Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/14 pp. 2-4
  • Ku Tuna da Waɗanda Suke Gidajen Kula da Tsofaffi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Tuna da Waɗanda Suke Gidajen Kula da Tsofaffi
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Suna Ware Amma Ba A Mance Da Su Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yadda Za Ku Amfana Daga Rukuninku na Wa’azi
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Abubuwa Biyar da Za Su Taimaka Mana Mu Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 6/14 pp. 2-4

Ku Tuna da Waɗanda Suke Gidajen Kula da Tsofaffi

1. Me ya sa muke bukata mu kai bishara ga waɗanda suke gidajen kula da tsofaffi?

1 Da kowace wayewar gari, mutane suna tsufa kuma suna fuskantar matsalolin da ke tattare da tsufa. (M. Wa. 12:1-7) Tsofaffi da yawa suna zama a gidajen kula da tsofaffi, shi ya sa ba ma cika samun su sa’ad da muke wa’azi gida-gida. Ko da yake tsofaffi da kuma wasu majiyyata da ke waɗannan gidajen ba su da ƙarfin tafiya sosai ko kuma ba sa tuna abubuwa da kyau, za su iya koyo kuma su zo ga sanin Jehobah har su soma bauta masa. Ta yaya za mu iya yi ma waɗannan mutanen wa’azin “begen nan mai-albarka” ko kuma ban farin ciki?—Tit. 2:13.

2. Mene ne mai kula da hidima zai yi don a ziyarci gidajen kula da tsofaffi?

2 Mataki na Farko: Mai kula da hidima ne zai zaɓi ƙwararrun masu shela don su ziyarci dukan gidajen kula da tsofaffi. Idan aka shirya da kyau kuma aka dogara ga Jehobah, za a iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki na rukuni a wurin.—Mis. 21:5; 1 Yoh. 5:14, 15.

3, 4. (a) Wane ne ya kamata mu samu idan muna so mu soma nazari na rukuni? (b) Ta yaya za mu iya bayyana abubuwan da gudanar da nazarin ta ƙunsa?

3 Matakan da za a ɗauka don a soma nazarin Littafi Mai Tsarki sun dangana ga girman gidan da ake kula da tsofaffin. Idan gidan yana da girma kuma akwai mazauna da kuma ma’aikata da yawa, zai fi dacewa ku sami mai karɓan baƙi don ku nemi izinin yin magana da manajan. A ƙananan gidaje don kula da waɗanda suka tsufa sosai, inda ake da mazauna kaɗan da kuma masu kula biyu ko uku, zai fi a tattauna da maigidan kai tsaye.

4 A kowane yanayin, ku bayyana cewa kuna sadaukar da lokacinku ne don ku ƙarfafa waɗanda suke son karatu da kuma tattauna labarai daga Littafi Mai Tsarki. Ku bincika don ku san ko akwai waɗanda za su so a riƙa tattauna Littafi Mai Tsarki da su a matsayin rukuni cikin minti 30 a kowane mako. Akwai littattafai dabam-dabam da za ku iya amfani da su, amma wasu sun ji daɗin yin amfani da Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki da kuma The Greatest Man Who Ever Lived. Za ku iya nuna wa manajan littattafan idan kuna so. Ku tattauna da manajan a kan rana da wuri da kuma lokacin da za ku riƙa yin nazarin, sa’an nan ma’aikatan za su iya rubuta hakan a kalandar da ke ɗauke da tsarin ayyukan ma’aikatar. Kada ku ji tsoron bayyana cewa ku Shaidun Jehobah ne. Ƙari ga haka, ku fahimtar da manajan cewa manufar zuwanku ita ce ku koyar da Littafi Mai Tsarki, ba ku yi taron coci ba.

5. Waɗanne abubuwa ne za su sa nazarin ya yi daɗi kuma ya kasance da amfani?

5 Yadda Za A Yi Nazarin: Yadda za ku gudanar da nazarin zai dangana ga yanayi da kuma mahallin wurin. Saboda haka, ku yi amfani da basira kuma ku tsara nazarin bisa ga yanayin. Ya kamata mai gudanar da nazarin ya kawo littafin da suke amfani da shi da yawa kuma ya karɓi littattafan bayan sun gama nazarin. Zai dace a riƙa zuwa da littattafan da aka wallafa da manyan rubutu. Ana iya gudanar da nazarin kamar yadda muka saba, wato a karanta sakin layi, a yi tambaya sa’an nan a bari a ba da amsa. Za a iya ba waɗanda suka iya karatu dama su karanta sakin layi ko kuma nassosi idan suna so. Ku gudanar da nazarin da fara’a da ban ƙarfafa kuma ku riƙa ba su dama su yi kalami. Ku nemi izinin manajan a duk lokacin da kuke so ku nuna musu bidiyon ƙungiyar Jehobah da zai taimaka musu su yi imani da koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma su koyi darussa daga wani labari da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki. Kuna iya soma da kuma kammala nazarin da addu’a. Wasu masu shela ma sukan raira waƙoƙinmu.

6. Mene ne ya kamata ku yi idan wani bai amince da wani bayani ba?

6 Mene ne ya kamata ku yi idan wani bai amince da wani bayani ba? Ku mai da martani cikin basira. (Kol. 4:6) Mai yiwuwa za ku iya karanta wani nassi da zai warware batun. Idan yin hakan ba zai taimaka ba, ku tabbatar masa cewa za ku tattauna batun da shi bayan nazarin.

7. Mene za ku iya yi idan wani ya yi tambaya ko kuma ya nuna cewa yana so ya ƙara koyo?

7 A wani lokaci, wani a cikin waɗanda kuke nazari da su yana iya yin tambaya ko kuma ya gaya muku cewa yana so ya daɗa koyo. Ga abin da wata ’yar’uwa takan faɗa: “Na ji daɗin tambayarka. Amma da yake tambayar ba ta shafi sauran mutanen ba, zan so in tattauna da kai kaɗai bayan nazarin.” A yawancin lokatai, yana yiwuwa a shirya da wanda yake so a yi nazari da shi a wuri da kuma lokacin da zai fi so.

8. Yaya ya kamata a ba da rahoton nazarin da aka yi da rukuni da kuma wanda aka yi da mutum ɗaya?

8 Zai fi dacewa masu shela da suka soma gudanar da nazarin su ci gaba da yin haka. Masu shela da suka gudanar da nazarin tare za su iya ba da rahoton awoyin da suka yi amfani da su. Da zarar nazarin ya tabbata, mai shelar da ya ja-goranci nazarin zai rubuta cewa ya koma ziyara sau ɗaya a duk lokacin da ya yi nazari da rukunin, sa’an nan a ƙarshen wata, ya rubuta cewa ya gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki sau ɗaya. Idan kuka yi nazari da wani da ke gidan, amma yana iya koya da kuma fahimtar abu da kyau, za ku rubuta rahoton yadda muka saba yi.

9, 10. Waɗanne halaye ne waɗanda suke gudanar da irin wannan nazarin za su nuna? Ka bayyana.

9 Kada Ku Daina Nazarin: Zai dace a kafa rana da kuma lokacin yin nazarin. Mazauna da kuma ma’aikatan za su so a riƙa yin nazarin a kai a kai kuma a kan lokaci. (Mat. 5:37) Saboda haka, kuna bukata ku zama masu cika alkawari kuma ku kasance da himma da kuma tsari. Rahoto ya nuna cewa ya fi dacewa ƙwararrun masu shela guda biyu su riƙa zuwa gudanar da nazarin tare. (M. Wa. 4:9, 10) Amma a manyan gidajen kula da tsofaffi, za a bukaci masu shela fiye da biyu.

10 Yana da muhimmanci mu kasance da fara’a kuma mu nuna cewa mun damu da mutane. (Filib. 2:4) A ziyararku ta farko, ku yi ƙoƙari ku gabatar da kanku ga kowanne cikin mahalartan. Ku rubuta sunayensu kuma ku haddace su kafin ziyararku ta gaba. Amma, wasu tsofaffi ba sa so a kira su da sunansu na fari, musamman ma mutumin da ba su saba da shi ba. Idan kuna da haƙuri da kuma juyayi, za su ga cewa kuna ƙaunar su kuma za su saki jiki.

11. Ta yaya ’yan’uwan da ke gudanar da nazarin za su girmama ma’aikatan da kuma dangin mazaunan?

11 Yana da muhimmanci mu girmama ma’aikatan da kuma dangin mazaunan kuma mu yi musu kirki. Da zarar kun tsara yadda za ku riƙa gudanar da nazarin, zai dace ku nemi izinin manajan a duk lokacin da kuke so ku canja tsarin. Ɗan’uwan da ke gudanar da nazarin zai iya neman shawarar manajan a kan yadda za su iya kyautata nazarin. Idan wani danginsu ya kawo ziyara sa’ad da kuke yin nazari, zai yi kyau ku sadu don ku gabatar da kanku kuma ku bayyana masa manufar nazarin. Ku tabbatar musu cewa kun damu da danginsu kuma ku gayyace su su yi nazarin tare da ku.

12, 13. Ka ba da labarin da ya nuna amfanin yin wa’azi a gidajen kula da tsofaffi.

12 Sakamako: Masu kula masu ziyara da kuma wasu ikilisiyoyi sun ba da rahoto mai kyau a kan irin wannan salon yin wa’azin. A wani gidan kula da tsofaffi, mazauna wajen 20 sun halarci tattaunawa ta farko. Hakan ya sa aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da guda shida daga cikinsu, amma ba a matsayin rukuni ba. A sakamako, wata a cikinsu ta yi baftisma. Wani nazarin da aka gudanar a wani gida dabam ya sa wata ’yar shekara 85 ta soma halartan taron ikilisiya kuma ta ce tana so a yi mata baftisma. Sa’ad da ake so a rage yawan ayyukan da ake yi a wani gidan kula da tsofaffi, sai aka dakatar da nazarin da Shaidun Jehobah suke gudanarwa, amma mazaunan suka kai kuka gaban manajan. Daga baya, aka soma gudanar da nazarin, amma a wannan lokacin, mutane 25 zuwa 30 ne suke halarta.

13 Mazauna a gidajen kula da tsofaffi da kuma wasu suna ganin irin ƙaunar da muke nuna ma waɗanda ke wurin. Alal misali, ba abin mamaki ba ne a ga wasu ma’aikata sun halarci taron kuma su yi kalami ko kuma karatu sa’ad da ake nazarin. Ƙoƙarin da muke yi wajen nuna cewa mun damu da waɗanda suke gidajen kula da tsofaffi yana ba da shaida mai kyau ga mutanen yankin. (1 Bit. 2:12) Bayan da aka gaya ma wani manaja manufar nazarin, sai ya ce: “Me ya sa ba ku soma wannan tuntuni ba? To yaushe za ku soma?” Wata manajar kuma ta rubuta cewa: “Zan shawarci kowane gidan kula da tsofaffi a yankin nan ya yarda a kafa musu wannan nazari na rukuni. Shaidun Jehobah suna yin hakan kyauta kuma sashe ne na hidimar da suke yi a yankin.” Wani gidan kula da tsofaffi a jihar Hawaii ya ba Shaidu Jehobah lambar yabo da ta nuna cewa suna da amfani sosai ga mazaunan gidan.

14. Me ya sa muke so mu taimaka ma waɗanda suke gidajen kula da tsofaffi?

14 Jehobah yana gayyatar tsofaffi su yabe shi. (Zab. 148:12, 13) Kuma hakan ya haɗa da tsofaffin da ke gidajen da ake kula da su. Shin akwai gidajen kula da tsofaffi a yankinku da kuke ganin mazauna gidan za su amfana daga bishara? Da taimakon dattawan ikilisiyarmu da kuma manajojin gidan kula da tsofaffi, za mu iya yin wa’azi ga mazaunan gidan. A duk lokacin da muka tuna da tsofaffi, za mu nuna cewa muna yin koyi da Jehobah.—Zab. 71:9, 18.

Yadda Ake Tattaunawa a Gidajen Kula da Tsofaffi

  • Ku sami mai karɓan baƙi da kuma manajan a duk lokacin da kuka je gudanar da nazari.

  • Ku je da kofi da yawa na littattafan da kuke tattaunawa da rukunin. Ku saka littattafan a cikin jaka mai kyau, kuma ku karɓi littattafan a ƙarshen nazarin.

  • Ku saki jiki kuma ku kasance da fara’a. Ku riƙa amfani da sunayen mazaunan.

  • Ku riƙa karanta da kuma tattauna sakin layi ɗaya bayan ɗaya.

  • Ku riƙa yin gajerun tambayoyi kuma ku yaba musu sa’ad da suka yi kalami.

  • Maimakon ku amsa tambaya a kan wata koyarwar da za ta iya jawo gardama, ku shirya da wanda ya yi tambayar don ku tattauna da shi a wani lokaci dabam.

  • Ku amsa tambayoyin ma’aikata da kuma na dangin mazaunan kai tsaye.

  • Idan tsofaffin ko danginsu ko kuma ma’aikata suka ba ku damar yin nazari da su, kada ku bar damar ta wuce.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba