Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 p. 22
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Su Wane ne Mahaya Hudun?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Yadda Mahaya Hudun Suke Shafan Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 p. 22

KA TUNA?

Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

A wane lokaci ne za a yanka ragon Idin Ƙetarewa a ranar 14 ga Nisan?

Wasu mafassaran Littafi Mai Tsarki sun ce ya kamata a yanka ragon “tsakanin yammar biyu,” wato da maraice ko da faɗuwar rana sa’ad da gari bai yi duhu sosai ba. (Fit. 12:6)​—12/15, shafuffuka na 18-19.

Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka wa matasa su yi zaɓi mai kyau?

Uku cikinsu su ne (1) Ku fara biɗan Mulkin Allah da kuma adalcinsa. (Mat. 6:19-34) (2) Ka yi wa wasu hidima da farin ciki. (A. M. 20:35) (3) Ka ji daɗin yi wa Jehobah ibada a ƙuruciyarka. (M. Wa. 12:1)​—1/15, shafuffuka na 19-20.

Yaushe ne za a ɗaura auren Ɗan ragon? (R. Yoh. 19:7)

Za a ɗaura auren Ɗan ragon bayan Sarki Yesu Kristi ya halaka Babila Babba kuma an kammala yaƙin Armageddon.​—2/15, shafi na 10.

Me ya sa Yahudawa na ƙar na farko suka yi ɗokin zuwan Almasihu? (Luk 3:15)

Ko da yake ba mu da tabbaci cewa Yahudawa a ƙarni na farko sun fahimci annabcin da Daniyel ya yi game da Almasihu kamar yadda muka fahimce shi a yau. (Daniyel 9:24-27) Duk da haka, wataƙila sun ji labarin yadda mala’ika ya sanar da wasu makiyaya ko kuma sun ji abin da annabiya Hannatu ta faɗa da ta ga Yesu sa’ad da yake jariri a lokacin da aka kawo shi haikali. Ƙari ga haka, shehuna ma sun zo suna neman “sarkin Yahudawa,” da aka haifa. (Mat. 2:1, 2) Daga baya, Yohanna mai yin baftisma ya nuna cewa Kristi zai bayyana ba da daɗewa ba.​—2/15, shafuffuka na 26-27.

Ta yaya za mu guji faɗin I daga baya kuma mu ce A’a? (2 Kor. 1:18)

Hakika, a wani lokaci zai zama dole mu kasa cika wani alkawarin da muka yi don wata larura da ta kama mu. Amma ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu cika alkawarin da muka yi.​—3/15, shafi na 32.

Ta yaya ne za mu guji kallon batsa?

Ga wasu matakai uku (1) Mu kawar da idanunmu daga abubuwan da za su iya tayar da sha’awar jima’i nan da nan. (2) Mu riƙa tunanin abubuwa masu kyau kuma mu duƙufa a yin addu’a. (3) Mu guji fina-finai da dandalin Intane da suke ɗaukaka batsa.​—Satumba-Oktoba shafi na 7.

Wane sakamako marar kyau ne ake samu idan wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa ta bar gida ko iyalinta zuwa wata ƙasa don neman kuɗi?

Idan iyaye da yara ba sa zama tare a gida ɗaya, yaran ba za su ji daɗin rayuwa ba kuma wataƙila ba za su sami tarbiyya mai kyau ba. Kuma yaran za su iya tsanan iyayensu. Ƙari ga haka, ma’aurata da ba sa zama tare za su iya fuskantar jarabar yin zina.​—4/15, shafuffuka na 19-20.

Waɗanne tambayoyi huɗu ne ya kamata mu tuna da su sa’ad da muke so mu yi wa mutane wa’azi?

Wane ne nake yi wa wa’azi? A ina ne nake yi wa mutane wa’azi? A wane lokaci ne ya fi dacewa in yi wa mutane wa’azi? Ta yaya ya kamata mu yi wa mutane wa’azi?​—5/15, shafuffuka na 12-15.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba