Bidiyo Mai Suna The Bible—Accurate History, Reliable Prophecy
Waɗanne tabbaci ne suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya jitu da tarihi? Waɗanne annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika ne suke tabbatar mana cewa annabce-annabce da aka yi na nan gaba za su samu cikawa? An tattauna waɗannan tambayoyi a bidiyon nan The Bible—Accurate History, Reliable Prophecy [Littafi Mai Tsarki—Tacaccen Tarihi, da Tabbataccen Annabci], wanda shi ne sashe na uku da ke cikin faifan DVD nan mai suna The Bible—A Book of Fact and Prophecy. Bayan kun kalli wannan bidiyon, za ku iya amsa waɗannan tambayoyin kuwa?
(1) Wane ne Tushen tabbataccen Labari da ke cikin Littafi Mai Tsarki? (Dan. 2:28) (2) A wacce hanya mai kyau ce Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙasar Masar na dā, kuma ta yaya annabcin da ke rubuce a Ishaya 19:3, 4 ta samu cikawa? (3) Ta yaya ’yan tarihi ta kimiyyar haƙa ƙasa suka tabbatar da bayanin da Littafi Mai Tsarki ya ba da game da ƙasar Assuriya, sarkinta, da kuma halakar Assuriya? (Nah. 3:1, 7, 13) (4) Waɗanne annabce-annabce game da Babila ne suka samu cikawa? (Irm. 20:4; 50:38; 51:30) (5) Wane annabci ne game da Midiya da Farisa ya kasance da gaske? (Isha. 44:28) (6) Ta yaya Daniyel 7:6 da 8:5, 8 suka samu cikawa a kan ƙasar Hellas? (7) Ta yaya Daniyel 7:7 ya samu cikawa sa’ad da ƙasar Roma ta zama mai mulkin duniya? (8) Waɗanne Kaisar ne aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? (9) Mene ne ya faru da Kiristoci a ƙarƙashin sarautar Nero? (10) Ta yaya annabce-annabce da suke Ru’ya ta Yohanna 13:11 da 17:10 suka samu cikawa? (11) Mene ne bayanuwar sarki na takwas? (12) Waɗanne abubuwa da suke cikin bidiyon ne suka nuna gaskiyar da ke rubuce a cikin Mai-Wa’azi 8:9? (13) Waɗanne annabce-annabce na nan gaba ne kake ɗokin ganin cikawarsu? (14) Ta yaya za ka iya yin amfani da wannan bidiyon don bayyana wa wasu cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne daga wurin Allah?