RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance da Halaye Masu Kyau—Bangaskiya
ME YA SA TAKE DA MUHIMMANCI:
Wajibi ne mu kasance da bangaskiya idan muna so mu faranta wa Allah rai.—Ibr 11:6
Idan muka gaskata da alkawuran Allah, za mu jimre jarrabawa.—1Bi 1:6, 7
Za mu iya yin zunubi idan ba mu da bangaskiya.—Ibr 3:12, 13
YADDA ZA KA KASANCE DA HALIN:
Ka roƙi Allah ya sa ka kasance da bangaskiya sosai.—Lu 11:9, 13; Ga 5:22
Ka karanta Kalmar Allah kuma ka yi bimbini a kai.—Ro 10:17; 1Ti 4:15
Ka riƙa tarayya da mutane masu bangaskiya sosai.—Ro 1:11, 12
Ta yaya zan ƙarfafa bangaskiyata da ta iyalina?
KU KALLI BIDIYON NAN KU KOYI HALAYEN DA ZA SU ƘARFAFA AMINCINKU—BANGASKIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Me ake nufin da “bangaskiya marar riya,” wato ta ƙwarai? (1Ti 1:5)
Idan muna son bangaskiyarmu ta yi ƙarfi, mene ne ya kamata mu guje wa?
Me ya sa muke bukatar bangaskiya a lokacin ƙunci mai girma? (Ibr 10:39)