Me Ya Sa Ka Tabbata Cewa Kana Bin Addini na Gaskiya?
‘Ku gwada ko mene ne nufin . . . Allah, mai-kyau, abin karɓa, cikakke.’—ROM. 12:2.
1. Mene ne limaman Kiristendam suka yi a lokacin yaƙi?
SHIN Allah yana so Kiristoci na gaskiya su riƙa zuwa yaƙi kuma su kashe mutanen wata ƙasa dabam? Mutane da yawa da suke da’awa cewa su Kiristoci ne sun sha yin hakan shekaru 100 da suka shige. Limaman cocin Katolika sun yi wa rundunan soja addu’a don su yaƙi wasu ’yan Katolika da ke wata ƙasa. Limaman cocin Furotestan ma sun yi hakan. Kisan da aka yi a Yaƙin Duniya na 2 ya nuna sakamakon da ake samu saboda irin wannan rashin imani.
2, 3. Mene ne Shaidun Jehobah suka yi a lokacin Yaƙin Duniya na 2 da kuma bayan haka, kuma me ya sa?
2 Mene ne Shaidun Jehobah suke yi a lokacin yaƙi? Tarihi ya nuna cewa ba su saka hannu a yaƙin da aka yi tsakanin ƙasa da ƙasa ba. Me ya sa? Domin suna bin gurbin Yesu da kuma koyarwarsa ne. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:35) Ƙari ga haka, suna bin ƙa’idodin da ke wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke Korinti.—Karanta 2 Korintiyawa 10:3, 4.
3 Kiristoci na gaskiya sun amince da ja-gorancin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma sun ƙi koyan yaƙi ko kuma saka hannu a yaƙi. Saboda haka, ana tsananta wa Shaidun Jehobah manya da yara, maza da mata. An tura da yawa cikinsu zuwa sansani da kuma kurkuku. Har ma an kashe wasu a lokacin Mulkin Nazi a ƙasar Jamus. Duk da waɗannan tsanantawa da Shaidun Jehobah suka fuskanta a ƙasashen Turai, ba su yi watsi da aikin da aka ba su na yin wa’azin bisharar Mulkin Jehobah ba. Sun yi hakan a duk yanayin da suka sami kansu, wato a kurkuku da sansani da kuma sa’ad da suke gudun hijira.a Shekaru bayan haka, sa’ad da ake kisan kāre dangi a ƙasar Ruwanda a shekara ta 1994, Shaidun Jehobah ba su saka hannu ba. Ƙari ga haka, sun nuna cewa ba ruwansu da zub da jinin da aka yi a ƙasar Yugoslavia ta dā.
4. Ta yaya halin Shaidun Jehobah na ƙin saka hannu a yaƙi ya shafi mutane?
4 Yadda Shaidun Jehobah suka ƙi saka hannu a yaƙi ya sa mutane da yawa a faɗin duniya sun amince cewa suna ƙaunar Allah da kuma maƙwabtansu da gaske. Hakan kuma ya sa mutane sun amince cewa su Kiristoci na gaskiya ne. Duk da haka, akwai wasu fannonin ibadarmu da suka sa mutane da yawa su gaskata cewa Shaidun Jehobah Kiristoci na gaskiya ne.
AIKIN ILIMANTARWA MAFI GIRMA A TARIHI
5. Wane canji ne mabiyan Kristi na farko suka fuskanta?
5 Sa’ad da Yesu ya soma hidimarsa a duniya, ya nuna cewa wa’azi game da Mulkin Allah ne ya fi muhimmanci. Ya zaɓi manzanni 12 don su soma aikin nan da za a yi a faɗin duniya. Daga baya kuma, ya horar da almajirai guda 70. (Luk 6:13; 10:1) Yesu ya shirya su don su yi wa mutane wa’azi, za su fara yi wa Yahudawa. Bayan haka, sai mai zai faru? Almajiran Yesu za su soma wa’azi ga mutanen al’ummai marasa kaciya. Hakika, wannan ba ƙaramin canji ba ne ga waɗannan almajiran Yesu masu ƙwazo!—A. M. 1:8.
6. Mene ne ya sa Bitrus ya fahimta cewa Jehobah ba ya nuna bambanci?
6 Jehobah ya aiki manzo Bitrus zuwa gidan Karniliyus, wani mutumin Al’ummai. Sai Bitrus ya fahimta cewa Allah ba ya nuna bambanci. Ya ba da umurni cewa a yi wa Karniliyus da iyalinsa baftisma. Daga nan ne addinin Kirista ya soma yaɗuwa, yanzu dukan mutane a faɗin duniya za su iya koyan gaskiya kuma su amince da ita. (A. M. 10:9-48) Saboda haka, Bitrus da sauran almajiran Yesu sun yi wa mutanen dukan al’ummai wa’azi.
7, 8. Mene ne ƙungiyar Jehobah ta yi don mutane su ji bishara? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.)
7 A tarihin Shaidun Jehobah na zamani, waɗanda suke ja-gora sun ɗauki wa’azin bishara da kuma koyar da ita da muhimmanci. Ƙari ga haka, sun tsara yadda za a gudanar da wannan aikin a faɗin duniya. A yau, kusan Shaidun Jehobah miliyan takwas ne suke yin iya ƙoƙarinsu don su yaɗa bishara a cikin harsuna sama da 600, kuma wannan adadin yana ci gaba da ƙaruwa! An san Shaidun Jehobah da wa’azi gida-gida da kuma a kan titi. Wani lokaci sukan yi amfani da tebura da ɗan amalanke don nuna littattafai.
8 Ƙungiyar Jehobah ta horar da mafassara sama da 2,900 don su fassara Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Suna yin fassara a sanannun harsuna, har da harsunan da ba a san su sosai ba amma da miliyoyin mutane suke yi. Alal misali, a ƙasar Sifen miliyoyin mutane suna yin yaren Catalan yau da kullum. A kwanan nan musamman, mutane suka soma yin yaren Catalan a biranen Valencia da Alicante da kuma tsibiran Balearic. Shaidun Jehobah suna wallafa littattafai a yaren Catalan, ana yin taro a yaren kuma hakan yana ratsa zukatan mutanen Catalonia.
9, 10. Mene ne yake nuna cewa ƙungiyar Jehobah tana son dukan mutane su koyi gaskiya?
9 Ana wannan aikin fassara da kuma koyar da mutane a wurare da yawa a faɗin duniya. Alal misali, yawancin mutane da ke Meziko suna yaren Sfanisanci, amma akwai wasu yaruka dabam-dabam da mutane suke yi. Yaren Maya ɗaya ne daga cikin waɗannan yarukan. Ofishin reshe da ke ƙasar Meziko ta tura mafassaran yaren Maya zuwa inda ake yaren a ƙasar don su riƙa yin yaren kuma su ji yadda ake yinsa a kullum. Wani misali kuma shi ne yaren Nepali, wanda ɗaya ne cikin yarukan da ake yi a ƙasar Nepal, kuma jama’ar da ke wurin sun fi miliyan 29. Ana yin wasu yaruka 120 a wannan ƙasar, amma mutane fiye da miliyan 10 suna yin yaren Nepali kuma wasu da yawa suna yin yaren ban da ainihin yarensu. Ƙari ga haka, ana wallafa littattafanmu da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a wannan yaren.
10 Ƙungiyar Jehobah ta ɗauki umurnin nan na yin bisharar Mulkin Allah a faɗin duniya da muhimmanci, ana ganin hakan daga yadda ake tallafa wa rukunonin fassara a faɗin duniya. An rarraba miliyoyin warƙoƙi da ƙasidu da mujallu ba tare da farashi ba a kamfen dabam-dabam da aka yi a faɗin duniya. Shaidun Jehobah suna samun kuɗi don gudanar da wannan aikin ta wajen gudummawar da ake bayarwa da son rai. Ta hakan, Shaidun Jehobah suna bin umurnin Yesu da ya ce: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.”—Mat. 10:8.
11, 12. Mene ne wa’azin da Shaidun Jehobah suke yi a faɗin duniya yake tabbatar wa mutane?
11 Shaidun Jehobah suna wa’azi da kuma koyarwa babu fashi kuma sun tabbata cewa suna bin addini na gaskiya. Hakan ya sa suna yin sadaukarwa sosai don su sanar da wannan gaskiyar ga mutanen dukan al’umma da kuma al’ada. Da yawa daga cikinsu sun sauƙaƙa rayuwarsu, sun koyi wani yare da kuma al’ada don su yi wannan wa’azin bishara mai muhimmanci. Wannan wa’azi da kuma koyarwa yana cikin abubuwan da suke tabbatar wa mutane cewa Shaidun Jehobah su ne ainihin mabiyan Yesu Kristi.
12 Shaidun Jehobah suna yin wannan aikin ne don sun tabbata cewa addininsu na gaskiya ne. Wane dalili ne kuma ya sa suka tabbata cewa suna bin addini na gaskiya?—Karanta Romawa 14:17, 18.
ABIN DA YA SA SUKA BA DA GASKIYA
13. Ta yaya Shaidun Jehobah suke kāre ƙungiyar Jehobah daga muguwar ɗabi’a?
13 Za mu iya amfana daga kalaman ’yan’uwa Kiristoci maza da mata da suka tabbata cewa suna bin addini na gaskiya. Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana bauta wa Jehobah ya ce: “Ƙungiyar Jehobah ba ta jinkirin yi wa wanda ya yi laifi horo ko kuma gyara ko da waye ne abin ya shafa kuma hakan yana sa ta kasance da ɗabi’a mai kyau.” Ta yaya ake samun wannan ɗabi’a mai kyau? Ta wajen bin ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma misalin da Yesu da almajiransa suka kafa. Saboda haka, mutane kaɗan ne kawai aka yi wa yankan zumunci a zamaninmu don sun ƙi su bi ƙa’idodin Allah. Yawancin Shaidun Jehobah suna yin rayuwar da ta dace a gaban Allah, kuma hakan ya haɗa da mutanen da a dā suka yi rayuwar da Allah bai amince da ita ba amma kuma suka canja salon rayuwarsu sa’ad da suka koyi gaskiya.—Karanta 1 Korintiyawa 6:9-11.
14. Mene ne mutane da yawa da aka yi musu yankan zumunci suka yi, kuma mene ne sakamakon?
14 Littafi Mai Tsarki ya ba da umurni cewa a yi wa waɗanda suka yi rashin biyayya yankan zumunci. Abin farin ciki shi ne, an sake dawo da waɗanda suka tuba daga miyagun ayyukansu zuwa cikin ikilisiya. (Karanta 2 Korintiyawa 2:6-8.) Da yake Shaidun Jehobah suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don gyara halayensu, hakan ya sa ikilisiya ta kasance da ɗabi’a mai kyau a kowane lokaci. Saboda haka, sun tabbata cewa wannan ita ce ƙungiyar da Jehobah ya amince da ita. Ko da yake coci suna barin mabiyansu su yi abin da suka ga dama, Shaidun Jehobah suna rayuwa bisa ƙa’idodin Jehobah kuma hakan ya sa mutane da yawa sun gaskata cewa Shaidun Jehobah suna bin addini na gaskiya.
15. Me ya tabbatar wa wani ɗan’uwa cewa yana bin addini na gaskiya?
15 Me ya sa waɗanda suka daɗe da zama Shaidun Jehobah suka tabbata cewa suna bin addini na gaskiya? Wani ɗan’uwa da ya ba shekaru 50 baya ya ce: “Tun da nake matashi, na gaskata cewa bangaskiyata ta dangana ga ginshiƙai uku: (1) akwai Allah; (2) kuma shi ne ya hure Littafi Mai Tsarki; da kuma (3) cewa Shaidun Jehobah ne suke yin nufin Jehobah a yau. Yayin da nake nazari cikin waɗannan shekarun, na sha gwada waɗannan ginshiƙai uku don in tabbata cewa suna da tushe. Tabbacin da nake samu a kan kowane ginshiƙin nan yana ƙaruwa kowace shekara, kuma hakan ya ƙarfafa bangaskiyata da tabbatar mini cewa lallai muna bin addini na gaskiya.”
16. Mene ne ya burge wata ’yar’uwa game da gaskiyar?
16 Wata ’yar’uwa mai aure da ke hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah da ke birnin New York ta yi kalami cewa: “Ƙungiyar Jehobah ce kaɗai take sanar da sunan Jehobah. Hakan gaskiya ce domin sunan Jehobah ya bayyana wajen sau 7,000 a cikin Littafi Mai Tsarki! Bayanin da ke 2 Labarbaru 16:9 tana ƙarfafa ni, ayar ta ce: ‘Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.’” Ta daɗa da cewa: “Gaskiyar ta koyar da ni yadda zan kasance da zuciya da ta kamalta a gaban Jehobah don ya yi amfani da ƙarfinsa wajen taimakona. Dangantakata da Jehobah ce ta fi muhimmanci a gare ni kuma na amince da matsayin Yesu na tanadar da ilimi game da Allah da ke ƙarfafa ni.”
17. Wane tabbaci ne wani da a dā bai gaskata cewa akwai Allah ba yake da shi, kuma me ya sa?
17 Wani da a dā bai gaskata cewa akwai Allah ba ya ce: “Halitta ta tabbatar mini cewa Allah yana son ’yan Adam su more rayuwa kuma saboda haka, ba zai ƙyale wahala ta ci gaba har abada ba. Ƙari ga haka, yayin da duniya take ƙara taɓarɓarewa cikin rashin imani, bayin Jehobah suna ƙara kasancewa da bangaskiya da himma da kuma ƙauna. Ruhun Jehobah ne kaɗai zai iya tabbatar da irin wannan yanayi mai ban al’ajabi a zamaninmu.”—Karanta 1 Bitrus 4:1-4.
18. Yaya kake ji game da kalaman da wasu ’yan’uwa biyu suka yi?
18 Wani ɗan’uwa kuma da ya daɗe da zama Mashaidi ya faɗi dalilan da suka sa ya amince da gaskiyar da muke wa’azinta, ya ce: “Nazarin da na yi shekaru da yawa ya tabbatar mini cewa Shaidun Jehobah sun yi ƙoƙari sosai don su koma ga ainihin koyarwar Kiristoci na ƙarni na farko. Na ga haɗin kai da ke tsakanin Shaidun Jehobah don na je wurare dabam-dabam a faɗin duniya. Gaskiyar da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ya sa na kasance da gamsuwa da farin ciki.” Sa’ad da aka tambayi wani ɗan’uwa da ya wuce shekara 60 dalilin da ya sa ya tabbata cewa yana bin addini na gaskiya, ɗan’uwan ya mai da hankali ga yadda Shaidun Jehobah suka ɗauki Yesu, ya ce: “Mun bincika rayuwa da kuma hidimar Yesu kuma mun amince da misalin da ya kafa. Mun yi canje-canje a rayuwarmu don mu kusaci Allah ta wurin Kristi Yesu. Mun fahimta cewa ta wurin hadayar fansar Kristi ne kawai za mu sami ceto. Kuma mun san cewa an ta da shi daga matattu. Mutane da za mu iya tabbata da su sun shaida hakan.”—Karanta 1 Korintiyawa 15:3-8.
ME YA WAJABA MU YI DA GASKIYAR?
19, 20. (a) Wane hakki ne Bulus ya ambata wa ’yan’uwa da ke ikilisiyar Roma? (b) Wane gata ne muke da shi a matsayin Kiristoci?
19 Kiristoci na gaskiya suna ƙaunar maƙwabtansu, shi ya sa ya wajaba mu yi wa maƙwabtanmu wa’azi game da gaskiyar da muka koya. Sa’ad da Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa da ke ikilisiyar Roma, ya ce: “Idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma ba da gaskiya cikin zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira: gama da zuciya mutum ya ke ba da gaskiya zuwa adalci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto.”—Rom. 10:9, 10.
20 A matsayin Shaidun da suka keɓe kansu ga Jehobah, mun tabbata cewa muna bin addini na gaskiya kuma mun san cewa gata ne mu yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah. Yayin da muke yin haka, bari yadda muke koyar da mutane da kuma yadda muke rayuwa ya tabbatar musu cewa muna bin addini na gaskiya.
a Ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 191-198, 448-454.