raunanne ne. (1 Kor. 1:26, 27; 2:3) Sa’ad da Bulus ya yi amfani da kalmar nan “ƙarfafa” wajen kwatanta wasu Kiristoci ba ya nufin cewa waɗannan sun fi sauran ’yan’uwansu daraja. (Rom. 15:1) A maimakon haka, yana nufin cewa Kiristoci da suke da ƙwazo su riƙa haƙuri da waɗanda ba su ƙware ba.
MUNA BUKATAR MU DAIDAITA RA’AYINMU NE?
7. Me ya sa taimaka wa waɗanda suke bukatar taimako bai da sauƙi?
7 Sa’ad da muka taimaka wa waɗanda suka kasa, muna yin koyi da Jehobah ne kuma zai albarkace mu. (Zab. 41:1; Afis. 5:1) Amma yin hakan bai da sauƙi. Me ya sa? Wataƙila muna tunani cewa hakkin kowa ne ya magance matsalarsa, saboda kowa ya yi ta kansa. Ko kuma don ba mu san yadda za mu taimaka musu ba, sai mu riƙa gudun su. Wata ’yar’uwa mai suna Cynthia,b wanda maigidanta ya gudu ya bar ta, ta ce: “Ba za ka ji daɗi ba idan ’yan’uwa suna gudun ka ko kuma ba sa yin abubuwan da ya kamata abokai na kud da kud su yi. Sa’ad da kake fama da matsaloli, kana bukatar mutane su riƙa kasancewa kusa da kai.” Sarki Dauda ya fuskanci irin wannan yanayi na rashin jin daɗi sa’ad da abokansa suka yashe shi.—Zab. 31:12.
8. Me zai taimaka mana mu kasance da tausayi sosai?
8 Za mu iya kasancewa masu tausayi idan muka tuna cewa ’yan’uwanmu maza da mata sun raunana ne don suna fama da rashin lafiya ko kuma don suna zama a cikin iyalin da ba a bauta wa Jehobah. Wasu kuma don suna fama da bakin ciki mai tsanani. Za mu iya fuskantar irin wannan yanayin a nan gaba. Ka tuna da Isra’ilawa. Sun sha wahala sosai a ƙasar Masar, amma kafin su shiga ƙasar alkawari, Jehobah ya ce musu sa’ad da matalauci ya bukaci taimako, kada su ‘taurare masa zuciyarsu ba.’ Jehobah yana so su san cewa ya cancanta a taimaka wa matalauta.—K. Sha 15:7, 11; Lev. 25:35-38.
9. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da ’yan’uwanmu suna fuskantar matsaloli? Ka ba da misali.
9 Bai kamata mu ɗauka cewa wani abin da ’yan’uwanmu suka yi ne ya sa suke fuskantar matsaloli ba ko kuma mu yi tunani cewa mun fi su. A maimakon haka, ya kamata mu taimaka wa ’yan’uwanmu sa’ad da suke bukatar taimako. (Ayu. 33:6, 7; Mat. 7:1) Alal misali, a ce wani ya yi hatsari da babur kuma aka kai shi asibiti. Mene ne ma’aikatan jinyar za su yi? Za su soma bincika wanda ya haddasa hatsarin ne? Babu, za su yi jinyar wanda ya ji ciwo ba tare da ɓata lokaci ba. Hakazalika, idan matsaloli sun sa wani ɗan’uwanmu ya raunana, abin da ya kamata mu yi shi ne mu taimaka masa.—Karanta 1 Tasalonikawa 5:14.
10. Me ya sa za mu iya ce waɗanda suka raunana “mawadata cikin bangaskiya” ne?
10 Idan muka yi tunanin yanayin ’yan’uwanmu da suka raunana, za mu fahimta cewa suna ƙoƙari. Wasu kasassu ne, amma kuma suna da ƙarfin hali. Ka yi tunanin irin ƙoƙarin da ’yar’uwar da maigidanta ba Mashaidi ba take yi. Ko kuma mahaifiya mai rainon ’ya’yanta ita kaɗai da take zuwa taro tare da yaran a kai a kai. Shin ba ka ganin cewa suna da bangaskiya da ƙarfin zuciya? Akwai matasan da ke fuskantar matsi a makaranta amma duk da haka, sun yi tsayin daka. Idan muka yi tunanin ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ’yan’uwanmu suke yi don su bauta wa Jehobah, hakan zai taimaka mana mu ɗauke su “mawadata cikin bangaskiya” kamar sauran ’yar’uwanmu da yanayinsu ke da ɗan dama.—Yaƙ. 2:5.
KA KASANCE DA IRIN RA’AYIN JEHOBAH
11, 12. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da irin ra’ayin Jehobah game da kasawar wasu? (b) Wane ne darasi ne muka koya game da yadda Jehobah ya bi da Haruna?
11 Misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kasance da irin ra’ayin Jehobah game da kasawar bayinsa. (Karanta Zabura 130:3.) Alal misali, a ce kana nan tare da Musa a lokacin da Haruna yake bayyana dalilin da ya sa ya ƙera maraƙin na zinariya, tunanin me za ka yi game da hujjojin da Haruna ya bayar? (Fit. 32:21-24) Ko kuma yaya za ka ɗauki Haruna a lokacin da yayarsa Maryamu ta sa shi sūkar Musa don ya auri macen da ba Ba’isra’iliya ba? (Lit. Lis. 12:1, 2) Da a ce kai ne, da mene ne za ka yi a lokacin da Haruna da Musa suka ƙi ba da girma ga Jehobah a lokacin da Ya tanadar wa Isra’ilawa ruwa a yankin Meribah ta hanyar mu’ujiza?—Lit. Lis. 20:10-13.
12 Da Jehobah ya hukunta Haruna don waɗannan kurakuran da ya yi nan da nan. Amma ya san cewa ko da yake Haruna ya kasa a wasu lokatai, shi ba mugun mutum ba ne. Wataƙila Haruna ya yi waɗannan abubuwa don an matsa masa kuma don ya saurari miyagun shawarwarin wasu ne. Amma, sa’ad da aka gaya masa laifin da ya yi, bai yi musu ba amma ya amince da hukuncin Jehobah. (Fit. 32:26; Lit. Lis. 12:11; 20:23-27) Jehobah ya ƙaunaci Haruna don bangaskiyarsa da halin tuba da yake da shi. Ƙarnuka bayan haka, abin da aka tuna game da Haruna da zuriyarsa shi ne tsoron Jehobah da suka kasance da shi.—Zab. 115:10-12; 135:19, 20.
13. Ta yaya za mu iya canja tunaninmu game da kasawar wasu? Ka ba da misali.
13 ’Yan’uwanmu za su iya yin kuskure kamar yadda Haruna ya yi. Idan hakan ya faru, yaya ya kamata mu ɗauke su? Muna bukata mu daidaita tunaninmu ne? (1 Sam. 16:7) Alal misali, yaya muke bi da matashin da yake nishaɗin da bai dace ba, ko kuma wanda yake da wuyan sha’ani? Kada mu yi saurin ɗauka cewa shi mugu ne. A maimakon haka, mu yi tunanin yadda za mu iya taimaka masa. Zai dace mu koya masa yadda zai yanke shawarwari masu kyau. Sa’ad da muka taimaka wa ’yan’uwanmu, za mu kasance da haƙuri kuma za mu ƙaunace su sosai.
14, 15. (a) Mene ne Jehobah ya yi sa’ad da ya lura cewa Iliya ya tsorata? (b) Wane darasi ne za mu koya daga yadda Jehobah ya taimaka wa Iliya?
14 Za mu iya daidaita ra’ayinmu da na Jehobah idan muka yi la’akari da yadda ya bi da wasu bayinsa da suka yi baƙin ciki mai tsanani. Iliya ɗaya ne daga cikinsu. Ya nuna gaba gaɗi sa’ad da ya ƙalubalanci masu bautar Baal amma ya gudu don ya ji cewa Sarauniya Jezebel tana so ta kashe shi. Tsoro ya sa shi ya yi tafiyar kilomita 150 zuwa Beer-sheba, daga baya ya shiga ciki cikin daji. Saboda wannan doguwar tafiyar da ya yi cikin rana, ya gaji kuma sai ya zauna a ƙarƙashin bishiya yana Allah-Allah ya “mutu.”—1 Sar. 18:19; 19:1-4.
15 Mene Jehobah ya yi sa’ad da ya ga yadda Iliya ya tsorata kuma yana baƙin ciki? Ya yi watsi da Iliya ne? A’a! Jehobah ya yi la’akari da yanayin bawansa Iliya kuma ya tura mala’ika don ya ƙarfafa shi. Mala’ikan ya ba Iliya abinci sau biyu don kada ‘tafiyar ta fi ƙarfinsa.’ (Karanta 1 Sarakuna 19:5-8.) Hakika, kafin ya ba da wani umurni wa Iliya, Jehobah ya saurare shi kuma ya tanadar masa da taimakon da yake bukata.
16, 17. Ta yaya za mu yi koyi da yadda Jehobah ya kula da Iliya?
16 Ta yaya za mu yi koyi da Allahnmu mai ƙauna? Bai kamata mu riƙa saurin ba da shawara wa ’yan’uwanmu ba. (Mis. 18:13) Zai fi kyau mu tausaya wa waɗanda muke ganin “marasa-daraja” saboda yanayinsu. (1 Kor. 12:23) Bayan haka ne za mu iya ɗaukan matakan da suka dace don mu taimaka musu.
17 Ka tuna da Cynthia da aka ambata ɗazu, wadda maigidanta ya gudu ya bar ta da ’ya’ya mata biyu. Ba su ji daɗi ba ko kaɗan don yadda ya yi watsi da su. Ta yaya ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya suka taimaka musu? Cynthia ta ce: “Cikin minti 45 da muka sanar da su, sun zo gidanmu. Suna ta kuka. Sun zauna tare da mu na tsawon kwana biyu ko uku. Da yake ba ma iya cin abinci da kyau kuma mun kasala, sai suka gayyace mu zauna tare da su a gidajensu.” Wannan labarin zai sa ka tuna da abin da Yaƙub ya rubuta cewa: “Idan wani ɗan’uwa ko’yar’uwa suna a tsiraici, kuma sun rasa abincin yini, ɗaya kuwa daga cikinku ya ce masu, Ku tafi lafiya, ku ji ɗumi, ku ƙoshi; ba ku ko ba su bukatar jiki ba; me ya amfana? Hakanan kuwa bangaskiya, in ba ta da ayyuka ba, mataciya ce cikin kanta.” (Yaƙ. 2:15-17) Taimakon da ’yan’uwa suka tanadar wa ’yar’uwa Cynthia da ’ya’yanta shi ne abin da suke bukata a lokacin. Wata shida bayan haka, Cynthia da ’ya’yanta suka sami ƙarfafa sosai har suka soma hidima ta ɗan lokaci.—2 Kor. 12:10.
’YAN’UWA DA YAWA ZA SU AMFANA
18, 19. (a) Ta yaya za mu iya taimaka wa waɗanda suka raunana? (b) Su wane ne suke amfana sa’ad da muka taimaka wa marasa ƙarfi?
18 Idan muna farfaɗowa daga rashin lafiya, yana ɗaukan lokaci kafin mu warware. Hakazalika, ɗan’uwa da kasala yana kamar wanda yake rashin lafiya ne, zai ɗauki lokaci kafin ya sake kasancewa da himma a bautarsa ga Jehobah. Gaskiya ne cewa wajibi ne ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a, kuma ya riƙa halartan taro a kai a kai don ya farfaɗo. Amma yana bukatar taimakonmu. Shin sa’ad da yake farfaɗowa, za mu nuna masa ƙauna da haƙuri kuwa? Ya kamata mu ci gaba da nuna masa ƙauna kuma mu taimaka masa ya fahimci cewa yana da amfani a cikin ikilisiya.—2 Kor. 8:8.
19 Muna yin farin ciki sa’ad da muka taimaka wa wasu. Ƙari ga haka, muna koyan halaye masu kyau kamar tausayi da haƙuri. Amma, ba mu kaɗai ba ne ke amfana. ’Yan’uwa a cikin ikilisiya za su ƙara nuna ƙauna ga juna. Mafi muhimmanci, muna koyi da Jehobah wanda yake ɗaukan kowane bawansa da mutunci. Hakika, muna da dalilai da yawa na bin umurnin da ya ce mu “taimaki marasa ƙarfi.”—A. M. 20:35.
a Charles Darwin a cikin wani littafinsa mai suna The Descent of Man, ya ce wasu abubuwan da ke cikin jikinmu “marasa amfani” ne. Wani mai ra’ayin bayyanau ya ce akwai abubuwa a cikin jikinmu da yawa da ba su da amfani, kamar tsiro da ke uwar hanji da ake kira appendix, da kuma wani halittar cikin jiki da ke kusa da wuya da ake kira thymus.
b An canja sunan.