Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 1 pp. 6-8
  • Littafi Mai Tsarki Sanannen Littafi Ne Mai Fadin Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Sanannen Littafi Ne Mai Fadin Gaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILIN DA YA SA ZAI DACE KA AMINCE DA LITTAFI MAI TSARKI
  • Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mutanen Allah Suna Fitowa Daga Babila
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Za Ka Iya Amincewa da Littafi Mai Tsarki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 1 pp. 6-8

Littafi Mai Tsarki Sanannen Littafi Ne Mai Faɗin Gaskiya

Tun ba yau ba, mutane da yawa daga wurare dabam-dabam sun yarda cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. A yau, miliyoyin mutane suna bin koyarwarsa. Duk da haka, wasu suna ganin bai da amfani a gare mu ko kuma tatsuniyoyi ne kawai ke cikinsa. Mene ne naka ra’ayin? Kana ganin abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

DALILIN DA YA SA ZAI DACE KA AMINCE DA LITTAFI MAI TSARKI

Ta yaya za ka san ko abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne? Ga wani misali: A ce kana da wani abokin da ya daɗe yana faɗa maka gaskiya, za ka yi shakka idan ya gaya maka wani abu? Shin, an san Littafi Mai Tsarki a matsayin littafin da ke ɗauke da gaskiya? Ga wasu misalai.

Marubutansa Sun Faɗi Gaskiya

Hoton hannun marubuci

Marubutan Littafi Mai Tsarki sun faɗi gaskiyar abin da suka sani, kuma ba su ɓoye kurakuransu ba. Alal misali, annabi Yunana ya rubuta labari game da rashin biyayyar da ya yi. (Yona 1:​1-3) Kuma a ƙarshen labarin, ya rubuta yadda Allah ya yi masa horo. Bai ma ambata cewa ya tuba kuma ya zama annabin kirki don a daraja shi ba. (Yona 4:​1, 4, 10, 11) Yadda marubutan Littafi Mai Tsarki suka rubuta ainihin abubuwan da suka faru ya nuna cewa suna son gaskiya sosai.

Shawarar da Ke Ciki Tana da Amfani

Ana samun shawarwari masu kyau a cikin Littafi Mai Tsarki kuwa? Ƙwarai. Alal misali, ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da abin da zai sa mu zauna lafiya da mutane. Ya ce: “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu.” (Matiyu 7:12) “Amsawa a hankali takan kwantar da fushi, amma yin magana da zafi tana tā da fushi.” (Karin Magana 15:1) Shawarar da ke Littafi Mai Tsarki tana da amfani a yau kamar yadda take a lokacin da aka rubuta ta.

Tarihin da Ke Ciki Gaskiya Ne

Hoton shebur da kasa

Da yawa daga cikin kayan tarihin da aka tono sun tabbatar da wanzuwar mutane da wurare da kuma aukuwar abubuwan da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ku lura da yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗi gaskiya a kan wani batun da mutane da yawa ba za su damu da shi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce a zamanin Nehemiya, mutanen Taya da suke zama a Urushalima sukan je su “kawo kifi da kuma kaya iri-iri” don su sayar.​—Nehemiya 13:16.

Akwai wani abin da ya nuna cewa wannan maganar gaskiya ce? Hakika. Masu binciken kayan tarihi na ƙarƙashin ƙasa sun tono wasu kayan mutanen Taya a ƙasar Isra’ila, kuma hakan ya nuna cewa mutanen Taya da Isra’ila ta dā sun yi kasuwanci tare. Ban da haka ma, an tono ƙasusuwan kifin Tekun Meditareniya a Urushalima, kuma waɗanda suka tono ƙasusuwan suna ganin ’yan kasuwa ne suka kawo kifin. Sa’ad da wani masanin kayan tarihi ya ga ƙasusuwan, sai ya ce: “Abin da aka rubuta a Neh[emiya] 13:16 game da yadda mutanen Taya suke zuwa Urushalima su sayar da kifi gaskiya ne.”

Yana faɗin Gaskiya a Batun Kimiyya

Hoton duniya, da ya nuna cewa babu kome da ke rike ta

Littafi Mai Tsarki littafi ne da aka rubuta game da Allah da kuma abubuwan da suka faru a dā. Amma a duk lokacin da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan kimiyya, ba ya kuskure. Ga wani misali.

Wajen shekaru 3,500 da suka shige, an rubuta a Littafi Mai Tsarki cewa an “rataya duniya babu kome a ƙarƙashinta.” (Ayuba 26:7) Hakan ya sha bambam da ƙagen da mutane suka yi cewa a kan ruwa ko wani katon kunkuru ne aka ajiye duniya. Wajen shekaru 1,100 bayan da aka rubuta littafin Ayuba, mutane sun ƙi su yarda cewa ba a ɗora duniya a kan wani abu ba. Sai a shekara ta 1687 ne Isaac Newton ya gano cewa ƙarfin maganaɗisu ne yake riƙe duniya, ba a ɗora ta a kan wani abu ba. Wannan binciken ya tabbatar da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa fiye da shekaru 3,000 kafin lokacin da Isaac Newton ya gano hakan!

Annabcin da Ke Littafi Mai Tsarki Suna Cika

Hoton katangar Babila da kofarta a bude

Annabcin da ke Littafi Mai Tsarki suna cika kuwa? Ga misali: Ishaya ya yi annabci cewa za a hallaka Babila.

Annabci: A ƙarni na takwas kafin haihuwar Yesu, wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Ishaya ya ce za a hallaka Babila. Ishaya ya yi wannan annabcin tun kafin Babila ta zama babban birni, kuma ya ce a ƙarshe za ta zama kango. (Ishaya 13:​17-20) Har ma Ishaya ya ambata sunan mutumin da zai ci birnin da yaƙi. Ya ce Sayirus ne sunansa kuma zai “busar da” rafuffukan birnin kafin ya ci birnin da yaƙi. Ƙari ga haka, ya ce Babiloniyawa za su bar ƙofar birninsu a buɗe.​—Ishaya 44:27–45:1.

Yadda Annabcin Ya Cika: Wajen shekaru 200 bayan Ishaya ya yi wannan annabcin, wani sarkin Fasiya ya kai wa Babila hari. Sunan sarkin Sayirus ne. Birnin Babila yana da kogin da ya kewaye shi kuma ya bi ta cikinsa. Ana kiran kogin, Kogin Yufiretis. Da yake sarkin ya san cewa birnin na da tsaro sosai, sai ya sa sojojinsa su yi wa kogin wata hanya dabam. Sa’ad da ruwan kogin ya ragu, sai Sayirus da sojojinsa suka haye kogin da ƙafa. Abin mamaki, Babiloniyawa sun bar ƙofar birnin da ke fuskantar kogin a buɗe! Sojojin Sayirus sun shiga birnin ta ƙofar kuma suka ci Babila da yaƙi.

Amma ga wani abu kuma da aka ce zai faru da Babila. An ce za ta zama kango. Ɗarurruwan shekaru bayan da aka ci ta da yaƙi, mutane sun ci gaba da zama a wurin. Amma yanzu, Babila ta zama kango, kuma kangonta da ke kusa da Bagadaza a ƙasar Iraƙi ya tabbatar da cewa annabcin da aka yi game da ita ya cika. Babu shakka za mu iya yarda da abin da ke Littafi Mai Tsarki ko da yana magana ne game da abin da zai faru a gaba.

SANANNEN LITTAFI MAI FAƊIN GASKIYA

Misalan da muka gani a baya, kaɗan ne kawai daga cikin misalai da dama da ya sa mutane suka amince da Littafi Mai Tsarki a matsayin “Kalmar Allah.”​—1 Tasalonikawa 2:13.

Amma waɗanne batutuwan da ke Littafi Mai Tsarki ne gaskiya? Za su amfane ka? Za a tattauna wasu daga cikin batutuwan nan a wannan mujallar. Za mu soma da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da mawallafinsa, wato Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba