Ka Tuna da Masu Hidima ta Cikakken Lokaci
“Ba ma fasa tunawa da aikinku na bangaskiya . . . da faman da kuke yi domin ƙauna.”—1 TAS. 1:3, Littafi Mai Tsarki.
1. Ta yaya Bulus ya ɗauki ’yan’uwan da suka yi aiki tuƙuru don yaɗa bishara?
MANZO Bulus ya daraja ’yan’uwan da suka yi aiki tuƙuru don su yaɗa bisharar Mulki. Ya ce: “Ba ma fasa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da faman da kuke yi domin ƙauna, da kuma sa zuciyarku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.” (1 Tas. 1:3) Babu shakka, Jehobah ma yana daraja fama da dukan bayinsa amintattu suke yi domin ƙauna, ko da yaya yanayinsu yake.—Ibran. 6:10.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 ’Yan’uwanmu da yawa a zamanin dā da kuma a yau sun yi sadaukarwa don su bauta wa Jehobah ta wajen yin hidima ta cikakken lokaci. Bari mu yi la’akari da yadda wasu suka yi hidima a ƙarni na farko. Za mu kuma tattauna wasu fasaloli na hidima ta cikakken lokaci a yau domin mu ga yadda za mu daraja ’yan’uwan da suka ba da kansu don su yi wannan hidimar.
KIRISTOCI NA ƘARNI NA FARKO
3, 4. (a) A waɗanne hanyoyi ne wasu ’yan’uwa a ƙarni na farko suka yi wa Jehobah hidima? (b) Ta yaya ’yan’uwa suka biya bukatunsu?
3 Jim kaɗan bayan Yesu ya yi baftisma, ya soma wa’azin da za a yi a dukan duniya. (Luk 3:21-23; 4:14, 15, 43) Bayan Yesu ya mutu, manzanninsa sun yi ja-gora wajen yaɗa bishara sosai. (A. M. 5:42; 6:7) Wasu Kiristoci kamar Filibus sun yi hidima a Falasɗinu. (A. M. 8:5, 40; 21:8) Bulus da kuma wasu sun yi hidima a wasu ƙasashe. (A. M. 13:2-4; 14:26; 2 Kor. 1:19) Wasu kamar Silwanisu, wato Sila da Markus da Luka sun yi hidima a matsayin marubuta. (1 Bit. 5:12) Kiristoci mata ma sun yi hidima tare da waɗannan amintattun ’yan’uwa. (A. M. 18:26; Rom. 16:1, 2) Abubuwan da suka shaida ya taimaka wajen sa labaran da ke Nassosin Helenanci na Kirista su yi daɗi sosai, kuma hakan ya nuna cewa Jehobah yana daraja bayinsa.
4 Ta yaya ’yan’uwan da suke hidima ta cikakken lokaci a zamanin dā suka biya bukatunsu? A wasu lokuta, ’yan’uwa Kiristoci sun gayyace su cin abinci, sun ba su masauki ko kuma sun taimaka musu a wasu hanyoyi, amma ba su suke roƙa a taimaka musu ba. (1 Kor. 9:11-15) Wasu ’yan’uwa da kuma ikilisiyoyi suna ba da taimako da yardar rai. (Karanta Ayyukan Manzanni 16:14, 15; Filibiyawa 4:15-18.) Bulus da kuma wasu abokan aikinsa sun yi aiki na ɗan lokaci don su biya bukatunsu.
MASU HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI A ZAMANINMU
5. Mene ne wasu ma’aurata suka faɗa game da hidima ta cikakken lokaci da suka yi?
5 A yau ma, ’yan’uwa da yawa suna ba da kansu don yin hidima ta cikakken lokaci dabam-dabam. (Ka duba akwatin nan “Hidima ta Cikakken Lokaci Dabam-dabam.”) Ta yaya suke ji don zaɓin da suka yi? Idan ka sami zarafi, za ka iya yi musu wannan tambayar, kuma babu shakka, za ka yi farin ciki sakamakon hakan. Ka yi la’akari da wannan misali: Wani ɗan’uwa da ya taɓa hidimar majagaba na kullum da hidimar majagaba ta musamman da wa’azi a ƙasashen waje da kuma hidima a Bethel a wata ƙasa ya ce: “Na san cewa yin hidima ta cikakken lokaci ce zaɓi mafi kyau da na taɓa yi. Sa’ad da nake ɗan shekara 18, ban san ko in je jami’a ko in yi aikin kuɗi na cikakken lokaci ko kuma in yi hidimar majagaba ba. Na san cewa Jehobah ba ya yasar da mutanen da suka yi hidima ta cikakken lokaci. Na sami damar yin amfani da baiwar da Jehobah ya ba ni sosai kuma da hakan ba zai yiwu ba da na biɗi wasu maƙasudai na duniyar nan.” Matarsa ta ce: “Kowace hidimar da na yi ta taimaka mini in ƙware. Mun gani sarai cewa Jehobah yana kāre mu da kuma yi mana ja-gora a kai a kai. Da hakan ba zai taɓa yiwu ba da a ce mun biɗi rayuwar jin daɗi. Ina godiya ga Jehobah kullum domin muna hidima ta cikakken lokaci.” Shin kai ma za ka so ka shaida irin wannan farin cikin?
6. Yaya Jehobah yake ɗaukan hidimar da muke yi?
6 Hakika, yanayin wasu ba zai sa su yi hidima ta cikakken lokaci a yanzu ba. Muna da tabbaci cewa Jehobah yana daraja hidimar da suke yi da dukan zuciyarsu. Ka yi la’akari da ’yan’uwan da Bulus ya ambaci sunansu a littafin Filimon 1-3, har da dukan ’yan’uwan da ke ikilisiyar Kolosi. (Karanta.) Bulus ya ji daɗin hidimar da suka yi, Jehobah ma ya yi hakan. Hakazalika, Ubanmu na sama yana jin daɗin hidimar da kake yi. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya tallafa wa waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci a yau?
YADDA ZA KA TAIMAKA WA MAJAGABA
7, 8. Wane irin aiki ne majagaba suke yi, kuma ta yaya wasu a cikin ikilisiya za su iya taimaka wa majagaba?
7 Majagaba masu ƙwazo suna kamar Kiristocin ƙarni na farko domin sun ƙarfafa ikilisiyoyi sosai. Da yawa cikinsu suna yin wa’azi na sa’o’i 70 a kowane wata. Ta yaya za ka iya taimaka musu?
8 Wata majagaba ta ce: “Ana gani kamar majagaba suna da ƙarfi sosai domin suna wa’azi kullum. Amma duk da haka, suna bukatar ƙarfafa.” (Rom. 1:11, 12) Wata ’yar’uwa kuma da ta yi hidimar majagaba shekaru da yawa ta yi furuci na gaba game da majagaban da ke ikilisiyarsu: “Suna aiki tuƙuru kuma ba sa karaya. Majagaba suna farin ciki sa’ad da wani ya ɗauke su a mota yayin da suke wa’azi ko ya gayyace su cin abinci ko ya ba su kuɗin mota ko na biyan wata bukata. Hakan yana nuna cewa kana kula da su.”
9, 10. Mene ne wasu ’yan’uwa suka yi don su taimaki majagaba a ikilisiyarsu?
9 Shin za ka so ka taimaka wa majagaba a hidima? Wani majagaba mai suna Bobbi ya ce: “Muna so ’yan’uwa su riƙa zuwa tallafa mana a wa’azi a cikin mako, ba a ƙarshen mako kaɗai ba.” Wani majagaba da ke ikilisiyar su Bobbi ya ce: “Samun ɗan’uwan da zai fita wa’azi tare da mu da tsakar rana yana da wuya sosai.” Wata ’yar’uwa da take hidima a Bethel da ke Brooklyn ta yi furuci na gaba game da lokacin da take hidimar majagaba. Ta ce: “Wata ’yar’uwa da take da mota ta ce, ‘A duk lokacin da kika rasa wanda za ki fita wa’azi tare da shi, ki kira ni domin mu je tare.’ ’Yar’uwar ta taimaka mini sosai don in ci gaba da hidimar majagaba.” Kuma wata mai suna Shari ta ce: “Bayan an kammala wa’azi, majagaba marasa aure suna yawan kaɗaitawa. Za ku iya ziyartar ’yan’uwa maza ko mata marasa aure zuwa ibada ta iyalinku a kai a kai. Yin wasu ayyuka kuma tare da su zai ƙarfafa su.”
10 Wata ’yar’uwa da ta yi hidimar majagaba kusan shekara 50 ta tuna sa’ad da ita da wasu ’yan’uwa mata suke hidimar majagaba tare. Ta ce: “Dattawan ikilisiyarmu sukan ziyarci majagaba bayan ’yan watanni. Sukan tambaye mu game da lafiyarmu da aikin da kuma su bincika ko akwai wani abin da ke damunmu. Sun damu da mu da gaske. Suna ziyartarmu don su ga ko da akwai taimakon da muke bukata.” Hakan zai iya tuna maka da yadda Bulus ya yi godiya sosai don hidimomin da wani magidanci mai suna Onisifurus ya yi masa.—2 Tim. 1:15-18.
11. Mene ne hidimar majagaba na musamman ya ƙunsa?
11 Wasu suna da majagaba na musamman da ke hidima a ikilisiyarsu kuma hakan babban gata ne. Waɗannan majagaban suna wa’azi na sa’o’i 130 a wata kuma suna wasu ayyuka a cikin ikilisiya. Domin suna waɗannan ayyukan, ba sa samun lokacin yin aikin da za su sami kuɗi. Ofishin reshe yana ba su alawus a kowane wata domin su mai da hankali ga hidimarsu.
12. Ta yaya dattawa da kuma wasu za su iya taimaka wa majagaba na musamman?
12 A waɗanne hanyoyi ne za mu iya tallafa wa majagaba na musamman? Wani dattijo a ofishin reshe da ke yawan sha’ani da majagaba na musamman da yawa ya ce: “Dattawa suna bukatar su riƙa tattaunawa da su, su san yanayinsu kuma su san yadda za su iya taimaka musu. Wasu masu shela suna tunani cewa ofishin reshe yana kula da dukan bukatun majagaba domin ana ba su alawus, duk da haka, ’yan’uwa a yankin za su iya tallafa musu a hanyoyi da yawa.” Majagaba na musamman ma suna bukatar ’yan’uwan da za su riƙa fita wa’azi tare da su. Za ka iya taimaka musu a wannan hanyar.
YADDA ZA KA TAIMAKA WA MASU KULA DA DA’IRA
13, 14. (a) Me ya kamata mu tuna game da masu kula da da’ira? (b) Mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa masu kula da da’ira?
13 Masu kula da da’ira da matansu suna da imani sosai kuma suna ƙarfafa mu. Duk da haka, suna bukatar ƙarfafa kuma suna son ’yan’uwan su riƙa fita wa’azi tare da su. Ƙari ga haka, suna farin ciki sa’ad da ’yan’uwa suka yi ɗan nishaɗi tare da su. Amma idan suna rashin lafiya kuma fa, wataƙila suna bukatar fiɗa ko kuma jinya? Suna farin ciki sosai sa’ad da ’yan’uwa a yankin sun biya bukatunsu kuma sun nuna cewa sun kula da su. Babu shakka, Luka, “ƙaunataccen likitan” da ya rubuta littafin Ayyukan Manzanni ya kula da Bulus da kuma abokan aikinsa sosai kuma hakan ya sa su matuƙar farin ciki.—Kol. 4:14; A. M. 20:5–21:18.
14 Masu kula da da’ira da matansu suna bukatar abokai na kud da kud. Wani mai kula da da’ira ya ce: “Kamar dai abokaina sun san lokacin da nake bukatar ƙarfafa. Suna yi mini tambayoyin da ke sa in furta abin da ke damu na. Yadda suke saurara sosai yana taimaka mini ƙwarai.” Masu kula da da’ira da matansu suna godiya sosai sa’ad da ’yan’uwa suka nuna cewa suna kula da su.
TALLAFA WA MASU HIDIMA A BETHEL
15, 16. Waɗanne ayyuka ne ’yan’uwan da ke hidima a Bethel da kuma Majami’ar Manyan Taro suke yi, kuma yaya za mu iya tallafa musu?
15 ’Yan’uwan da ke hidima a Bethel da kuma Majami’un Manyan Taro suna aiki mai muhimmanci don tallafa wa wa’azin bishara da ake yi a ƙasarsu. Idan kuna da masu hidima a Bethel a ikilisiyarku ko da’irarku, ta yaya za ku nuna cewa kuna daraja su?
16 A lokaci na farko da waɗannan ’yan’uwan suka zo Bethel, suna iya yin kewar gida domin ba sa tare da iyalinsu da abokansu. Suna farin ciki sosai idan ’yan’uwa a Bethel da kuma a ikilisiya sun zama abokansu! (Mar. 10:29, 30) Aikin da suke yi a Bethel yana ba su damar halartar taro da kuma yin wa’azi kowane mako. Amma a wasu lokuta, waɗannan ’yan’uwan suna samun wasu ƙarin ayyukan da suke yi a Bethel. Idan ’yan’uwa a ikilisiyoyi suka fahimci hakan kuma suka nuna godiya don aikin da suke yi, kowa zai amfana.—Karanta 1 Tasalonikawa 2:9.
TAIMAKA WA MASU HIDIMA A WATA ƘASA
17, 18. Waɗanne ayyuka ne ’yan’uwan da ke hidima a wata ƙasa suke yi?
17 Waɗanda suke hidima a wata ƙasa suna iya fuskantar ƙalubale saboda bambancin abinci da yare da al’ada da kuma yanayin ƙasar. Me ya sa suka yarda su yi irin wannan canji duk da waɗannan kaluɓalen da za su fuskanta?
18 Wasu masu wa’azi a ƙasashen waje ne kuma ainihin aikin da suke yi shi ne yin wa’azi a yankin da mutane da yawa za su amfana daga iliminsu. Ofishin reshe yana tanadar musu da masauki da kuma alawus da za su biya bukatunsu da shi. Wasu kuma da ke hidima a wata ƙasa suna aiki a ofishin reshe ko kuma suna taimaka don a gina ofisoshin reshe da ofisoshin fassara da Majami’un Manyan Taro ko kuma Majami’un Mulki. Ana tanadar musu da abinci da masauki da kuma wasu abubuwa. Waɗannan ’yan’uwan suna kamar masu hidima a Bethel domin suna halartar taro da yin wa’azi a kai a kai a yankinsu. Hakika, suna taimaka mana a hanyoyi da yawa.
19. Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwan da suka zo hidima a ƙasarmu?
19 Ta yaya za ka iya taimaka wa masu hidima ta cikakken lokaci da suka zo yin hidima a ƙasarku? Ku san cewa ba su saba da wasu irin abincin da ake ci a yankinku ba. Zai dace ku yi la’akari da haka sa’ad da kuka gayyace su cin abinci a gidanku. Za ku iya tambayarsu irin abincin da suke so. Ku riƙa haƙuri da su yayin da suke koyon yarenku da al’adunku. Zai iya ɗaukan lokaci kafin su fahimci dukan abin da kuka ce, amma za ku iya koya musu yadda ake furta kalmomi a yaren. Waɗannan ’yan’uwan suna so su koyi yaren da kuma al’adun ƙasar!
20. Ta yaya za ku iya taimaka wa masu hidima ta cikakken lokaci da kuma iyayensu?
20 Masu hidima ta cikakken lokaci suna tsufa kuma wasu suna da iyaye tsofaffi a gida. Yawancin iyaye tsofaffi da Shaidu ne suna so yaransu su ci gaba da hidima ta cikakken lokaci. (3 Yoh. 4) Hakika, masu hidima ta cikakke lokaci suna iya ƙoƙarinsu sa’ad da iyayensu suke bukatar taimako kuma suna yin hakan a kai a kai. Amma, ya kamata ’yan’uwan da ke can gida su riƙa taimaka wa waɗannan tsofaffin. Ku tuna cewa masu hidima ta cikakken lokaci suna aiki tuƙuru wajen yaɗa bishara, kuma wannan ne aikin da ya fi muhimmanci a duniya a yau. (Mat. 28:19, 20) Zai dace ku taimaka wa iyayen masu hidima ta cikakken lokaci.
21. Ta yaya masu hidima ta cikakken lokaci suke ji game da taimako da ƙarfafa da ake ba su?
21 Ba neman wadata ba ne yake sa masu hidima ta cikakken lokaci suke wannan hidimar, amma don su yi hidima ga Jehobah ne kuma su taimaka wa mutane. Suna godiya sosai idan kuka taimaka musu. Wata ’yar’uwa da ke hidima a wata ƙasa ta ce: “Ko da gajeriyar wasiƙa ka aika musu, hakan yana nuna cewa ka damu da su kuma kana son hidimar da suke yi.”
22. Mene ne ra’ayinka game da masu hidima ta cikakken lokaci?
22 Babu shakka, Jehobah yana saka wa masu hidima ta cikakken lokaci kuma wannan ne hidima mafi muhimmanci a yau? Hidimarsu tana ɗauke da ƙalubale, tana sa wadar zuci da kuma sa a koyi halaye masu kyau da za su taimaka musu a sabuwar duniya. Bari dukanmu mu riƙa tunawa da masu hidima ta cikakken lokaci don ‘aikin bangaskiyarsu da . . . ƙaunarsu.’—1 Tas. 1:3.