Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 9/1 p. 16
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Gabatarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 9/1 p. 16

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Shin yadda rayuwar nan za ta kasance ke nan?

Wani tsoho da jariri suna kallon nesa

Kana gani muna cika saurin mutuwa ne?

Ka taɓa yin tunani cewa ma’anar rayuwa kawai ita ce yin wasa da aiki da aure da samun yara da kuma tsufa? (Ayuba 14:1, 2) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane masu hikima ma sun yi irin wannan tunanin.—Karanta Mai-Wa’azi 2:11.

Shin rayuwa tana da ma’ana kuwa? Ya kamata mu fara yin wannan tambayar, Yaya rayuwa ta soma? Yadda Allah ya halicci kwakwalwarmu da kuma jikinmu ya sa mutane da yawa sun gaskata cewa akwai Mahalicci mai hikima. (Karanta Zabura 139:14.) Idan haka ne, yana da manufa mai kyau na halittar mu. Sanin wannan manufar za ta taimaka mana mu yi rayuwa mai ma’ana.

Me ya sa aka halicci mutum?

Allah ya albarkaci iyayenmu na farko kuma ya ba su aiki mai kyau. Manufarsa ita ce su cika duniya da ’ya’ya, su sa ta zama aljanna kuma su rayu har abada a cikinta.—Karanta Farawa 1:28, 31.

An jinkirta manufar Allah sa’ad da iyayenmu suka taka dokarsa. Amma Allah bai fid da rai a kanmu ba kuma bai canja manufarsa ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah yana kan aiki tukuru don ya ceci mutane masu aminci kuma ya aiwatar da manufarsa ga duniya. Saboda haka, Allah yana so ka ji daɗin rayuwa yadda ya nufa tun asali! (Karanta Zabura 37:29.) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai sa ka koyi yadda za ka amfana daga nufin Allah.

Don karin bayani, ka duba babi na 3 a wannan littafin, Shaidun Jehobah ne suka wallafa

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba