DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 63-66
Sababbin Sammai da Sabuwar Duniya Za Su Sa Mu Murna Sosai
Jehobah yana da tabbaci sosai cewa zai cika alkawarin da ya yi na sabonta sammai da duniya a Ishaya sura 65, shi ya sa ya furta shi kamar ya riga ya cika.
Jehobah yana halittar sababbin sammai da sabuwar duniya, inda ba za a ƙara tunawa da al’amura na dā ba
65:17
Mene ne sababbin sammai?
Sabuwar gwamnati ce da za ta cire mugunta a duniya
An kafa ta a shekara ta 1914 sa’ad da Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah
Mece ce sabuwar duniya?
Mutane ne daga ƙabilai da harsuna da kuma ƙasashe dabam-dabam da suke goyon bayan Mulkin Allah
A wace hanya ce ba za a ƙara tuna da al’amura na dā ba?
Abubuwan da ke sa mu baƙin ciki ba za su riƙa faruwa ba
Mutane masu adalci za su riƙa jin daɗin rayuwa kowace rana