Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 4 p. 16
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka daina alhini?
  • Shin za mu taɓa daina yin alhini kuwa?
  • Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Maza da Suke Yawan Damuwa
    Karin Batutuwa
  • Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ta Yaya Salamar Kristi Za Ta Yi Mulki A Cikin Zukatanmu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 4 p. 16
Wata iyali na cikin Aljanna

A Mulkin Allah, mutane ‘za su faranta zuciyarsu cikin yalwar salama.’​—Zabura 37:11

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka daina alhini?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Kuna zuba dukan alhininku [a wurin Allah], domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsaki ya gaya mana cewa Allah zai iya taimaka mana mu magance yawan alhini.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Idan ka yi addu’a, za ka sami “salamar Allah” da za ta sa ka daina damuwa.​—Filibiyawa 4:​6, 7, Littafi Mai Tsarki.

  • Ƙari ga haka, karanta Kalmar Allah za ta taimaka maka ka jimre matsaloli.​—Matta 11:​28-30.

Shin za mu taɓa daina yin alhini kuwa?

Wasu sun yi imani cewa . . .wajibi ne mu yi alhini a matsayinmu na ’yan Adam, wasu kuma sun gaskata cewa mutum zai daina alhini ne bayan ya mutu. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Allah zai cire abubuwan da ke sa mu damuwa. “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • A Mulkin Allah, mutane za su yi rayuwa cikin kwanciyar hankali da kuma salama.​—Ishaya 32:18.

  • Ba za mu tuna da abubuwan da ke sa mu damuwa ko baƙin ciki ba.​—Ishaya 65:17.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 3 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba