Bidiyo Mai Suna The Bible—Its Power in Your Life
Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa miliyoyin mutane su canja rayuwarsu zuwa mai kyau. Waɗanne ne wasu cikin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, waɗanda in mun yi amfani da su, za su taimaka mana mu shawo kan matsalolinmu na yau? Babu shakka za ka more samun amsa ga wannan tambayar ta wurin kallon faifan DVD nan, The Bible—Its Power in Your Life [Littafi Mai Tsarki—Ikonsa a Rayuwarka], wanda shi ne sashe na biyu cikin uku da ke cikin bidiyon nan mai suna The Bible—A Book of Fact and Prophecy. Bayan ka kalli wannan bidiyon, za ka iya amsa waɗannan tambayoyi kuwa?
(1) Me ya sa za mu iya ce Littafi Mai Tsarki ya fi sauraran littattafai muhimmanci? (Ibran. 4:12) (2) Idan Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa mutane su kyautata rayuwarsu, me ya sa ’yan Adam suke da matsaloli da yawa? (3) Mene ne ainihin jigon Littafi Mai Tsarki? (4) Waɗanne ayoyin Littafi Mai Tsarki ne aka ambata a bidiyon da zai iya taimaki ma’aurata su (a) kyautata yadda suke tattaunawa da juna (b) kame fushinsu? (5) Ta yaya yadda Kiristoci suke ɗaukan aure zai kyautata rayuwar iyali? (Afis. 5:28, 29) (6) Ta yaya Jehobah ya kafa wa iyaye misali mai kyau? (Mar. 1:9-11) (7) Ta yaya iyaye za su iya sa nazarinsu na iyali ya kasance mai ƙayatarwa? (8) Ban da nazarin Littafi Mai Tsarki, mene ne Kalmar Allah ta ƙarfafa iyaye su yi wa yaransu? (9) Ta yaya shawarar Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaki iyalai su shawo kan matsalolin kuɗi? (10) Waɗanne ƙa’idodin Nassosi game da tsabta, ƙwayoyi da maye da alhini ne idan an yi amfani da su za su taimaka wajen rage rashin lafiya? (11) Waɗanne alkawuran Littafi Mai Tsarki ne za su iya sa mu jimre? (Ayu. 33:25; Zab. 145:16) (12) Ta yaya koyarwa da ke cikin Kalmar Allah ta taimake ka ka kyautata rayuwarka? (13) Ta yaya za ka yi amfani da wannan bidiyon don taimaka wa mutane?