AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Me ya sa zai dace mu yi addu’a?
Jehobah yana so mu riƙa yin magana da shi a kai a kai, muna gaya masa damuwarmu. (Luka 18:1-7) Yana sauraronmu domin ya damu da mu. Tun da yake Ubanmu na sama ya ba mu damar yin addu’a, zai dace mu yi hakan, ko ba haka ba?—Karanta Filibiyawa 4:6.
Addu’a ba hanyar neman taimako ba ce kawai. Maimakon haka, addu’a tana taimaka mana mu kusaci Allah. (Zabura 8:3, 4) Idan muna gaya wa Allah abubuwan da ke zuciyarmu a kai a kai, dangantakarmu da shi za ta daɗa danƙo.—Karanta Yaƙub 4:8.
A wace hanya ce ya kamata mu yi addu’a?
Yayin da muke addu’a, Allah ba ya so mu riƙa yin amfani da kalmomin burga ko maimaita addu’o’in da muka haddace. Ƙari ga haka, ba lallai sai mun tsaya ko mun durƙusa kafin mu yi addu’a ba. Jehobah ya ce mu riƙa yin addu’a daga zuciya. (Matta 6:7) Alal misali, a ƙasar Isra’ila ta dā, Hannatu ta yi addu’a game da wata matsala a iyalinta da ke ci mata tuwo a ƙwarya. Sa’ad da aka biya mata bukatarta, ta yi godiya ga Allah ta addu’a.—Karanta 1 Sama’ila 1:10, 12, 13, 26, 27; 2:1.
Hakika addu’a babban gata ne a gare mu! A cikin addu’a, za mu iya gaya wa Mahaliccinmu matsalolinmu. Za mu iya yabonsa kuma mu gode masa don alherinsa. Saboda haka, kada mu yi watsi da wannan babban gatan.—Karanta Zabura 145:14-16.