Ku Marabce Su!
1. A wane lokaci ne za mu iya ba da shaida sosai, kuma don me?
1 A lokacin tunawa da mutuwar Yesu da ake yi kowace shekara ne muke samun dama mai kyau na ba da shaida. Muna sa rai cewa mutane fiye da miliyan 10 za su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu a wannan shekarar, kuma za su koyi hanyoyi guda biyu masu muhimmanci da aka nuna wa ’yan Adam ƙauna ta wajen fansar Yesu. (Yoh. 3:16; 15:13) Za su koya game da albarka da za su iya mora saboda wannan kyauta daga Jehobah. (Isha. 65:21-23) Amma ba mai ba da jawabi ne kaɗai zai ba da shaida a wannan ranar ba. Dukan ’yan’uwa da suka halarci taron za su iya ba da shaida sosai ta wajen marabtar baƙi da kyau.—Rom. 15:7.
2. Ta yaya za mu marabci baƙinmu da fara’a?
2 A maimakon ku je ku zauna kawai kuna jiran a soma taron, zai dace ku yi ƙoƙari ku gai da mutane da suke wurin kuma ku gaya musu sunanku. Waɗanda muka gayyata za su iya jin tsoro domin ba su san abin da zai faru a taron ba. Yadda muka marabce su da fara’a zai sa hankalinsu ya kwanta kuma su ji daɗin taron. Idan kuna son ku sani ko waɗanda suka zo sun sami gayyata ne daga wurin wani, za ku iya tambayarsu ko wannan ne farkon zuwansu a taronmu ko kuma sun waye wani a cikin ikilisiyar. Idan zai yiwu, za ku iya gaya musu su zauna tare da ku don su yi amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma littafin waƙarku. Idan kuna amfani da Majami’ar Mulki ne, za ku iya ɗan zagayawa da su don su ga wurin da kyau. Bayan an gama jawabin, za ku iya gaya musu cewa kuna shirye don ku amsa tambayoyinsu. Amma idan ana bukatar ikilisiyarku ta bar wurin taron nan da nan domin wata ikilisiya ta shiga, za ku iya cewa: “Zan so in ji ra’ayinka, ya ka ga taronmu? Ina kake da zama don in zo mu tattauna?” Sai ku shirya yadda za ku sake haɗuwa don ku ci gaba da tattaunawa da su. Dattawa musamman za su yi ƙoƙari su ƙarfafa ’yan’uwan da suka daina fita wa’azi amma sun halarci taron.
3. Me ya sa yana da kyau mu yi ƙoƙari don mu marabce baƙi da suka zo taron tunawa da mutuwar Yesu?
3 Ga wasu baƙi da yawa, wannan zai zama lokaci na farko da suke shaida farin ciki da salama da kuma haɗin kai da ke tsakaninmu domin muna bauta wa Jehobah. (Zab. 29:11; Isha. 11:6-9; 65:13, 14) Mene ne baƙinmu za su riƙa tunawa bayan sun bar wurin taron? Ra’ayinsu game da mu zai dangana ne bisa yadda muka marabce su.