Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 2 pp. 5-9
  • Yadda Rashin Gaskiya Zai Iya Shafan Ka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Rashin Gaskiya Zai Iya Shafan Ka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • RASHIN GASKIYA YAKAN ƁATA DANGANTAKA
  • RASHIN GASKIYA YANA SA WASU MA SU YI RASHIN GASKIYA
  • Amfanin Zama Mai Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Zama Masu Gaskiya a Kowane Abu
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 2 pp. 5-9
Mata biyu suna tattaunawa da juna

Yadda Rashin Gaskiya Zai Iya Shafan Ka

“A yawancin lokuta, ana iya magance manya-manyan matsaloli ta wajen yin rashin gaskiya.”​—⁠In ji Samantha a Afirka ta Kudu.

Ka yarda da wannan furucin? Kamar Samantha, dukanmu mun taɓa fuskantar manya-manyan matsaloli. Matakin da muka ɗauka sa’ad da aka matsa mana mu yi rashin gaskiya zai nuna ko mu masu gaskiya ne ko a’a. Alal misali, idan a kullum muna ƙoƙari mu kāre kanmu, babu shakka, za mu iya yin ƙarya don mu cim ma hakan. Kuma za mu sami mummunan sakamako idan aka gano cewa ƙarya muka yi. Ka yi la’akari da abubuwan da ke gaba.

RASHIN GASKIYA YAKAN ƁATA DANGANTAKA

Mutane sukan zama abokai bayan sun yarda da junansu. Idan mutane biyu suka yarda da juna, dangantakarsu za ta yi danƙo. Amma hakan ba ya faruwa farat ɗaya. Mutane suna amincewa da juna ne idan suna yawan kasancewa tare kuma suna tattaunawa a sake babu son kai. Amma, yin rashin gaskiya sau ɗaya tak zai iya ragargaje wannan dangantakar. Kuma da zarar an daina yarda da juna, zai iya zama da wuya a sake yarda da juna.

Shin wani abokinka ya taɓa cin amanarka? Yaya ka ji sa’ad da hakan ya faru? Babu shakka, ranka ya ɓace sosai. Ba laifi ba ne idan ka yi fushi domin rashin gaskiya yana ɓata abokantaka.

RASHIN GASKIYA YANA SA WASU MA SU YI RASHIN GASKIYA

Wani bincike da farfesan ilimin tattalin arziki mai suna Robert Innes da ke Jami’ar Kalifoniya ya yi, ya nuna cewa “mutane sukan yi rashin gaskiya domin wasu sun yi musu rashin gaskiya.” Hakazalika, rashin gaskiya yana kamar ƙwayoyin cuta masu yaɗuwa. Idan ka ci gaba da abota da marar gaskiya, babu shakka, kai ma za ka bi halinsa.

Ta yaya za ka guji yin rashin gaskiya? Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka. Don Allah ka bincika wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da ke gaba.

Ire-iren Rashin Gaskiya

Ƙarya

Wani mutum ya cire zoben aurensa

MECE CE ƘARYA? Faɗin abin da ba daidai ba ga wani da ya kamata ya san gaskiya. Yin ƙarya ya ƙunshi canja magana don a ruɗi wani ko ƙin ba da cikakken bayani don a yaudari wani ko kuma ƙara gishiri a magana don a cim ma wani mugun buri.

ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: “Mashiririci abin ƙyama ne ga Ubangiji: Amma asirinsa yana tare da masu-adalci.” (Misalai 3:32) “Ku riƙa faɗi wa junanku da makwabtanku gaskiya, kuna kawar da ƙarya.”​—Afisawa 4:25.

Tsegumi

Wasu maza biyu suna rada yayin da wani yake shigowa cikin dakin da suke

MENE NE TSEGUMI? Yin ƙarya da maƙirci don a ɓata sunan wani.

ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: “Don ba itace wuta ta kan mutu: Wurin da babu mai-tsegumi kuma, husuma ta kan kwanta.” (Misalai 26:20) “Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.”​—Misalai 16:28, Littafi Mai Tsarki.

Zamba

Wani mutum ya nuna agogon hannu da ya boye cikin aljuhunsa

MECE CE ZAMBA? Ruɗin mutum don a saci kuɗinsa ko kayansa.

ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: “Kada ku zalunci [zambaci, NW ] ɗan ƙodago wanda yake matalauci.” (Kubawar Shari’a 24:​14, 15, LMT) “Wanda ya zalunci fakirai ya jawo ma Mahaliccinsa zargi: amma wanda ya nuna jinƙai ga masu-mayata yana girmama shi.”​—Misalai 14:31.

Sata

Wani ya saci walat daga jaka

MECE CE SATA? Ɗaukan kayan mutum ba tare da izininsa ba.

ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: “Mai yin sata kada ya ƙara yin sata: amma gwamma ya yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da yake da kyau, domin shi kasance da abin da za shi ɗiba shi bayar ga wanda ya rasa.” (Afisawa 4:28) “Kada ku yaudaru . . . ɓarayi, da masu-ƙyashi, da masu-maye, da masu-alfasha, da masu-ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.”​—1 Korintiyawa 6:9, 10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba