Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/11 p. 1
  • “Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • “Bari Ku Zama Masu Haske” Don Ku Daukaka Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Haske Daga Allah Na Korar Duhu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • ‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 5/11 p. 1

“Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”

1. Wanne gata ne muke da shi?

1 Kyan haske daga safiya zuwa yamma yana yabon Jehobah Allah. Amma hasken da Yesu ya ce almajiransa su kasance da shi dabam ne, wato, “hasken rai.” (Yoh. 8:12) Samun wannan wayewa ta ruhaniya baiwa ce ta musamman wadda ta kamata mu daraja. Yesu ya ba da umurni: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane,” don mutane su amfana. (Mat. 5:16) Ana bukatar a sa wannan hasken ya haskaka sosai tun da akwai duhu na ruhaniya sosai! Ta yaya za mu iya yin koyi da Kristi, wajen sa haskenmu ya haskaka?

2. Ta yaya Yesu ya nuna muhimmancin sa mutane su samu wayewa ta ruhaniya?

2 Ta Yin Wa’azi: Yesu ya yi amfani da lokacinsa da kuzarinsa da kuma dukiyarsa don ya sa hasken gaskiya ya haskaka ga mutane a gidajensu da wuraren da akwai jama’a sosai da kuma kan dutse, a duk inda akwai mutane. Ya san cewa sa mutane su samu wayewa ta ruhaniya tana da tamani sosai. (Yoh. 12:46) Yesu ya shirya almajiransa su zama “hasken duniya” don mutane da yawa su samu sanin gaskiya. (Mat. 5:14) Sun bar haskensu ya haskaka ta yin nagarta ga maƙwabtansu da kuma gaya musu saƙon gaskiya.

3. Ta yaya za mu iya nuna godiya sosai ga haske na gaskiya?

3 Mutanen Allah suna ɗaukan hakki na yin “tafiya kamar ’ya’yan haske” da muhimmanci, kuma suna wa’azi a duk inda akwai mutane. (Afis. 5:8) Karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu littattafai na Kirista a inda mutane za su iya ganin ka a lokacin shaƙatawa a wajen aiki ko kuma makaranta zai iya sa ka tattauna Nassosi da wani. Wata ’yar’uwa ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ta wannan hanyar kuma ta ba ’yan ajinta sha biyu littattafai!

4. Me ya sa ‘sa haskenmu ya haskaka’ ya haɗa da nuna hali mai kyau?

4 Ta Ayyuka Masu Kyau: Sa haskenmu ya haskaka ya kuma haɗa da halinmu na yau da kullum. (Afis. 5:9) Ana yawan lura da halin Kirista a wurin aiki da makaranta da wurin da akwai mutane da yawa, kuma hakan yana ba da zarafi na tattauna saƙon gaskiya na Littafi Mai Tsarki. (1 Bit. 2:12) Alal misali, hali mai kyau na wani yaro mai shekara biyar ya sa malamarsa ta kira iyayensa. Sai ta ce, “Ban taɓa ganin yaro mai irin wannan ɗabi’a mai kyau ba!” Hakika, hidimarmu da kuma halinmu mai kyau yana jawo mutane zuwa “hasken rai,” kuma hakan yana sa a yabi Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba