‘Ku Zama Masu Taushin Hali’
1. Mene ne mutane suke bukata sosai a yau?
1 ’Yan Adam da yawa a yau suna bukatar a bi da su da taushin hali fiye da dā. Yanayin duniya da ke ci gaba da taɓarɓarewa ya kawo rashin farin ciki da taƙaici da kuma rashin bege a ko’ina. Miliyoyin mutane suna bukatar taimako, kuma mu a matsayin Kiristoci muna da hakkin nuna tabbatacciyar kulawa ga maƙwabtanmu. (Mat. 22:39; Gal. 6:10) Ta yaya za mu iya kula da mutane hakan?
2. A wace hanya mafi kyau ce za mu nuna taushin hali?
2 Aikin da Ake Bukatar Nuna Taushin Hali: Allah ne kaɗai tushen ƙarfafa na gaske da na dindindin. (2 Kor. 1:3, 4) Jehobah ya aririce mu mu yi koyi da shi ta zama ‘masu-taushin hali,’ kuma ya ba mu aikin mu yi wa maƙwabtanmu wa’azin Mulki. (1 Bit. 3:8) Yin iya ƙoƙarinmu a wannan aiki ne hanya mafi kyau na ƙarfafa “masu-karyayyen zuciya,” domin Mulkin Allah ne kaɗai begen da ’yan Adam masu shan wahala suke da shi. (Isha. 61:1) Ba da daɗewa ba, Jehobah mai yin juyayi ga mutanensa, zai aikata don ya kawar da mugunta kuma ya kafa sabuwar duniya ta adalci.—2 Bit. 3:13.
3. Ta yaya za mu yi koyi da yadda Yesu yake ɗaukan mutane?
3 Ka Ɗauki Mutane Yadda Yesu ya Ɗauke Su: Ko sa’ad da Yesu yake yi wa taro mai girma wa’azi, bai ɗauke su a matsayin rukuni kawai ba. Yana ganinsu a matsayin mutane ɗai-ɗai da suke bukatar taimako don su ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Suna kama da tumaki da ba su da makiyayi da zai yi musu ja-gora. Abin da Yesu ya gani ya taɓa zuciyarsa, kuma hakan ya motsa shi ya koyar da su cikin haƙuri. (Mar. 6:34) Ɗaukan mutane yadda Yesu ya ɗauke su zai ƙarfafa mu mu nuna musu juyayi na gaske a matsayin mutane ɗai-ɗai. Za a ga hakan a yadda muke magana da kuma yanayin fuskarmu. Yin wa’azi zai zama abin da ya fi muhimmanci a gare mu, kuma za mu yi magana yadda zai dace da bukatun kowannensu.—1 Kor. 9:19-23.
4. Me ya sa za mu nuna taushin hali?
4 Taron mutane mai girma daga dukan al’ummai suna saurarar saƙon Mulki da kuma kulawa da ake nuna musu. Yayin da muka ci gaba da nuna taushin hali, za mu ɗaukaka da kuma faranta ran Allahnmu Jehobah mai taushin hali.—Kol. 3:12.