Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/10 p. 7
  • Yadda Za Ka Koya wa Sababbi Yin Wa’azi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Koya wa Sababbi Yin Wa’azi
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Koyar da Sababbi
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Ku Koya Musu Su Rika Bauta wa Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Ka Zama Abokin Wa’azi Mai Taimako
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ku Yi Koyi da Masu Shela da Suka Fi Ku Ƙwarewa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 5/10 p. 7

Yadda Za Ka Koya wa Sababbi Yin Wa’azi

1. Yaya ka ji a rana na farko da ka fita yin wa’azi?

1 Ka tuna rana na farko da ka fita yin wa’azi na gida zuwa gida? Wataƙila, gabanka ya faɗi sosai. Idan kana aiki ne tare da mai yin nazari da kai ko kuma wani mai shela, babu shakka ka yi farin cikin samun taimakonsa. Yanzu da ka riga ka ƙware a matsayin mai hidima, kana da hakkin koya wa sababbi yin wa’azi.

2. Menene ya kamata sababbin masu shela su koya?

2 Sababbin masu shela suna bukatan su koyi yadda ake soma tattaunawa da maigida, yin amfani da Littafi Mai Tsarki a ƙofa, komawa ziyara, somawa da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya kamata su kuma koyi hanyoyin yin wa’azi dabam-dabam, kamar yin wa’azi a titi da kuma wuraren sana’a. Za ka iya taimaka musu su samu ƙaruwa a waɗannan hanyoyin ta misalinka da kuma shawarwarinka.

3. Ta yaya za mu iya taimaka wa wasu ta misalinmu?

3 Ka Koyar ta Misali: Yesu ya nuna wa almajiransa yadda za su yi wa’azi. (Luk. 8:1; 1 Bit. 2:21) Idan ka yi shirin yin aiki tare da sabon mai shela, ka shirya gabatarwa da mai shelan zai iya koya, wataƙila ta yin amfani da samfurin da ke cikin littattafanmu. Sai ka yi wa’azi a ƙofa ɗaya ko biyu don mai shelan ya ji abin da za ka ce. Kafin ku isa wani ƙofa, kana iya tambayar mai shelan abin da ya lura da shi game da amfanin gabatarwarka. Hakan zai taimaka masa ya ga muhimmancin yin aiki tare da wasu a hidima kuma zai sa ya kasance masa da sauƙi ya karɓi duk wata shawarar da za ka ba shi bayan ya yi gabatarwansa.

4. Ta yaya za mu iya taimaka wa sabon mai shela bayan mun saurari gabatarwarsa?

4 Ka Ba da Shawarwari: Yesu ya kuma ba almajiransa umurni game da yadda za su yi wa’azi. (Mat. 10:5-14) Za ka iya taimaka wa sabon mai shela a wannan hanyar. Idan yana yin wa’azi, ka saurara sosai. Bayan kun bar ƙofar, kada ka yi jinkirin yaba masa sosai, ko da ka lura da wani sashe na gabatarwarsa da ke bukatan gyara. Kafin ka ba shi shawara, kana iya bari ka gani ko ya samu ci gaba a wannan sashen a ƙofa ta gaba. Wataƙila ya ɗan tsorata ne. Ka kuma tuna cewa, dukan masu shela ba su da iyawa iri ɗaya, kuma akwai hanya mai kyau fiye da ɗaya na yin wani abu.—1 Kor. 12:4-7.

5. Menene za mu iya cewa sa’ad da muke ba da shawara?

5 A wasu lokatai, sabon mai shela zai nemi shawara daga wurinka. Amma idan bai yi hakan ba, ka tambaye shi. Ta yaya za ka yi hakan cikin hikima? Wasu masu shela da suka ƙware sukan yi wannan tambayar, “In ba ka wata shawara?” ko, “Ya ka ga gabatarwar nan?” Wata hanya kuma ita ce, “Sa’ad da nike sabon mai shela, yana yi mini wuya in . . . , amma abin da ya taimaka mini shi ne. . . . ” Wani lokaci yana da muhimmanci ku tattauna littafin nan Reasoning from the Scriptures tare. Don kada ka cika shi da bayanai, ka ba shi shawara a kan sashe ɗaya na gabatarwarsa.

6. Game da hidima, ta yaya ‘ƙarfe yakan wasa ƙarfe’?

6 Ƙarfe Yana Wasa Ƙarfe: Bulus ya ƙarfafa Timotawus, ƙwararren mai wa’azi, ya mai da hankali ga koyarwansa kuma ya yi ci gaba. (1 Tim. 4:13, 15) Wataƙila ka yi shekaru da soma yin wa’azi, kada ka taɓa daina kyautata iyawarka. Ka koya daga wurin masu shela da kake wa’azi tare da su, har da waɗanda ba su ƙware ba sosai a hidima, kuma ka riƙa taimaka wa wasu sosai, musamman sababbi, don su zama ƙwararrun masu shelar bishara.—Mis. 27:17.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba