Za Ku Iya Yin Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci?
1. Me ya sa zai dace mu ƙara ƙoƙari a wa’azi a lokacin Tuna da mutuwar Yesu?
1 Lokacin tunawa da mutuwar Yesu yana ba mu zarafin ƙara ƙoƙari a wa’azi. Lokaci ne da ya kamata mu tuna da yadda Jehobah ya nuna mana ƙauna ta wajen ba da Ɗansa ya fanshe mu daga zunubi. (Yoh. 3:16) Hakan yana sa mu nuna godiya ga Jehobah kuma mu ƙara kasancewa da ƙwazo wajen gaya wa mutane abubuwan da Jehobah yake yi wa ’yan Adam. (Isha. 12:4, 5; Luk 6:45) Lokaci ne kuma da muke jin daɗin yin kamfen don mu gayyaci abokanmu da kuma mutane da ke yankinmu su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu tare da mu. Bayan haka, sai mu yi ƙoƙari mu ziyarci waɗanda suka halarci taron Tuna mutuwar Yesu don mu ci gaba da tattaunawa da su. Za ku iya ƙara ƙoƙari a wa’azi ta wajen yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watannin Maris da Afrilu da kuma Mayu?
2. Me ya sa watan Maris ya zama wata mai kyau na yin hidimar majagaba na ɗan lokaci?
2 Ku Keɓe Watan Maris don Yin Hidima ta Musamman: Maris wata ne da zai ba mu zarafin yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Waɗanda suke son su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci za su iya ba da awa 30 ko 50. Idan mai kula da da’ira zai ziyarci ikilisiyarku a watan Maris, waɗanda suke hidimar majagaba na ɗan lokaci za su iya halartar taron da zai yi da majagaba na kullum. An ƙara tsawon lokacin rarraba takardun gayyata don Tuna da mutuwar Yesu da za a yi a ranar Talata, wato, 26 ga Maris, 2013. Saboda haka, a wannan shekarar za a soma rarraba takardun a ranar 1 ga Maris. Ƙari ga haka, watan Maris yana da Lahadi guda biyar da Asabar guda biyar. Zai dace ku duba yanayinku ku ga ko zai yiwu ku haɗa kai da sauran ’yan’uwa don ku sa wannan watan ya zama wata na musamman a wannan shekara.
3. Wane tsari ne za mu iya bi don mu sami zarafin yin wa’azi sosai?
3 Ku Fara Shiri Tun Yanzu: Yanzu ne ya dace ku bincika yanayinku ko zai yiwu ku yi gyara don ku sami zarafin yin hidimar majagaba. Zai dace kowa a cikin iyalinku ya ba da haɗin kai. Saboda haka, za ku iya tattauna maƙasudanku a matsayin iyali a lokacin da kuke Bauta ta Iyali da yamma sa’an nan ku tsara ayyukanku. (Mis. 15:22) Idan ba za ku iya yin majagaba na ɗan lokaci ba, kada ku yi sanyin gwiwa. Za ku iya daidaita ayyukanku don ku yi wa’azi fiye da yadda kuka saba yi a duk ranar da kuka fita wa’azi. Ko kuma za ku iya keɓe ƙarin kwana ɗaya don fita wa’azi a mako.
4. Wane amfani ne za mu mora idan muka ƙara ƙwazo a yin wa’azi a watannin Maris da Afrilu da kuma Mayu?
4 Yayin da muka ƙara ƙwazo a yin wa’azi a watannin Maris da Afrilu da Mayu, za mu sami damar yi wa Jehobah da kuma mutane hidima kuma hakan zai sa mu kasance da farin ciki da gamsuwa sosai. (Yoh. 4:34; A. M. 20:35) Amma, abin da ya fi muhimmanci shi ne, sadaukar da kai da muke yi yana faranta wa Jehobah rai.—Mis. 27:11.