Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w17 Yuni p. 21
  • “Mai-Albarka Ce Hikimarki”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Mai-Albarka Ce Hikimarki”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Abigail Da Dauda
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ta Nuna Basira
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ta Yi Amfani da Hankalinta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Mata Da Suka Faranta Wa Jehovah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
w17 Yuni p. 21
Abigail

“Mai-Albarka Ce Hikimarki”

DAUDA ya yi wannan maganar sa’ad da yake yaba ma wata mata da ya haɗu da ita a kan hanya. Kuma sunan matar Abigail, amma me ya sa Dauda ya yi wannan kalaman kuma mene ne za mu iya koya daga misalin wannan matar?

A lokacin da Dauda yake gudu don Sarki Saul yana neman ya kashe shi ne ya haɗu da wannan matar. Abigail matar Nabal ce kuma shi mutum ne mai arziki sosai, ban da haka ma, suna zama a kudancin Yahudiya. Dauda da mutanensa suna nan kamar “gānuwa” ce da ke kāre bayin Nabal da garkensa. Don hakan, Dauda ya tura bayinsa su je wajen Nabal don su roƙe shi ya ba su ‘ko mene ne’ da yake da shi wato ko abinci ne. (1 Sam. 25:​8, 15, 16) Abin da Dauda ya roƙa bai fi ƙarfin Nabal ba don sun taimaka masa sosai.

Amma Nabal da sunansa yake nufin “wauta” ko wawa, ya yi abu daidai da sunansa. Ya ƙi ya ba da abin da Dauda ya roƙe shi kuma ya zage bayin Dauda. Don haka, Dauda ya tsai da shawarar kashe shi da kuma iyalinsa.​—1 Sam. 25:​2-13, 21, 22.

Abigail ta ɗauki mataki sa’ad da ta ji abin da Dauda yake son ya yi musu. Da ladabi ta roƙi Dauda kada ya yi abin da yake son yi, don kada ya ɓata dangantakarsa da Jehobah. Ban da haka ma, ta kai wa Dauda wanda zai zama sarki a nan gaba da kuma mutanensa abinci da yawa. Dauda ya gode mata kuma ya san cewa Jehobah ya yi amfani da ita don ya hana shi yin kisa. Dauda ya ce wa Abigail: “Mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.”​—1 Sam. 25:​18, 19, 23-35.

Babu shakka, ba za mu so mu zama kamar Nabal ba wanda ba ya nuna godiya don abubuwan da mutane suke masa. Ƙari ga haka, idan muka lura cewa masifa tana nan tafe muna bukatar mu guje mata. Hakika, mu ma za mu iya roƙon Jehobah kamar yadda marubucin wannan Zabura ya yi da ya ce: “Ka koya mani shari’a mai-kyau da sani kuma.”​—Zab. 119:66.

Wasu sukan lura da halinmu mai kyau. Kuma ko da sun faɗa ko ba su yi hakan ba, suna iya ji kamar Dauda da ya ce: “Mai-albarka ce hikimarki.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba