DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | NAHUM 1–HABAKKUK 3
Ka Yi Tsaro da Ƙwazo a Ibadarka
Hab 1:5, 6
Mutane suna ganin kamar ba zai taɓa yiwu Babiloniyawa su halaka Urushalima ba. A lokacin, Yahudawa sun ƙulla dangantaka da ƙasar Masar. Kuma mutanen Masar sun fi mutanen Babila ƙarfi. Ban da haka ma, Yahudawa suna ganin cewa Jehobah ba zai taɓa bari a halaka Urushalima da kuma haikalin ba. Duk da haka, wannan annabcin zai faru kuma Habakkuk yana bukatar ya yi tsaro kuma ya yi ƙwazo a hidimarsa.
Mene ne ya tabbatar mini da cewa duniyar nan ta kusan zuwa ƙarshe?
Ta yaya zan ci gaba da yin tsaro da kuma ƙwazo a hidimata?