Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Kasance da Tsarki?
“Ku zama masu-tsarki.”—LEV. 11:45.
1. Ta yaya littafin Levitikus zai taimaka mana?
AN AMBACI tsarki a cikin littafin Levitikus fiye da kowane littafi na Littafi Mai Tsarki. Da yake ana bukatar bayin Jehobah su kasance da irin wannan halin, bincika da kuma fahimtar littafin Levitikus zai taimaka mana mu kasance da tsarki.
2. Yaya aka tsara littafin Levitikus?
2 Annabi Musa ne ya rubuta littafin Levitikus kuma littafin yana cikin “kowane nassi” da yake da amfani wajen koyarwa. (2 Tim. 3:16) A asalin harshen da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sunan Jehobah ya bayyana aƙalla sau goma a cikin kowace surar littafin. Fahimtar littafin Levitikus da kyau zai taimaka mana mu guji yin wani abin da zai ɓata sunan Allah. (Lev. 22:32) Sau da yawa, littafin ya yi amfani da furucin nan “ni ne Ubangiji” kuma hakan yana tuna mana cewa ya kamata mu yi wa Allah biyayya. A wannan talifin da kuma na gaba, za mu koyi darussa masu amfani daga littafin Levitikus da kyauta ce daga wurin Allah kuma hakan zai taimaka mana mu yi wa Allah tsarkakkiyar ibada.
KASANCEWA DA TSARKI FARILLA CE
3, 4. Mene ne tsarkake Haruna da ’ya’yansa yake wakilta? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
3 Karanta Levitikus 8:5, 6. Jehobah ya naɗa Haruna a matsayin babban firist na Isra’ila, ’ya’yansa maza kuma su yi hidimar firistoci a madadin al’ummar. Haruna yana wakiltar Yesu Kristi kuma ’ya’yansa suna wakiltar mabiyan Yesu da aka shafa da ruhu mai tsarki. Saboda haka, tsarkakewar Haruna yana wakiltar tsarkakewar Yesu ne? A’a, Yesu bai da zunubi kuma shi “marar-aibi” ne, don haka, ba ya bukatar tsarkakewa. (Ibran. 7:26; 9:14) Amma bayan da aka tsarkake Haruna, ya wakilci Yesu wanda yake da tsarki da kuma adalci. To, mene ne tsarkakewar da aka yi wa ’ya’yan Haruna yake wakilta?
4 Tsarkakewar ’ya’yan Haruna yana wakiltar tsarkakewar waɗanda aka zaɓa su yi hidimar firist a sama. Baftismar da aka yi wa waɗannan shafaffun yana da alaƙa ne da tsarkakewar ’ya’yan Haruna? A’a, domin baftisma ba ya wanke zunubi, maimakon haka, yana nuna ne cewa mutum ya ba da kansa gaba ɗaya don ya yi nufin Jehobah Allah. Ana tsarkake shafaffu “ta wurin kalman,” kuma wannan yana nufin cewa za su riƙa bin koyarwar Kristi da zuciya ɗaya. (Afis. 5:25-27) Ta hakan ne ake tsarkake da kuma tsabtacce su. “Waɗansu tumaki” kuma fa?—Yoh. 10:16.
5. Me ya sa za a iya ce an tsarkake waɗansu tumaki ta wurin Kalmar Allah?
5 ’Ya’yan Haruna ba sa wakiltar “taro mai-girma” na waɗansu tumaki. (R. Yoh. 7:9) Shin an tsarkake da kuma tsabtacce waɗannan mutane da suka yi baftisma da Kalmar Allah ne? Hakika! Sa’ad da waɗanda suke da begen zama a duniya suka karanta abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da amfanin fansar Yesu, suna ba da gaskiya ga abin da ke Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, suna “bauta . . . dare da rana.” (R. Yoh. 7:13-15) Yayin da shafaffu da kuma waɗansu tumaki suna “al’amura” masu kyau, za su riƙa amfana daga tsarkakewar. (1 Bit. 2:12) Jehobah zai yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga yadda shafaffu da kuma waɗansu tumaki suke tsabta da kuma haɗin kai yayin da suke sauraron Makiyayinsu, Yesu kuma suna yin biyayya da shi!
6. Wane irin bincike ne ya kamata mu yi wa kanmu?
6 Bayin Jehobah a yau za su amfana sosai daga yadda aka bukaci firistocin Isra’ila su riƙa kasancewa da tsabta. Waɗanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su sukan lura da tsabtar wuraren da muke bauta da kuma yadda adonmu yake da kyau da kuma tsabta. Duk da haka, tsabtar firistoci ya taimaka mana mu fahimta cewa ya kamata dukan waɗanda suke so su bauta wa Jehobah su kasance da “zuciya mai-tsarki.” (Karanta Zabura 24:3, 4; Isha. 2:2, 3.) Wajibi ne mu kasance da tsabta a hankalinmu da zuciyarmu da kuma a jiki don mu bauta wa Allah da tsarki. Hakan yana bukata mu riƙa bincika kanmu a kai a kai, bayan haka ne wasu za su ga cewa suna bukata su yi wasu canje-canje sosai don su kasance da tsarki. (2 Kor. 13:5) Alal misali, ya kamata wanda ya yi baftisma da yake kallon hotunan batsa ya tambayi kansa, ‘Shin wannan halin yana sa in kasance da tsarki?’ Bayan haka, zai dace ya nemi taimako don ya daina irin wannan banzan halin.—Yaƙ. 5:14.
KU KASANCE DA TSARKI TA WAJEN YIN BIYAYYA
7. Bisa ga littafin Levitikus 8:22-24, wane misali ne Yesu ya kafa?
7 A lokacin da aka soma yin hidima ta firist, an sa jinin rago a kunnuwan dama na Haruna Babban Firist da kuma ’ya’yansa maza, da manyan yatsun hannunsu na dama da kuma manyan yatsunsu na kafa ta dama. (Karanta Levitikus 8:22-24.) Yin amfani da jini a wannan hanyar tana nuna cewa firistocin za su yi iya ƙoƙarinsu wajen yin hidimarsu. Hakazalika, Yesu Babban Firist ya kafa wa shafaffu da kuma waɗansu tumaki misali mai kyau. Ya bi ja-gorar Allah. Yesu ya yi nufin Jehobah da hannayensa, sawayensa kuma sun bi tafarki mai tsarki.—Yoh. 4:31-34.
8. Mene ne ya wajaba dukan bayin Jehobah su yi?
8 Wajibi ne shafaffun Kiristoci da kuma waɗansu tumaki su bi tafarkin aminci na Yesu Babban Firist. Ya kamata dukan bayin Jehobah su bi ja-gorar Kalmar Allah kuma kada su guji yin abin da zai saɓa wa ruhu mai tsarki. (Afis. 4:30) Wajibi ne su “bi miƙaƙƙun hanyoyi” da sawayensu.—Ibran. 12:13, Littafi Mai Tsarki.
9. Mene ne wasu ’yan’uwa uku da suka yi aiki da mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suka faɗa, kuma ta yaya furucinsu zai taimaka maka ka ci gaba da kasancewa da tsarki?
9 Mene ne wasu ’yan’uwa uku da suke da begen yin rayuwa a duniya da suke aiki da wasu cikin membobin Hukuma da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suka ce? Ɗaya daga cikinsu ya ce: “Yin aiki tare da su babban gata ne, amma cuɗanya da na yi da su ya nuna cewa waɗannan ’yan’uwan ajizai ne ko da yake an shafa su da ruhu mai tsarki. Duk da haka, a shekarun nan da nake aiki tare da su, burina shi ne in riƙa yin biyayya ga waɗanda suke ja-gora.” Ɗan’uwa na biyu ya ce: “Nassosi kamar su 2 Korintiyawa 10:5, game da yin ‘biyayya ga Kristi,’ ya taimaka mini in riƙa yin biyayya da kuma ba da haɗin kai ga waɗanda suke ja-gora. Ina yin wannan biyayyar da zuciya ɗaya.” Ɗan’uwa na ukun ya ce: “Son abin da Jehobah yake so da ƙin abin da ya tsana da bin ja-gorarsa da kuma yin abin da ke faranta masa rai ya bukaci biyayya da ƙungiyarsa da kuma waɗanda yake amfani da su don cim ma nufinsa ga duniya.” Wannan Ɗan’uwan ya tuna da misalin Ɗan’uwa Nathan Knorr, mamba na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Akwai lokacin da ɗan’uwa Knorr, ya amince da darussan da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 1925 mai jigo, “Birth of the Nation” (Haihuwar Al’umma), ko da yake wasu sun ƙi su amince da waɗannan darussan. Irin wannan biyayya ya burge wannan ɗan’uwan sosai. Yin bimbini a kan furucin waɗannan ’yan’uwa uku zai taimaka maka ka kasance da tsarki ta wurin yin biyayya.
KA BI DOKAR ALLAH GAME DA JINI DA ZUCIYA ƊAYA
10. Me ya sa yake da muhimmanci mu bi dokar Allah game da jini?
10 Karanta littafin Levitikus 17:10. Jehobah ya umurci Isra’ilawa kada su “ci kowane irin jini.” Ana bukatar Kiristoci su guji cin jini, wato jinin dabba ko kuma na mutum. (A. M. 15:28, 29) Abin ban tsoro ne mu yi tunanin yin wani abu da zai sa Allah ya “yi gāba” da mu kuma ya datse mu daga cikin ikilisiyarsa. Muna ƙaunarsa kuma muna so mu yi masa biyayya. Ko muna fuskantar abin da zai sa ranmu cikin hadari, mun kuɗiri niyyar cewa ba za mu bi ra’ayin mutanen da ba su san Jehobah ba balle su yi masa biyayya. Hakika, ko da yake za a yi mana ba’a don ba ma karɓan ƙarin jini, mun fi so mu yi wa Allah biyayya. (Yahu. 17, 18) Wane ra’ayi game da wannan batun ne zai taimaka mana mu “lura,” wato mu ƙudurta cewa ba za mu ci jini ba kuma ba za mu karɓi ƙarin jini ba?—K. Sha 12:23.
11. Me ya sa za mu ce Ranar Kafara ba al’ada ba ce kawai?
11 Yadda babban firist yake yin amfani da jini a Ranar Kafara da ake yi kowace shekara ya sa mu fahimci ra’ayin Allah game da jini. An yi amfani da jini kawai don wani abu mai muhimmanci, wato don neman gafara daga Jehobah a madadin mutane da suka yi zunubi. Saboda haka, za a yayyafa jinin bijimi da na akuya kusa da kuma gaban sandukin alkawari. (Lev. 16:14, 15, 19) Hakan yana sa Jehobah ya gafarta wa Isra’ilawa zunubansu. Ƙari ga haka, Jehobah ya ba da doka cewa idan mutum ya yanka dabba don abinci, sai ya zubar da kuma rufe jinin da ƙasa, don “ran dukan nama yana cikin jininsa.” (Lev. 17:11-14) Shin wannan al’ada ce da babu amfani? A’a. Yin amfani da jini a Ranar Kafara da kuma umurnin a zubar da jini a ƙasa ya jitu da dokar da Jehobah ya ba wa Nuhu da zuriyarsa game da jini. (Far. 9:3-6) Jehobah ya gaya musu kada su ci jini kamar abinci. Wane darasi ne Kiristoci za su koya daga wannan?
12. Ta yaya wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa ya nuna cewa jini da gafara suna da alaƙa?
12 A lokacin da manzo Bulus yake rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa game da ikon tsarkakewa da jini yake da shi, ya ce: Kusan “dukan abu, bisa ga shari’a, da jini a kan tsarkake shi, kuma in ba zubawar jini babu gafara.” (Ibran. 9:22) Ko da yake amfanin hadayar dabbobi na ɗan lokaci ne, hakan ya tuna wa Isra’ilawa cewa su masu zunubi ne kuma suna bukatar hadayar da zai kawar da zunubansu gaba ɗaya. Hakika, Dokar “ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba, ba ainihin siffarsu ba.” (Ibran. 10:1-4) Ta yaya zai yiwu a gafarta zunubai?
13. Yaya kake ji game da sanin cewa Yesu ya miƙa amfanin hadayarsa ga Jehobah?
13 Karanta Afisawa 1:7. Yadda Yesu Kristi “ya ba da kansa kuma dominmu,” da yardar rai yana da ma’ana sosai ga waɗanda suke ƙaunarsa da kuma Ubansa. (Gal. 2:20) Amma dai, abin da Yesu ya yi bayan tashinsa daga matattu ne ya yantar da mu kuma ya sa a gafarta zunubanmu. Yesu ya cika abin da ake yi a Ranar Kafara bisa ga Doka. A ranar, babban firist yakan ɗebi jinin dabbobin da aka kawo hadaya ya kai wuri Mafi Tsarki a mazauni, bayan haka sai ya shiga da jinin cikin haikalin Sulemanu, kuma ya miƙa hadayar kamar yana gaban Allah. (Lev. 16:11-15) Hakazalika, Yesu ya je sama da abin da ya cim ma ta wurin ba da jininsa kuma ya miƙa shi ga Jehobah. (Ibran. 9:6, 7, 11-14, 24-28) Muna godiya sosai cewa an gafarta mana zunubanmu kuma muna da lamiri mai kyau don mun ba da gaskiya ga Yesu saboda jinin da ya zubar a madadinmu!
14, 15. Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci da kuma bi dokar Jehobah game da jini?
14 Shin ka fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ba mu umurni cewa kada mu ci “kowane irin jini”? (Lev. 17:10) Ka fahimci dalilin da ya sa Allah ya ɗauki jini da tsarki? Domin jini da rai ɗaya ne a gabansa. (Far. 9:4) Shin ka yarda cewa ya kamata mu amince da ra’ayin Allah game da jini kuma mu bi umurninsa cewa kada mu ci ko karɓi jini? Za mu sami salama da Allah ne kawai idan mun ba da gaskiya ga fansar Yesu kuma mun amince cewa jini yana da tsarki a gaban Mahaliccinmu.—Kol. 1:19, 20.
15 Za mu iya samun kanmu a yanayin da za a bukaci ƙarin jini. Ko kuma wani cikin iyalinmu ko aboki zai iya samun kansa a wani yanayi da za ce yana bukatar ƙarin jini. A wannan mawuyacin lokacin, za a bukaci tsai da shawara game da hanyoyin jinya da abubuwan da aka samo daga jini. Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi bincike sosai kuma mu tsai da shawara kafin jinyar gaggawa. Yin hakan tare da yin addu’a ga Jehobah za su taimaka mana mu yi tsayin daka kuma mu guji ƙarya dokar Jehobah game da jini. Hakika, ba ma son mu ɓata ran Jehobah ta yin abin da ya haramta a cikin Kalmarsa! Likitoci da kuma wasu da suka amince da ƙarin jini suna ƙarfafa mutane su ba da gudummawar jini don ceton rayuka. Amma, mutanen Jehobah masu tsarki sun san cewa Mahalicci ne yake da ikon ba da umurni game da yadda za a yi amfani da jini. A gabansa, “kowane irin jini” yana da tsarki. Wajibi ne mu kuɗiri niyyar bin dokarsa game da jini. Ya dace mu nuna godiya don ikon fansar jinin Yesu ta yadda muke aikatawa. Ta jinin Yesu ne kawai za mu iya samun rai na har abada da kuma gafarar zunubanmu.—Yoh. 3:16.
ABIN DA YA SA JEHOBAH YA CE MU KASANCE DA TSARKI
16. Me ya sa ya kamata mu kasance da tsarki?
16 A lokacin da Allah yake ceton Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar, ya gaya musu: “Ni ne Ubangiji wanda ya kawo ku daga cikin ƙasar Masar, domin in zama Allahnku: za ku zama masu-tsarki fa, gama ni mai-tsarki ne.” (Lev. 11:45) An bukaci Isra’ilawa su kasance da tsarki don Jehobah mai tsarki ne. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, wajibi ne mu kasance da tsarki. Littafin Levitikus ya bayyana hakan dalla-dalla.
17. Mene ne ra’ayinka yanzu game da littafin Levitikus?
17 Babu shakka, mun amfana sosai da muka tattauna wasu sassan littafin Levitikus. Hakika, wannan nazarin ya sa mun ƙara godiya don wannan littafin Levitikus da aka hure. Hakika, yin bimbini a kan wasu bayyanai da ke littafin Levitikus ya ƙara sa mun fahimci dalilan da suka sa ya kamata mu kasance da tsarki. Duk da haka, waɗanne abubuwa ne za mu ƙara koya daga wannan sashen Littafi Mai Tsarki? Mene ne kuma za mu iya koya game da bauta wa Jehobah da tsarki? Za mu tattauna waɗannan abubuwan a talifi na gaba.