RAYUWAR KIRISTA
Rayuwa Mafi Inganci
Akwai hanyoyi da dama a ƙungiyar Jehobah da matasa za su iya faɗaɗa hidimarsu. Ka kalli bidiyon nan Rayuwa Mafi Inganci don ka ga yadda Cameron ta yi amfani da ƙuruciyarta a hanyar da ta dace. Sai ka yi ƙoƙarin amsa tambayoyin da ke ƙasa. (Ka shiga jw.org/ha ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA.)
Mene ne Cameron ta fi ɗauka wa da muhimmanci a rayuwarta?
Yaushe ta tsai da shawarar faɗaɗa hidimarta kuma ta yaya ta yi hakan?
Yaya ta yi shiri don ta yi hidima a inda ake da bukatar masu shela a wata ƙasa?
Waɗanne ƙalubale ne Cameron ta fuskanta yayin da take hidima a wata ƙasa?
Me ya sa zai kasance da albarka mu yi hidima a wani wuri da ba mu taɓa hidima ba?
Ta yaya Allah ya albarkaci Cameron?
Me ya sa hidimar Jehobah ce kaɗai take sa mutum ya yi rayuwa mafi inganci?
Waɗanne maƙasudai ne matasa za su iya kafawa a ƙungiyar Jehobah?