Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/14 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da Ita a Kowane Lokaci
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Yi Amfani da Sabuwar Warƙar da Aka Wallafa don Dandalinmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Gabatarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 7/14 p. 4

Gabatarwa

A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?

Bayan gaisuwa, ka miƙa wa maigidan warƙar don ya ga jigon kuma ka ce: “Muna wani kamfen ne a faɗin duniya don rarraba wannan warƙar da ke ɗauke da wani saƙo mai muhimmanci. Zan so wannan ta zama naka.”

Idan kana so ka bar warƙar a gidan da babu kowa, kada ka ajiye ta a inda mutane za su iya gani kuma kada ka naɗe ta in ba dai yin hakan ya zama dole ba.

Idan maigidan ya so saƙon ko kuma ya so ku tattauna, za ka iya neman ra’ayinsa a kan tambayoyin da ke gaban warƙar. Ka buɗe warƙar kuma ka karanta masa inda aka yi ƙaulin Zabura 119:144, 160. Ka bayyana masa cewa warƙar tana ɗauke da adireshin wani dandali da zai taimaka masa ya sami amsoshi a Littafi Mai Tsarki. Za ka iya kunna masa bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? don ya ga misali. Kafin ka tafi, ka nuna masa tambayoyi uku da ke bayan warƙar kuma ka tambaye shi wadda ta fi damunsa. Ka gaya masa cewa za ka so ka dawo don ka nuna masa yadda zai iya samun amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga wannan tambayar a jw.org. Idan ka koma, ku tattauna amsar daga dandalinmu a sashen KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI.

Idan kuma kuna rarraba takardar gayyata zuwa taron yanki a wannan lokacin, ka miƙa wa maigidan takardar gayyatar tare da warƙar kuma ka ce, “Mun haɗa maka da takardar gayyata zuwa wani babban taro da za a yi kyauta.”

Hasumiyar Tsaro Yuli–Agusta

A ƙarshen mako, za ku iya ba da Hasumiyar Tsaro idan hakan zai dace. Za ku iya cewa: “Za mu kuma so mu ba ka mujallunmu na kwanan nan. Wannan Hasumiyar Tsaro ta amsa tambayar nan, Akwai Wanda Zai Iya Sanin Gobe?”

Awake! Agusta

A ƙarshen mako, ga abin da za ku iya faɗa don ku ba da mujallar Awake! idan hakan zai dace: “Za mu kuma so mu ba ka mujallunmu na kwanan nan. Wannan mujallar Awake! ta ba da amsar tambayar nan, Ta yaya mutane za su iya sulhuntawa da juna?”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba