Kada Ka Yi Wasa da Gatan Yin Aiki Tare da Jehobah!
“Mu abokan aiki na Allah ne.”—1 KOR. 3:9.
1. Yaya Jehobah yake ɗaukan aiki, kuma mene ne ya yi game da hakan?
JEHOBAH ma’aikaci ne da ke jin daɗin aikinsa. (Zab. 135:6; Yoh. 5:17) Jehobah yana son mala’iku da ’yan Adam su yi farin ciki shi ya sa ya ba su aiki mai ƙayatarwa. Alal misali, ya ba wa Ɗansa na fari damar yin aiki tare da shi sa’ad da yake halittan abubuwa. (Karanta Kolosiyawa 1:15, 16.) Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya kasance tare da Allah a sama kuma shi “gwanin mai-aiki ne.”—Mis. 8:30.
2. Mene ne ya nuna cewa mala’iku suna da aiki mai muhimmanci kuma mai gamsarwa?
2 Daga farko zuwa ƙarshe, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai da suka nuna cewa Jehobah yana ba wa mala’ikunsa aiki a koyaushe. Bayan da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi kuma aka kore su daga cikin Aljanna, a gabashin gonar Adnin Allah “ya sanya Cherubim, da takobi mai-harshen wuta mai-juyawa a kowace fuska, domin a tsare hanyar itace na rai.” (Far. 3:24) Kuma Ru’ya ta Yohanna 22:6 ta bayyana cewa Jehobah “ya aike mala’ikansa ya bayyana wa bayinsa al’amuran da za su faru ba da jinkiri ba.”
’YAN ADAM KUMA FA?
3. Yaya Yesu ya bi misalin Ubansa sa’ad da yake duniya?
3 Sa’ad da Yesu yake duniya a matsayin kamili, ya yi aikin da Jehobah ya ba shi da farin ciki. Yesu ya bi misalin Ubansa kuma ya ba almajiransa aiki mai muhimmanci. Ya sa su marmarin yin aikin sa’ad da ya ce: “Hakika, hakika, ina ce maku, Wanda ya ba da gaskiya gareni, ayyukan da na ke yi shi kuma zai yi; ayyuka kuma waɗanda sun ɗara waɗannan zai yi; domin ina tafiya wurin Uban.” (Yoh. 14:12) Yesu ya nuna musu cewa wannan aiki na gaggawa ne, shi ya sa ya ce: “Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa’ad da ba mai iya aiki.”—Yoh. 9:4, Littafi Mai Tsarki.
4-6. (a) Me ya sa muke godiya cewa Nuhu da Musa sun yi aikin da Jehobah ya ba su? (b) Waɗanne abubuwa ne aka cim ma daga ayyukan da Allah ya ba wa ’yan Adam?
4 Kafin Yesu ya zo duniya, an ba ’yan Adam aiki mai gamsarwa. Adamu da Hawwa’u ba su yi aikin da Allah ya ba su ba, amma wasu sun cika aikin da aka ba su. (Far. 1:28) An ba Nuhu takamaiman umurni a kan yadda zai gina jirgi don ya ceci rayukan mutane a lokacin babbar Rigyawa. Ya yi duk abin da Jehobah ya umurce shi. Nuhu ya bi umurnin Jehobah da kyau shi ya sa muke da rai a yau!—Far. 6:14-16, 22; 2 Bit. 2:5.
5 An ba Musa takamaiman umurni a kan yadda za a gina mazauni da kuma tsara firistoci, kuma ya bi umurnin da kyau. (Fit. 39:32; 40:12-16) Muna amfana a yau don ya bi umurnin da aka ba shi da kyau. Ta yaya? Manzo Bulus ya bayyana cewa waɗannan fannonin Dokar suna nuni ga “kyawawan abubuwan da ke gaba.”—Ibran. 9:1-5, 9; 10:1, LMT.
6 Allah yana ba bayinsa ayyuka dabam-dabam yayin da yake cika nufinsa. Duk da haka, aikin da suka yi ya ɗaukaka Jehobah kuma ya amfani waɗanda suka yi biyayya. Hakan ya shafi abubuwa da Yesu ya cim ma kafin ya zo duniya da kuma sa’ad da yake duniya. (Yoh. 4:34; 17:4) Hakazalika, aikin da aka ba mu a yau yana ɗaukaka Jehobah. (Mat. 5:16; karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Me ya sa muka ce hakan?
RA’AYIN DA YA DACE GAME DA AIKI
7, 8. (a) Ka kwatanta aikin da Kiristoci suke yi a yau. (b) Me ya kamata mu yi idan Jehobah ya umurce mu?
7 Abin farin ciki ne cewa Jehobah ya ba ’yan Adam ajizai gatan zama abokan aikinsa. (1 Kor. 3:9) Waɗanda suke gina Majami’un Mulki da Majami’un Taro da rassan ofishi suna yin aikin gini kamar yadda Nuhu da Musa suka yi. Ko da aikinka ya shafi gyara Majami’ar Mulki ko kuma gina hedkwatarmu da ke Warwick, a jihar New York, ka ɗauki wannan gatan da muhimmanci. (Ka duba hoton da ke shafi na 23.) Hidima mai tsarki ce. Amma, dukan Kiristoci suna yin wa’azi kuma wannan aikin yana kama da aikin gini. Aikin nan yana ɗaukaka Jehobah kuma yana amfanar mutane masu biyayya. (A. M. 13:47-49) Ƙungiyar Allah tana ba da ja-gora a kan yadda za a yi wannan aikin da kyau. A wani lokaci, hakan zai sa a canja mana aiki.
8 Bayin Jehobah masu aminci suna marmarin bin ja-gora da ake bayarwa ta ƙungiyarsa. (Karanta Ibraniyawa 13:7, 17.) Wataƙila ba za mu fahimci dukan dalilan da suka sa aka canja tsarin hidimarmu ba. Duk da haka, mun san cewa za mu amfana idan muka ba da haɗin kai ga Jehobah a duk wani canjin da ya ga damar yi.
9. Wane misali mai kyau ne game da hidima dattawa suke kafawa a ikilisiya?
9 Dattawa suna nuna cewa suna marmarin cim ma nufin Jehobah ta hanyar da suke ja-gora a cikin ikilisiya. (2 Kor. 1:24; 1 Tas. 5:12, 13) Suna aiki da ƙwazo kuma suna bin sababbin tsare-tsare da ƙungiyar Jehobah ke bayarwa. Suna kuma saurin daidaita yanayinsu da duk wani sabon tsari game da wa’azin Mulkin Allah. Ko da yake da farko wasu sun yi jinkirin tsara yin wa’azi ta tarho da kuma a tashan jirgin ruwa ko kuma wa’azi a inda akwai jama’a, amma sa’ad da suka gwada, sun sami sakamako mai kyau. Alal misali, wasu majagaba guda huɗu a Jamus sun soma fita wa’azi a yankin da ake kasuwanci da aka daɗe ba a yi wa’azi a wurin ba. Michael ya ce: “Mun yi shekaru ba mu yi irin wannan wa’azin ba, saboda haka mun ɗan yi jinkiri. Jehobah ya san cewa muna jinkiri kuma ya sa mun ji daɗin yin wa’azi da safen. Mun yi farin ciki cewa mun bi umurni da ke cikin Hidimarmu ta Mulki kuma mun dogara ga Jehobah!” Kana marmarin saka hannu a sababbin hanyoyi yin wa’azi da ake yi a yankinku?
10. Wane canji ne ƙungiyar Jehobah ta yi a shekarun baya?
10 A wasu lokatai ana yin canji a yadda ake gudanar da ayyuka a ƙungiyar Jehobah. A shekarun baya, an haɗa wasu rassan ofishi wuri ɗaya. Hakan yana bukatar wasu ’yan’uwa da ke aiki a waɗannan wuraren su amince da yanayin, amma sun ga amfanin yin hakan nan da nan. (M. Wa. 7:8) Abin farin ciki ne cewa waɗannan bayin Jehobah sun taimaka a tarihin mutanensa na zamani!
11-13. Wane ƙalubale ne wasu suka fuskanta saboda canje-canje da aka yi a ƙungiyar Jehobah?
11 Muna iya koyan darasi mai kyau daga waɗanda suka yi hidima a rassan ofishi da aka haɗa. Wasu sun yi shekaru da yawa suna hidima a waɗannan rassan ofishi. An gaya wa wasu ma’aurata da suka yi hidima a ƙaramin Bethel da ke Amirka ta Tsakiya su koma hidima a Bethel da ke ƙasar Mexico da ya ninka nasu sau 30. Rogelio ya ce: “Barin iyali da abokai ba shi da sauƙi.” Juan, wani ɗan’uwa da aka ce ya koma Mexico ya ce: “Kamar mun sake soma rayuwa ne, wajibi ne mu sake yin abokai. Muna bukatar mu saba da al’adu da kuma ra’ayoyinsu.”
12 Masu hidima a Bethel da ke ƙasashen Turai da aka ce su koma hidima a reshen ofishi da ke Jamus ma sun fuskanci irin wannan ƙalubale. Duk wanda ya san yadda zama a Siwizalan yake da daɗi zai fahimci cewa barin wannan wuri mai tsaunuka masu kyaun gani bai da sauƙi. Kuma waɗanda suka ƙaura daga ƙaramin Bethel da ke ƙasar Austria sun yi kewar irin rayuwar da suka yi a wurin.
13 Waɗanda suke ƙaura zuwa wata ƙasa suna bukata su saba da sabon wurin zama da yin aiki tare da ’yan’uwa da ba su taɓa ganinsu ba, kuma wataƙila su yi wani aiki dabam. Hakan yana nufin cewa za su riƙa halartan taro a wata ikilisiya kuma su yi wa’azi a yankin da ba su saba da shi ba, a wani lokaci ma za su bukaci su koyi wani yare. Yin irin waɗannan canje-canje bai da sauƙi. Duk da haka, ’yan’uwa da yawa masu hidima a Bethel sun rungumi waɗannan canje-canjen. Me ya sa suka yi hakan?
14, 15. (a) Ta yaya ’yan’uwa da yawa suka nuna cewa suna marmarin yin aiki tare da Jehobah a kowane irin aikin da aka ba su? (b) Ta yaya suka kafa mana misali mai kyau?
14 Grethel ta ce: “Na yarda na koma wata ƙasa domin in nuna wa Jehobah cewa ina ƙaunarsa fiye da wata ƙasa ko gini ko kuma gata.” Dayska ta ce: “Na amince in ƙaura sa’ad da na tuna cewa Jehobah ne ya ce in yi hakan.” André da Gabriela sun yarda da hakan, sun ce: “Mun ga cewa hakan zai ba mu zarafin saka bautar Jehobah gaba da ra’ayoyinmu.” Sun gaskata cewa ya fi kyau su bi umurnin da ƙungiyar Jehobah take bayarwa maimakon su ƙi umurnin.
15 Domin an haɗa wasu rassan ofishi wuri ɗaya, an tura wasu ’yan’uwa da ke a Bethel su yi hidimar majagaba. Wannan ya shafi ’yan’uwa da dama masu hidima a Bethel sa’ad da aka haɗa rassan ofishi na ƙasashen Denmark da Norway da Sweden a waje ɗaya kuma aka kira shi reshen ofishi da ke Scandinavia. Florian da Anja suna cikin waɗanda aka tura hidimar majagaba, sun ce: “A ganinmu, sabon hidimarmu zai ba mu damar koyan abubuwa da dama. Yin hidimar Jehobah a kowane yanayi gata ne a gare mu. A gaskiya, Jehobah ya albarkace mu sosai!” Ko da yake waɗannan canje-canjen ba za su shafi yawancinmu ba, duk da haka, ya kamata mu yi koyi da waɗannan ’yan’uwan ta wajen saka al’amuran Mulki kan gaba a rayuwarmu, ko ba haka ba? (Isha. 6:8) Jehobah yana albarkar waɗanda suke marmarin yin aiki tare da shi a kowane yanayi.
KA CI GABA DA MORE GATAN YIN AIKI TARE DA JEHOBAH!
16. (a) Mene ne Galatiyawa 6:4 ta shawarce mu mu yi? (b) Wane babban gata ne za mu iya samu?
16 Da yake mu ajizai ne, mukan gwada kanmu da wasu, amma kalmar Allah ta ce mu mai da hankali ga abubuwan da za mu iya yi. (Karanta Galatiyawa 6:4.) Yawancinmu ba mu da wani matsayi a cikin ƙungiyar Jehobah. Ƙari ga haka, ba dukanmu ba ne za mu iya zama majagaba ko masu wa’azi a ƙasashen waje ko kuma masu hidima a Bethel. Babu shakka, waɗannan gata ne masu kyau! Amma ya kamata mu tuna cewa yin wa’azi ne babban gatan da muke da shi. Ta hakan, muna aiki tare da Jehobah. Ya kamata mu ɗauki wannan gata da muhimmanci!
17. Wane yanayi ne muke fuskanta a duniyar Shaiɗan, amma me ya sa bai kamata mu karaya ba?
17 Da yake muna rayuwa a duniyar Shaiɗan, ba za mu iya bauta wa Jehobah yadda muke so ba. Kula da iyali ko rashin lafiya ko kuma wani yanayi dabam zai iya hana ka yin wasu abubuwa a bautar Jehobah. Amma kada ka karaya. Kada ka yi wasa da gatan yin aiki tare da Allah ta wajen sanar da mutane game da sunansa da Mulkinsa a kowane lokaci. Abin da ya fi muhimmanci shi ne kana yin iya ƙoƙarinka a bautarka ga Jehobah kuma kana addu’a cewa ya albarkaci ’yan’uwanka da suke da damar yin hidima fiye da kai. Ka tuna cewa duk wanda yake yabon sunan Jehobah yana da mutunci a gabansa!
18. Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu yi watsi da su, kuma me ya sa?
18 Jehobah ya ba mu gatan kasancewa abokan aikinsa duk da kasawarmu da ajizancinmu. Babu shakka, muna ɗaukan wannan gatan da muhimmanci sosai a wannan kwanaki na ƙarshe! Saboda haka, bari mu ƙudiri niyyar yin watsi da duk abubuwan da muke sha’awa da yake mun san cewa a sabuwar duniya, Jehobah zai ba mu damar samun “hakikanin rai,” wato rai na har abada cikin kwanciyar hankali da salama.—1 Tim. 6:18, 19.
19. Mene ne Jehobah ya yi mana alkawarinsa a nan gaba?
19 Da yake muna gab da shiga sabuwar duniya, ka tuna da abin da Musa ya gaya wa Isra’ilawa sa’ad da suke gab da shiga Ƙasar Alkawari, ya ce: “Ubangiji Allahnka kuma za ya albarkace ka cikin dukan aikin hannunka.” (K. Sha 30:9) Bayan Armageddon, waɗanda suka duƙufa a yin aiki tare da Allah za su gāji wannan duniyar da Allah ya yi musu alkawarinta. A lokacin, za a ba mu wani sabon aiki, wato aikin mai da duniya aljanna mai ban sha’awa!