Ku Yi Amfani da Ikon Kalmar Allah a Wa’azi
Idan wani ya yarda mu yi masa wa’azi, zai dace mu yi amfani da wannan damar don mu karanta masa Kalmar Allah kai tsaye. An nanata hakan a taro na musamman na shekarar da ta wuce. A taron, mai kula da da’ira ya ba da jawabi mai jigo “Ku Yi Amfani da Ikon Kalmar Allah a Wa’azi.” Shin ka tuna da muhimman darussa da aka bayyana?
Me ya sa maganar Jehobah ta fi namu iko sosai?—2 Tim. 3:16, 17.
Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake ratsa zukatan mutane, ya daidaita ra’ayinsu da halayensu da kuma ɗabi’unsu?—Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2012, shafi na 27, sakin layi na 7.
Sa’ad da muke karanta ma wani wata aya a hidima, ta yaya za mu jawo hankalinsa ga Kalmar Allah a hanyar da za ta sa mutumin ya ɗauki kalmomin da muhimmanci sosai?—Ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 148, sakin layi na 3-4 da kuma Hidimarmu ta Mulki ta Maris 2013, shafi na 6, sakin layi na 8.
Me ya sa yake da muhimmanci mu tattauna kuma mu bayyana nassosin da muka karanta wa mutane, kuma ta yaya za mu iya yin hakan?—A. M. 17:2, 3; ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 154, sakin layi na 4 zuwa shafi na 156, sakin layi na 5.