DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZEKIYEL 42-45
An Maido da Bauta ta Gaskiya!
Wahayin da aka saukar wa Ezekiyel game da haikali ya tabbatar wa Isra’ilawan da suke zaman bauta cewa za a maido da bauta ta gaskiya. Ƙari ga haka, ya tuna musu da ƙa’idodin Jehobah na bauta ta gaskiya.
Firistoci za su koya wa mutanen ƙa’idodin Jehobah
44:23
Ka ba da misalin yadda bawan nan mai aminci ya taimaka mana mu bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki. (kr 110-117)
Mutanen za su bi ja-gorancin waɗanda Jehobah ya naɗa
45:16
A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna goyon bayan dattawan ikilisiyarmu?