DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 60-68
Ku Yabi Jehobah Mai Jin Addu’a
Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka cika alkawuranka
61:1, 8
Idan muna ambata alkawuranmu a addu’a, hakan zai sa mu yi ƙoƙari mu cika su
Wa’adin da muka yi na bauta wa Allah shi ne alkawarin da ya fi muhimmanci
Hannatu
Ka nuna ka dogara ga Jehobah ta wurin gaya masa damuwarka
62:8
Addu’a mai kyau ita ce wadda za ka gaya wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka
Idan muka gaya wa Jehobah abin da muke bukata, za mu gane idan ya amsa mana
Yesu
Jehobah yana jin addu’ar dukan waɗanda suke masa biyayya
65:1, 2
Jehobah yana jin addu’o’in “dukan masu rai” da suke so su san shi kuma su bauta masa
Za mu iya yin addu’a ga Jehobah a kowane lokaci
Karniliyus
Abubuwan da nake so in gaya wa Jehobah a addu’a.