Ka Riƙa Jin Muryar Jehobah a Duk Inda Kake
“Kunnuwanka kuma za su ji magana daga bayanka, tana cewa, Wannan ita ce hanya.”—ISHA. 30:21.
1, 2. Ta yaya Jehobah yake yi wa bayinsa ja-gora?
JEHOBAH yana ja-gorar mutanensa tun da daɗewa. Ya bayyana wa wasu mutane abin da zai faru a nan gaba ta wurin yin amfani da mala’iku ko wahayi ko kuma mafarkai. Ƙari ga haka, Jehobah ya ba su takamammun ayyuka. (Lit. Lis. 7:89; Ezek. 1:1; Dan. 2:19) Wasu kuma sun sami ja-gora daga mutane da suke wakiltar sashen ƙungiyar Jehobah a duniya. Ko da a wace hanya ce Jehobah ya ba mutane kalmarsa, waɗanda suka bi umurninsa sun sami albarka.
2 A yau, Jehobah yana amfani da Littafi Mai Tsarki da ruhunsa mai tsarki da kuma ikilisiya don ya ja-goranci mutanensa. (A. M. 9:31; 15:28; 2 Tim. 3:16, 17) Yana ja-gorarmu a hanyar da za mu fahimta kamar kunnuwanmu suna jin murya daga bayanmu tana cewa: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.” (Isha. 30:21) Ƙari ga haka, Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya ja-goranci ƙungiyarsa ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45) Muna bukatar mu ɗauki ja-gorancin da yake mana da muhimmanci don rayuwarmu ta har abada ta dangana ga yin biyayya.—Ibran. 5:9.
3. Me zai iya sa ya kasance mana da wuya mu saurari muryar Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
3 Shaiɗan Iblis ya san cewa bin ja-gorar Jehobah zai ceci rayukanmu, shi ya sa yake ƙoƙari ya hana mu sauraron muryar Jehobah. Ƙari ga haka, zuciyarmu tana da “rikici” kuma za ta iya shafan yadda muke bin ja-gorar Jehobah. (Irm. 17:9) Don haka, bari mu tattauna yadda za mu iya shawo kan abubuwan da za su sa ya kasance mana da wuya mu saurari muryar Jehobah. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda sauraron Jehobah da kuma tattauna da shi a addu’a zai iya taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da shi a kowane lokaci.
YADDA ZA MU SHAWO KAN DABARUN SHAIƊAN
4. Ta yaya Shaiɗan yake gurɓata tunanin mutane?
4 Shaiɗan yana ƙoƙari ya gurɓata tunanin mutane ta wurin yi musu ƙarya da kuma yaɗa bayanai masu yaudara. (Karanta 1 Yohanna 5:19.) Ban da littattafan da ake wallafawa, ana yaɗa ƙarya ta rediyo da talabijin da kuma Intane a ko’ina a duniya. Ko da yake ana iya samun wasu bayanai masu amfani a waɗannan wuraren, amma waɗannan kafofin suna iya ɗaukaka wasu halaye da kuma ra’ayoyin da suka saɓa wa ƙa’idodin Jehobah. (Irm. 2:13) Alal misali, suna ɗaukaka auren jinsi ɗaya, kuma hakan ya sa mutane suna gani cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da luwaɗi ya wuce gona da iri.—1 Kor. 6:9, 10.
5. Ta yaya za mu guji ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan?
5 Ta yaya waɗanda suke ƙaunar ƙa’idodin Jehobah za su guji ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan? Ta yaya za su iya bambanta nagarta da mugunta? ‘Ta wurin biyayya da umurnan [Allah].’ (Zab. 119:9, Littafi Mai Tsarki) Kalmar Allah tana ɗauke da ja-gorar da za ta iya taimaka mana mu sansance gaskiya daga ƙarya. (Mis. 23:23) Yesu ya yi ƙaulin Nassosi kuma ya ce: “Mutum za ya rayu . . . da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Mat. 4:4) Ya kamata mu koyi yadda za mu riƙa yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka yi la’akari da misalin Yusufu. Tun da daɗewa kafin Musa ya rubuta dokar Allah game da yin zina, Yusufu ya fahimci cewa zina zunubi ne a gaban Allah. Bai ma yi tunanin yi wa Jehobah laifi ba sa’ad da matar Fotifa ta matsa masa ya yi abin da bai da kyau. (Karanta Farawa 39:7-9.) Ko da yake ta daɗe tana matsa masa, amma Yusufu bai yarda ta rinjaye shi ya yi zunubi a gaban Allah ba. Yana da muhimmanci mu saurari muryar Jehobah, ba ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yaɗawa ba.
6, 7. Mene ne muke bukatar yi idan muna so mu guji shawarar ƙarya ta Shaiɗan?
6 Duniya tana cike da koyarwa masu rikitarwa na addini kuma hakan ya sa mutane da yawa sun ɗauka cewa ba zai yiwu a sami addinin gaskiya ba. Amma Jehobah ya tanadar da ja-gora ga waɗanda suke so. Tun da haka ne, dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Ba zai taɓa yiwuwa mu saurari muryoyi biyu a lokaci ɗaya ba. Saboda haka, ya kamata mu ‘san muryar’ Yesu kuma mu saurare shi domin shi ne Jehobah ya naɗa ya kula da tumakinsa.—Karanta Yohanna 10:3-5.
7 Yesu ya ce: “Ku yi lura fa da abin da kuke ji.” (Mar. 4:24) Umurnin Jehobah yana nan dalla-dalla da kuma kyau, duk da haka, wajibi ne mu saurari umurnin da zuciya ɗaya. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya sauraron shawarar Shaiɗan maimakon shawara mai kyau da Allah ke bayarwa. Saboda haka, bai kamata mu bar waƙoƙi da bidiyoyi da shirye-shiryen talabijin da littattafai da abokai da malamai da masana na wannan duniyar su yi iko da mu ba.—Kol. 2:8.
8. (a) Ta yaya zuciyarmu za ta iya sa Shaiɗan ya rinjaye mu? (b) Me zai iya faruwa idan muka ƙi yin hattara da alamun da suke nuna cewa mun kusan yin zunubi?
8 Shaiɗan ya san cewa muna fama da jarabar yin zunubi, saboda haka, yana ƙoƙarin ganin cewa mun yi abubuwan da ba su da kyau. Sa’ad da Shaiɗan ya yi yunkurin rinjayar mu mu yi zunubi, kasancewa da aminci ga Jehobah yana yin wuya. (Yoh. 8:44-47) Ta yaya za mu iya yin nasara? Ka yi la’akari da mutumin da ya ƙyale sha’awar yin zunubi ta mamaye zuciyarsa kuma a ƙarshe ya yi zunubin da bai taɓa tsammanin zai yi ba. (Rom. 7:15) Shin me ya kai ga haka? Wataƙila ya daina sauraron muryar Jehobah da sannu-sannu. Zai iya zama cewa bai yi hattara da abin da ke shiga zuciyarsa ba ko kuma ya ƙyale hakan ya faru da gangan. Mai yiwuwa, ya daina yin addu’a ko halartan taro ko kuma fita wa’azi a kai a kai. Da shigewar lokaci, ya ƙyale sha’awar yin abin da bai da kyau ta mamaye tunaninsa kuma ya yi zunubi. Za mu iya guje wa irin wannan mugun yanayin idan mun mai da hankali ga alamun da suke nuna cewa mun kusa yin zunubi kuma muka ɗauki mataki nan da nan don mu daidaita yanayin. Ƙari ga haka, idan muna sauraron muryar Jehobah, za mu yi tir da ra’ayoyin ’yan ridda.—Mis. 11:9.
9. Me ya sa yake da muhimmanci mu gano abubuwan da za su sa mu faɗa cikin masifa tun da wuri?
9 Idan mutum yana rashin lafiya, sanin irin cutar da ke damunsa tun da wuri zai iya ceton ransa. Hakazalika, za mu iya guje wa masifa idan muka gano abubuwan da za su iya sa mu faɗa cikin wannan yanayin. Da zarar mun gano waɗannan abubuwan, zai dace mu ɗauki mataki nan da nan kafin ‘Iblis ya tsare mu’ mu yi nufinsa. (2 Tim. 2:26, LMT) Mene ne za mu iya yi idan muka gano cewa tunaninmu da muradinmu ya yi nesa da abin Jehobah yake bukata a gare mu? Zai dace mu dawo wurinsa ba tare da ɓata lokaci ba, kuma mu buɗe kunnuwanmu don mu saurari shawararsa da zuciya ɗaya. (Isha. 44:22) Gaskiyar ita ce, idan muka yanke shawara marar kyau, hakan zai iya sa mu baƙin ciki sosai kuma mu sha wahala a wannan mugun zamanin. Shi ya sa zai dace mu ɗauki mataki nan da nan sa’ad da muka gano cewa muna bijirewa don kada mu sha irin wannan wahalar!
SHAWO KAN FAHARIYA DA HAƊAMA
10, 11. (a) Waɗanne alamu ne za su nuna ko mutum yana da fahariya? (b) Wane darasi za mu iya koya daga tawayen da Korah da Dathan da kuma Abiram suka yi?
10 Ya kamata mu fahimci cewa zuciyarmu ma za ta iya sa mu bijire wa Jehobah. Kuma hakan ya nuna cewa sha’awar yin zunubi tana da ƙarfi sosai! Ka yi la’akari da waɗannan misalan, fahariya da kuma haɗama. Ka bincika yadda kowane cikin waɗannan halayen zai iya sa mu daina sauraron muryar Jehobah kuma mu bi wani tafarki da zai sa mu faɗa cikin masifa. Mutum mai fahariya yana ɗaukan kansa da muhimmanci kuma don haka, yana gani kamar zai riƙa yin duk abin da ya ga dama kuma babu wanda ya isa ya gaya masa abin da zai yi. Saboda haka, zai iya gani ya fi ƙarfin bin ja-gora da kuma shawarar da Kiristoci da dattawa da kuma ƙungiyar Jehobah ke bayarwa. Irin wannan mutumin zai yi nesa da Jehobah kuma ba zai iya jin muryarsa ba.
11 A lokacin da Isra’ilawa suke tafiya a jeji, Korah da Dathan da Abiram sun yi wa Musa da Haruna tawaye. Da yake suna da fahariya, sun so su bauta wa Jehobah yadda suka ga dama. Wane mataki ne Jehobah ya ɗauka? Ya halaka su. (Lit. Lis. 26:8-10) Wannan labarin ya koya mana wani darasi mai muhimmanci sosai! Yin tawaye da Jehobah yana jawo masifa. Bari mu riƙa tuna cewa “bayan girman kai sai halaka.”—Mis. 16:18; Isha. 13:11.
12, 13. (a) Ka ba da wani misalin da ya nuna cewa haɗama za ta iya haifar da mutuwa. (b) Ka bayyana yadda haɗama za ta iya mamaye zuciyarmu nan da nan idan ba mu mai da hankali ba.
12 Ka yi la’akari kuma da haɗama. Mai haɗama yana gani cewa ja-gorar Jehobah bai shafe shi ba kuma yana yin abin da ya ga dama ko da hakan ya saɓa wa ƙa’ida. Alal misali, sa’ad da annabi Elisha ya warƙar da wani sojan Suriya mai suna Na’aman daga kuturtarsa, sojan ya ba shi kyauta amma annabin ya ƙi karɓa. Amma, bawan Elisha mai suna Gehazi, ya yi kwaɗayin kyautan kuma ya gaya wa kansa: “Na rantse da ran Ubangiji, zan bi shi a guje, in karɓi wani abu daga gareshi.” Ba tare da sanin Elisha ba, Gehazi ya bi Na’aman a guje kuma ya yi masa ƙarya cewa annabin ya ce a ba shi “talent guda na azurfa, da riga biyu.” Me ya faru da Gehazi a sakamakon abin da ya yi da kuma ƙaryar da ya yi wa annabin Jehobah? Kuturtar Na’aman ta kama Gehazi!—2 Sar. 5:20-27.
13 Haɗama takan soma da sannu-sannu kuma idan ba mu mai da hankali ba, za ta mamaye mu kuma ta ɓata halinmu. Labarin Achan a Littafi Mai Tsarki ya nuna abin da haɗama za ta iya haddasawa. Ka lura da yadda haɗama ta mamaye zuciyar Achan nan da nan. Ya ce: ‘Sa’anda na ga wani kyakkyawan mayafi irin na Babila, a cikin ganimar yaƙi, da shekel ɗari biyu na azurfa, da harshen zinariya, a bakin nauyin shekel hamsin, sa’annan na yi ƙyashinsa, na ɗauke su.’ Maimakon Achan ya guji wannan sha’awar, haɗama ta sa ya sato waɗannan kayayyakin kuma ya ɓoye su a tent nasa. Sa’ad da Jehobah ya fallasa laifin Achan ga kowa, sai Joshua ya gaya masa cewa Jehobah zai halaka shi. A wannan ranar, aka jejjefi Achan da iyalinsa har suka mutu. (Josh. 7:11, 21, 24, 25) Za mu iya zama masu haɗama idan ba mu yi hankali ba. Saboda haka, ya kamata mu ‘tsare kanmu daga dukan ƙyashi,’ wato haɗama. (Luk 12:15) Ko da yake a wasu lokatai za mu iya yin tunanin banza kamar na yin lalata, zai dace mu riƙa kame kanmu kuma kada mu bar wannan sha’awar ta mamaye zuciyarmu har ta sa mu aikata zunubi.—Karanta Yaƙub 1:14, 15.
14. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da muka lura cewa muna da halin fahariya da kuma haɗama?
14 Fahariya da haɗama za su iya jawo haɗari. Yin tunani a kan sakamakon aikata laifi zai sa mu mai da hankali don mu riƙa jin muryar Jehobah. (K. Sha 32:29) A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya gaya mana abin da bin tafarki mai kyau ya ƙunsa da albarkar da za mu samu idan muka yi hakan. Ƙari ga haka, ya gaya mana sakamakon bin tafarki marar kyau. Idan zuciyarmu ta soma tunanin yin fahariya da kuma haɗama, ya kamata mu yi hattara kuma mu tuna da sakamakon yin zunubi. Ya kamata mu yi tunanin yadda yin laifi zai iya shafan mu da iyalinmu da abokanmu da kuma dangantakarmu da Jehobah.
KA CI GABA DA YIN ADDU’A GA JEHOBAH
15. Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Yesu game da yin addu’a?
15 Jehobah yana son mu ji daɗin rayuwa. (Zab. 1:1-3) Yana ba mu ja-gorar da muke so a daidai lokacin da muke bukata. (Karanta Ibraniyawa 4:16.) Ko da yake Yesu cikakke ne, ya dogara ga Jehobah kuma ya yi ta addu’a babu fashi. Jehobah ya taimaka wa Yesu kuma ya ja-gorance shi a hanyoyi da yawa. Ya aika mala’iku su kula da shi, ya tanadar masa da ruhu mai tsarki kuma ya yi masa ja-gora sa’ad da yake zaɓan manzanninsa sha biyu. Jehobah ya yi magana daga sama don ya nuna cewa yana goyon bayan Yesu kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17; 17:5; Mar. 1:12, 13; Luk 6:12, 13; Yoh. 12:28) Kamar Yesu, muna bukata mu riƙa yin addu’a ga Allah. (Zab. 62:7, 8; Ibran. 5:7) Addu’a za ta taimaka mana mu kusaci Jehobah kuma mu yi rayuwa a hanyar da za ta ɗaukaka shi.
16. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu ji muryarsa?
16 Ko da yake Jehobah yana ba mu shawara a sauƙaƙe, amma ba ya tilasta wa kowannenmu ya bi ta. Saboda haka, muna bukatar mu roƙe shi ya ba mu ruhu mai tsarki kuma zai ba mu a yalwace. (Karanta Luka 11:10-13.) Don haka, yana da muhimmanci mu ‘yi lura da yadda muke ji.’ (Luk 8:18) Alal misali, zai zama munafunci mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu shawo kan sha’awar yin lalata idan muka ci gaba da kallon batsa ko kuma fina-finan da suke nuna yin lalata. Muna bukatar mu kasance a yanayi ko kuma wuraren da ruhun Jehobah yake, kamar a taron ikilisiya. Bayin Jehobah da yawa sun guji haɗari ta wurin sauraron muryar Jehobah sa’ad da ake yin taro. A sakamako, sun gane cewa suna da wani hali marar kyau kuma sun ƙoƙarta sun daina halin.—Zab. 73:12-17; 143:10.
KA CI GABA DA KASA ƘUNNE GA MURYAR JEHOBAH
17. Me ya sa yake da haɗari mu dogara ga kanmu?
17 Ka yi la’akari da labarin Sarki Dauda na ƙasar Isra’ila. A lokacin da yake matashi, ya yi nasara a kan Goliyat Ba-filisti. A sakamako, Dauda ya zama soja da sarki da mai kāriya da kuma mai yanke wa al’ummar shawara. Amma sa’ad da Dauda ya dogara ga kansa, zuciyarsa ta yaudare shi kuma ya yi zunubi mai tsanani da Bath-sheba, har ma ya shirya a kashe mijinta Uriah. Sa’ad da aka yi wa Dauda horo, ya nuna tawali’u ta wajen amincewa da laifinsa kuma daga baya, ya sake zama abokin Jehobah.—Zab. 51:4, 6, 10, 11.
18. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da sauraron muryar Jehobah?
18 Bari mu bi shawarar da ke 1 Korintiyawa 10:12 kuma kada mu yi garaje. Da yake ba za mu iya ‘shirya tafiyarmu’ ba, za mu iya sauraron murya Jehobah ko kuma na Abokin gabansa, wato Shaiɗan. (Irm. 10:23) Bari mu ci gaba da yin addu’a da bin ja-gorar ruhu mai tsarki da kuma sauraron muryar Jehobah a kowace rana.