Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Nuna Yadda Ake Nazari da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Mai yiwuwa mutane da yawa ba za su fahimce mu ba idan muka ce musu za mu so mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Suna iya ɗauka cewa sai sun shiga wani aji don nazari ko kuma su soma nazari ta hanyar wasiƙa. Saboda haka, maimakon mu gaya musu kawai cewa za mu so mu yi nazari da su, zai dace mu nuna musu yadda ake yin nazari da mutane. A cikin ’yan mintoci, za mu iya nuna wa mutane cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki abu ne mai sauƙi kuma zai wayar da kansu sosai.
Ku Bi Shawarar Nan Wannan Watan:
Ku roƙi Jehobah ya taimaka muku ku soma nazari da wani.—Filib. 2:13.
Ku yi ƙoƙari ku nuna ma aƙalla mutum ɗaya yadda ake nazari da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? sa’ad da kuke wa’azi.