Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 6 p. 16
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah yana amsa dukan addu’o’i kuwa?
  • Shin dole ne mu zauna ko durƙusa ko haɗa hannunmu ko kuma tsaya sa’ad da muke addu’a?
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Allah Zai Saurari Addu’o’ina Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 6 p. 16
Wata mata tana addu’a

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Allah yana amsa dukan addu’o’i kuwa?

SHIN ZA KA CE YANA AMSA ADDU’O’IN . . .

  • Kowa

  • Wasu mutane

  • Ba ya amsa addu’a

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Ubangiji yana kusa da dukan . . . waɗanda suke kira gareshi da gaskiya.”​—Zabura 145:18.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Allah ba ya jin addu’o’in mutanen da ba sa masa biyayya. (Ishaya 1:15) Amma, za su iya ‘daidaita al’amari’ ta wajen canja salon rayuwarsu.​—Ishaya 1:​18, Littafi Mai Tsarki.

  • Idan muna so Allah ya amsa addu’armu, dole ne ta jitu da nufinsa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.​—1 Yohanna 5:⁠14.

Shin dole ne mu zauna ko durƙusa ko haɗa hannunmu ko kuma tsaya sa’ad da muke addu’a?

WASU SUN CE dole ne. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

Akwai misalan mutanen da Allah ya amsa addu’o’insu yayin da suka “zauna” ko “tashi” ko sunkuyar da “kansu” ko kuma “durƙusa.” (1 Labarbaru 17:16; 2 Labarbaru 30:27; Ezra 10:1; Ayyukan Manzanni 9:40) Zai iya amsa addu’armu a kowane irin yanayi.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Allah yana sauraron masu tawali’u.​—Zabura 138:6.

  • Kana iya yin addu’a a kowane yare ko kuma a cikin zuciyarka.​—2 Labarbaru 6:​32, 33; Nehemiya 2:​1-6.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 17 na littafin nan, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba