Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 9/11 p. 3
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Za Mu Yi Addu’a Ba Fasawa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 9/11 p. 3

Akwatin Tambaya

◼ Shin ya kamata a yi addu’a sa’ad da ake nazarin Littafi Mai Tsarki a bakin kofa?

Soma da kuma rufe nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a yana da amfani sosai. Ta wurin yin addu’a, muna roƙon Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki don tattaunawarmu. (Luk 11:13) Addu’a tana kuma nanata wa ɗalibinmu cewa nazarin Littafi Mai Tsarki yana da muhimmancin kuma hakan yana koya masa yadda ake yin addu’a. (Luk 6:40) Saboda haka, yana da kyau mu soma yin addu’a da mutumin nan da nan bayan mun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Amma dai, tun da yake yanayi ya bambanta, mai gudanar da nazarin yana bukatar nuna sanin ya kamata wajen shawarta ko zai yi addu’a a bakin kofa kafin su yi nazarin Littafi Mai Tsarki ko babu.

Wani abu mai muhimmanci da za mu yi la’akari da shi shi ne wurin da ake nazarin. Da hikima za a iya soma da kuma rufe nazarin da ake yi da addu’a idan wurin da ake gudanar da nazarin babu surutu da yawa. Amma, idan yin hakan zai jawo hankalin mutane ko kuma zai sa daliɓin rashin sakewa, zai dace a jira sai lokacin da za a yi nazarin a wurin da babu surutu kafin a soma da kuma rufe da addu’a. Ko a ina ne ake yin nazarin, ya kamata mu nuna sanin ya kamata don sanin lokacin da za a soma yin addu’a sa’ad da ake nazarin Littafi Mai Tsarki da wani.—Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Maris 2005, shafi na 4 na Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba